Rawar da Barca ta taka wajen lashe kofi uku a kakar 2024/25

Asalin hoton, Getty Images
An kammala kakar 2024/25, wadda abin alfahari ce ga Barcelona, sakamakon lashe La Liga da Coapa del Rey da Spanish Super Cup da ta yi.
Ƙungiyar ta yi namijin ƙwazo a kakar farko da sabon koci, Hansi Flick ya ja ragama, har ya kai ƙungiyar zagayen daf da karshe a Champions League.
Sai dai ta kasa kai wa karawar ƙarshe a gasar ta zakarun Turai, bayan da Inter Milan ta fitar da ita.
Ga jerin bajintar da Barcelona ta yi na kai wa ga nasara a kakar nan:
Barcelona ta ci wasa 44
A wasan ƙarshe da Barcelona ta buga a bana ranar Lahadi, ta doke Athletic Club 3-0 a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.
Kenan nasara ta 44 jimilla kenan a kakar da cin karawa 28 a La Liga da tara a Champions League da biyar a Copa del Rey da biyu a Spanish Super Cup.
Lewandowski ya ci ƙwallo 42

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Poland, Robert Lewandowski ya ci wa Barcelona ƙwallo 42 a dukkan karawa a 2024/25.
Tsohon ɗan wasan Bayern Munich ya zura 27 a La Liga da 11 a Champions League da uku a Copa del Rey da guda ɗaya a Spanish Super Cup.
Haka kuma ƙwallo biyun da Lewandowski ya ci Athletic Club a wasan ƙarshe ranar Lahadi, kenan ya zazzaga sama da 100 a ragar Barcelo.
Raphinha ne kan gaba a ƙwazo tsakanin ƴan wasa

Asalin hoton, Getty Images
A kan ci ƙwallo ne da zarar wani ya baka tamaula, abin da Raphinha ya ƙware kenan a 2024/25.
Ɗan ƙasar Brazil ya bayar da 22 aka zura a raga, Mohamed Salah ne kan gaba na Liverpool mai 23 a dukkan manyan gasar Turai, wato Premier League da La Liga da Serie A da Bundesliga da kuma Ligue 1.
Haka kuma Raphinha ya taka rawar gani a yawan buga wasanni a Barcelona, ya buga minti 4,661 kenan kaso 81 cikin 100.
Sai dai Pedri ne kan gaba da minti 4,643 da kuma Lamine Yamal mai minti 4,548, shi kuwa Jules Kounde ya yi minti 4,423 kafin ya ji rauni.
Barcelona ta zura ƙwallo 174 a raga
Barcelona ce kan gaba a yawan cin ƙwallaye a raga mai 174 a dukkan gasar Turai da aka yi a bana.
Paris Saint-Germain ce ta biyu mai ƙwallo 147, sai Bayern Munich mai 138 da Real Madrid mai 137 da kuma Liverpool mai 123 daga manyan gasar Turai biyar 2024/25.
Haka kuma ƙungiyar da Hansi Flick ke jan ragama ta buga shots 414, kenan kaso 66.51cikin 100 da raba ƙwallo kaso 88.43 cikin 100.
Haka kuma da cin ƙwallo 19 daga bani in baka 10.
Barcelona ta yi wasa 21 ƙwallo bai shiga raga ba
Barcelona ta buga karawa 21 ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba a kakar nan.
Daga ciki wasa ɗaya daga Marc ter Stegen da shida daga Iñaki Peña da kuma 14 a wajen Wojciech Szczęsny.
Hansi Flick ya yi amfani da ƴan wasa 30 a bana

Asalin hoton, Getty Images
A dukkan wasannin da Barcelona ta yi a bana, Flick ya yi amfani da ƴan wasa 30 ne.
Waɗanda ake sawa a kodayaushe har da Raphinha da Pedri da Lamine Yamal da kuma taimakaon matasa da ya haɗa da Dani Rodríguez da Toni Fernández da Andrés Cuenca, dukkansu sun taka rawar gani.
An fara cin Barca daga baya ta farke ta lashe karawar
Sau tara ana fara cin Barcelona a kakar bana daga baya ta sa ƙwazo ta farke har ta kai ta yi nasara a fafatawar.
Hansi Flick ba zai manta da ƙwazon da Barcelona ta yi ba a kan Real Madrid wadda ta fara cin ƙwallo a Spanish Super Cup da Copa del Rey daga baya aka doke ta.
Flick ya yi nasara karo huɗu a kan Real Madrid har da gida da waje a La Liga da lashe Copa del Rey da Spanish Super Cup a kan ƙungiyar Santiago Bernabeu.
Barcelona ta ci ƙwallo 23 daga wajen da'ira 18

Asalin hoton, Getty Images
Daga cikin ƙwallo 174 da Barcelona ta zura a raga a kakar nan, ta ci 23 daga wajen da'ira ta 19.
Lamine Yamal ne kan gaba, wanda ya zura bakwai a raga.
Barcelona ce kan gaba a wannan bajintar a dukkan manyan gasar Turai biyar, sai Real Madrid ta biyu mai 22da kuma Manchester City mai 18 a raga.
Barcelona ta samu maki 45 a wasannin waje
Cikin maki 88 da Barcelona ta hada a La Liga da ta kai ta lashe kofin kuma na 28 jimilla a 2024/25- ta samu 45 daga wasannin da ta buga a waje.
Ita ce kan gaba a wannan ƙwazon a manyan gasar Turai biyar, wadda take ta biyu ita ce Atalanta a gasar Serie A mai naki 42 points.











