'Kansar maƙoshi ta raba ni da muryata da aurena'

- Marubuci, Komla Adom
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, BBC News, Accra
- Lokacin karatu: Minti 4
Ba a rasa duk wani mai dauke da sankara da labari mai sosa rai cike da dimbin tausayi, jajircewa da fatan makoma mai kyau.
Yayin da miliyoyin mutane ke fama da wannan cuta, kowanne labari na tattare da sosa rai kuma idan ka saurara sai ka ji wani abu na daban.
A wannan shekarar taken ranar yaƙi da cutar shi ne, hadin-kai ta fuskar labarai masu ƙayatarwa.
Taken na magana ne ko ankararwa kan labarai da ba a fadi kan yanayi na azabtarwa da masu dauke da cutar ko wadanda suka rayu bayan fama cutar suka fuskanta, galibi labarai ne da ba a fadinsu.
Daya daga cikin irin wadannan labarai shi ne na Mary Amankwah Fordwor, wata babbar jami'ar jinya a asibitin St. Anthony Catholic da ke Ghana da aka gano tana dauke da sankara a makoshinta a shekarar 2021.
"Na wayi gari da kumburi a makoshina ta wajen wuya wanda ya ƙi warkewa," a cewar matar mai yara biyu a hirarta da BBC. Likitoci daga baya suka fahimci wannan kumburi da nake shawa maguguna kansa ce.
An yi mata tiyata sau 14, wasu kamar ba za ta rayu ba a karshe dai, an cire mata abin da ke taimakawa magana. Yanzu da na'ura take iya magana kuma ba ta iya cin abinci kamar a baya.
An gano tana dauke da wannan cuta ne ana gab da kara mata mukami a inda take aiki. Cutar ta katse mata rayuwa, ba wai fannin aiki kadai ba har da rayuwarta, ta hanyoyi daban-daban, ciki har da rasa aurenta na tsawon shekara 12.
A kowacce shekara, mutane kusan miliyan 1.1 ke fama da kansa a Afirka, inda mutane dubu dari bakwai ke rasa rayukansu, a cewar Hukumar Lafiya Duniya, WHO. Alkaluman na da yawa - inda a duniya mutum miliyan 10 ke mutuwa duk shekara - yayin da duniya ke fama da yaƙi da cutar, wanda har yanzu ke daure kai a duniya.

Asalin hoton, Mary Amankwah Fordwor
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"A lokacin da ake mun gashi da magunguna, ina ganin mutane na mutuwa, sai na kirkiri dandali a manhajar WhatsApp wanda ya kunshi mutane 12, inda nake amfani da rayuwata da yadda nake tafiyar da lamura wajen karfafa musu cewa akwai rayuwa a gaba bayan kansan makoshi, kamar yada ta shaidawa BBC.
Mary ta rinka jan hankali sosai musamman a shafin Tiktok da Instagram da Youtube.
Idan ta ziyarci makarantu, coci-coci da kungiyoyi, tana magana kan aminta da yada rayuwa ta zo mata.
"Ban san me ake nufi da son-kai ba. Ban san me ake nufi da yarda da kai ba, sai da na gamu da wannan cuta ta kansar makoshi', a cewarta.
Likitoci sun gagara gano me ya haddasa wa Mary Kansa. Sai dai a cewar Hukumar Lafiya Duniya, WHO, kashi 90 cikin 100 na mutane, jikinsu na yaki da cututtuka da ke juyewa su koma kansa, irin wadannan cututuka ko kwayoyin cututuka na iya zama kansa ta makoshi ko baki ko kansar mafitsara da gaban mata ko wajen bahaya.
A 2019, Irin wadannan kwayoyin cututuka sun haifar da cututtukan kansa dubu 620 a mata, maza kuma dubu 70 a fadin duniya.
Sashin da ke sa ido kan cuttukan kansa a WHO a 2022 a Ghana ya gano kansa ko sankarar makoshi shi ne na 17 cikin ire-iren kansa har 32 da ake fama da shi, inda ake samun mutane 227 a kowacce shekara da karin kashi biyar a kowacce shekara. A Afirka, mutane 10,665 sun kamu da sabbin na'ikan kansa a 2022.
"Mutane na watsi da alamomi ko yanayin da idan an gano da wuri, ya iya taimakawa wajen takaita yaduwarta a jiki, a cewar Dakta Ama Boatemaa Prah, kwararriya a fannin kansa da ke asibitin koyarwa na Korlebu da ke Ghana
Alamonin farko sun hada da kumburi ko murya ta sauya. Sannan akwai wahala wajen numfashi da murar da ba a warkewa.
"Muna ganin manya masu shekaru da ke fama da kansar makoshi amma a yanzu abin ya koma kan matasa 'yan kasa da shekara 40, a cewar Dakta Prah.
Yayinda Mary tayi sa a wajen samun kulawa da rayuwa, likitoci sun ce yayi wuri a iya tantace ko yanke ta rabu da kansa baki daya.
"Kansa makoshi ba wai ta tafi mun da murya ta ba ce kawai; ta kuma rabani da aure na na shekaru 12," a cewarta.
Ta kasance daya daga cikin matan da mazajensu ke rabuwa da su a lokaci tsananin fama da cutar kansa, kamar yadda bincike da jami'ar Michigan ke nunawa a 2014. Kashi 31 cikin 100 na ma'aurata na rabuwa saboda dalilai na cutar, musamman maza da ba sa jure jinyar matansu.
Wani bincike daga cibiyar bincike ta kansa, Fred Hutchinson a 2009, ta ce alkaluman matan da ake saki saboda kansa ya karu na kashi 20.8 cikin 100, yayinda na maza baya zarta kashi 2.9 cikin 100.
Kwarraru a fannin lafiya a Ghana sun ce wannan yanayi na karuwa duk da dai su basu da alkaluma a hukumance.
Mary ta bai wa kanta kwarin-gwiwar da kuma nuna rashi nadama mutuwar aurenta. Ta ce rayuwarta tafi komai muhimmanci, sanna ko ba komai tana tare da iyayenta da yaranta biyu - masu shekara 11 da 8 - da suke tare da ita, duk da cewa ba wai sun fahimci abin da take ciki bane
"Mama na fadamana cewa tana da Kansa kuma muna zuwa dubata lokacin da aka yi mata aiki, Ina ta tsoron kada ta mutu. Amma yanzu tana tare da mu, muna cikin farin-ciki, a cewar Emmanuella, mai shekara takwas.
Dr Prah ta bayyana yanayi Mary da labari mai janhankali da karfafa gwiwa. "Ta kasance mai jajircewa, kuma kullum cikin farin ciki. Muna son masu irin wannan cuta su koye abubuwa na kwarin-gwiwa da jajircewa daga gareta a yaki da wannan cuta ta kansa." a cewar likitar.
Taken bikin na bana - hadin-kai da labarai masu karfafawa - wani tsari ne da zaa shafe shekaru uku ana dabbakawa domin karfafawa da jan hankali cewa cuta ba mutuwa ba ce.











