Mummunan tarihin da Man United da Tottenham suka kafa a Premier ta bana

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham da Manchester United za su kara a wasan karshe a Europa League ranar Laraba.
Manchester United tana mataki na 16 da maki 39 a teburin Premier League da tazarar maki ɗaya tsakani da Tottenham ta 17.
Wannan shi ne karo na huɗu da za su kece raini a bana:
Premier League ranar Lahadi 16 ga watan Fabrairun 2025
- Tottenham 1 - 0 Man Utd
English League Cup ranar Alhamis 19 ga watan Disambar 2024
- Tottenham 4 - 3 Man Utd
Premier League ranar Lahadi 29 ga watan Satumbar 2024
- Man Utd 0 - 3 Tottenham
Ɗan wasan Manchester United, Joshua Zirkzee ya yi atisaye ranar Talata, bayan jinya da ya sha fama.
Haka shima Diogo Dalot da kuma Leny Yoro sun motsa jiki ranar Talata a filin atisayen United da ke Carrington.
Zirkzee, mai shekara 23 ya ji rauni ranar 13 ga watan Afirilu, inda kociyan United, Ruben Amorim ya ce ɗan kasar Netherlands ya kammala buga sauran wasannin bana.
Zirkzee ya ci wa United ƙwallo uku a kakar bana.
Yoro mai shekara 19 ya taka rawar gani a kakar nan a United, koda yake yana fama da rauni, wanda ya ji rauni a karawa da West Ham United ranar 11 ga watan Mayu,
The Europa League winner earns a place in next year's Champions League.
Wasu batutawan kan wasan Tottenham da Man United

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ƙungiyoyin biyu sun kasa taka rawar gani a Premier
Ba wanda zai ce maka Manchester United da Tottenham za su tsinci kansu a matakin ƴan can kasan teburi a Premier Leage a bana.
United tana ta 16 a kasan teburi da maki 39 tana buga kaka mafi muni tun bayan 1973/74.
Ita kuwa Tottenham, wadda take ta 17 da tazarar maki ɗaya da United, an doke ta karo 21 a Premier League a kakar nan.
Kenan lashe wannan kofin shi ne zai kawo karshen kalubalen da kociyoyin ƙungiyar ke fuskanta.
Kuma duk wadda ta lashe Europa League, za ta buga Champions League a kaka mai zuwa.
Ko Tottenham za ta kawo karshen kaka 17 rabon da ta lashe kofi?
Wannan wasan karshen dama ce ga Tottenham ta lashe babban kofi a tarihi, tun bayan ɗaukar kofin gida League Cup a 2008, wadda rabonta da na zakarun Turai tun bayan lashe UEFA Cup a1984 UEFA.
Ko Amorim zai samu sauki kan matsin da ke gabansa?
Ruben Amorim ya kwan da sanin lashe kofin nan na Europa, zai samu saukin gudanar da aikinsa nan gaba a United, wanda ya maye gurbin Erik ten Hag.
Idan har United ba ta lashe Europa League ba, zai zama karon farko da ba za ta buga gasar zakarun Turai ba tun 2014/15.
Kenan da zarar United ta ɗauki kofin zai ba ta damar shiga gasar Champions League a baɗi.
Bilbao zai karɓi bakuncin karawa tsakanin manyan kungiyoyin Ingila biyu
Filin wasa naSan Mames zai karɓi bakuncin wasan karshe tsakanin Tottenham da Manchester United ranar Laraba a gasar Europa League.
Tuni Sifaniya take fargabar hatsaniya tsakanin magoya bayan ƙungiyoyin biyu, waɗan da za su je kallon fafatawar.
Tuni ake tunanin da yawa za su je Sifaniya ba tare da tikiti ba, sannan ga masu kallo tamaula ana shan barasa da sauran batutuwan da ake hasashen za su iya kawo hatsaniya.
Ko a wasan da Manchester United ta buga da Athletic Bilbao, an sa ran za a samu rashin jituwa, amma sai aka ga akasin hakan.
Yadda aka tanadi tsaro a birnin Bilbao

Asalin hoton, Getty Images
Birnin Bilbao na san karɓar bakuncin magoya baya 50,000 daga Ingila a wasan karshen a Europa League tsakanin Tottenham da Manchester United.
Tuni mahukuntan Sifaniya suka tanadi tsaro a filin wasan Athletic Bilbao da ake kira San Mames Stadium, inda aka kafa katanga mai tsawo da shinge mai ɗauke da ƙaya.
Sama da jami'an tsara 3,000 aka tanada a birnin, waɗan da za su kula da tsaro da tabbatar da bn doka da oda da samar da shingen da sai mai ɗauke da tikiti ne zai wuce zuwa sitadiya.
An kuma tanadi wajen zaman ƴan kallo a wajen birnin ga waɗan da ba su da tikitin shiga stadiya, inda aka tanadi abubuwan more rayuwa har da lita 60,000 na barasa, domin tattatasu a waje ɗaya dom magance matsala.
Tuni kuɗin wurin kwana da na otal otal ya yi tashin gwauron zabo a birnin Bilbao, inda yake da karancin otal, wasu da dama sun tsaya a Cantabria da Gipuzkoa ko Alava, in da bai da nisa zuwa Bilbao.
An kuma tanadi matakan tsaro a filin tashi da saukar jirgin sama da tashar jirgin kasa da bakin iyakar kasar.
An kuma tsara yadda za a saukaka zirga-zirga tsakanin magoya baya, inda aka tanadi jiragen sama na ƙawa 174.
Duk da tsare-tsaren da birnin Bilbao ke yi ba zai kai wanda aka yi a Sevilla ba, wanda ya ɗauki ƴan kallo 150,000 a wasan karshe a Europa League tsakanin Rangers da Eintracht Frankfurt.
Tuni dai birnin na Bilbao ya fara ɗaukar harama a wasan karshe tsakanin Tottenham da Manchester United tun daga ranar Talata.
Mummunan tarihin da Tottenham da Man United suka yi a Premier a bana

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United
A bara Manchester United ta kare a mataki na takwas a teburin Premier League, shi ne gurbi mafi muni a babbar gasar tamaula ta Ingila.
Sai a wannan kakar United ta yi kasa zuwa mataki na 16 da maki 39, duk runtsi sai dai United ta kare a mataki na 14 koda za ta yi nasara a wasan karshe, sannan wasu karawar ta ranar Lahadi su yi mata kyau - kenan za ta yi fatan a doke Wolverhampton da kuma West Ham a wasansu na karshe.
Haka kuma United za ta kare da tarihin karacin lashe wasa 11 da maki 42, idan ta yi nasarar doke Aston Villa kenan ranar Lahadi.
Idan ka kwatanta da cin wasa 16 da maki 58 a kakar 2021/22.
An ci United wasa 18 a Premier League, kenan ta samu kari karo huɗu a kan yawan wasannin da aka doke ta a bara.
Haka kuma wasa tara a jere ba tare da nasara ba, ya haura yawan bakwai da ta yi a 1992.
Haka kuma United ta zura ƙwallo 42 a raga a Premier League, sai ta ɗura bakwai a ragar Aston Villa ranar Lahadi, shi ne za ta yi kan-kan-kan da 49 da ta ci a 2015/16, wato kakar da ta yi karancin zura ƙwallaye a raga.
An kuma zura mata 54 a bana, yayin da aka ɗura mata 57 a 2021/22 da kuma 58 a bara.
Wannan ce kakar da ƴan wasan United aka kasa samun wanda ya ci ƙwallo 10 jo fiye da haka, sai idan Bruno zai Ci Aston Villa biyu ko kuma Amad Diallo ya ci uku a ranar Lahadi.
United ta kori Erik ten Hag a cikin watan Nuwamba, wata huɗu tsakani, bayan da ya tsawaita ƙwantiragin ci gaba da horar da tamaula a Old Trafford.
Daga nan ta maye gurbinsa da Ruben Amorin daga Portugal, wanda ya yi nasara da yawa fiye da yawan wasannin da ya ci, shi ne kociya mafi muni a yawan kasa cin wasanni tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a United.
Tottenham

Asalin hoton, Getty Images
Tottenham tana mataki na 17 a teburin Premier League, wadda a baya ta taɓa karwa a matsayi na 15 a 1993/94 da a mataki na 14 har karo biyu.
Kenan tana fatan yin nasara a kan Brighton ranar Lahadi, sannan a doke Wolverhampton da kuma West Ham, shi ne zai sa ta kara yin sama daga gurbin da take.
An doke ta sau 21 a Premier League rashin ƙwazo mai kyau a tarihin gasar a wajenta.
Haka kuma wasa 11 ta ci, kuma saura karawa ɗaya ta ragae ranar Lahadi, idan ba haka ba za ta kare a matakin karancin wasanni a kakar nan.
Za kuma ta kare da karancin maki 38 ko kuma 41 da zarar ta yi nasara ranar Lahadi.
Kakar da ta kare da karancin maki ita ce a 1997/98 da maki 44 da kuma maki 45 a 1993/94 bayan wasa 42.
Duk da cin ƙwallo 63, Tottenham za ta kare a kasa-kasan teburi a tarihi, wadda ta yi wannan tarihin bayn cin ƙwallaye da yawa ita ce Manchester City a 2003/04, wadda ta kare a matsayi na 16 a lokacin.
Koci, Ange Postecoglou ya sanar a cikin watan Satumba cewar ''Ina cin kofi a kaka ta biyu a kan aikin horar da tamaula. Hakan bai canja ba.
Ranar Laraba dama ce ga kociyan na ɗaukar kofi kamar yadda ya sanar, wanda ya horar da tamaula a South Melbourne da Brisbane Roar da Yokohama F. Marinos da Celtic da matasan tawagar Australia ƴan kasa da shekara da ta 20 da babbar ƙungiyar kasar.











