Me kuke son sani kan wasan Champions League da za a yi ranar Talata?

Asalin hoton, Getty Images
Za a buga wasa tara a Champions League ranar Talata da ƙungiyoyi 18 za su kece raini a tsakaninsu.
Kenan za a ci gaba da wasan zagaye na biyar-biyar a cikin rukuni da ake sa ran samun waɗanda za su kai zagayen ƴan 16 a babbar gasar tamaula ta nahiyar Turai ta bana.
Kawo yanzu ƙungiya uku ce take da maki 12 kowacce - da ta haɗa da Bayern Munich da Arsenal da Inter Milan da Manchester City ta huɗu mai maki 10 da kuma Paris St Germain mai rike da kofin mai maki tara ta biyar a teburi.
Waɗanda suke na karshen teburi sun haɗa da Benfica da Ajax da ba su da maki ko ɗaya daga karawa hurhuɗu a cikin rukuni.
Duk kungiyar da ta kare daga matakin farko a teburi zuwa ta 16 ne za su je zagaye na biyu a babbar gasar tamaula ta zakarun Turai ta kakar nan.
Wasannin da za a buga ranar Talata:
- Ajax da Benfica
- Galatasaray da Union Saint-Gilloise
- Bodø / Glimt da Juventus
- Borussia Dortmund da Villarreal
- Chelsea da Barcelona
- Manchester City da Bayer Leverkusen
- Marseille da Newcastle United
- Napoli da Qarabağ
- Slavia Prague da na Athletic Club
Ajax da Benfica
Ajax da Benfica ne kaɗai da ba wadda take da maki kawo yanzu a wasannin Champions League, bayan wasa hurhuɗu a cikin rukuni a kakar 2025/26.
Wannan shi ne karo na 10 da za su fuskanci juna a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai, inda Benfica ta yi nasara biyu da Ajax ta ci huɗu da canjaras huɗu.
Portugal ce ta yi nasarar cin Ajax 1-0 a Amsterdam a wasa na biyu da suka fuskanci juna a 2021/22 zagayen ƴan 16.
An doke Ajax wasa bakwai a gasar Zakarun Turai, karon farko da ta daɗe da yin rashin nasara da yawa a tarihin ƙungiyar a gasar.
Idan da Ajax za ta zura ƙwallo uku ko fiye da haka, za ta zama ta farko daga Netherlands da za ta ci 400 ko fiye da haka a European Cup ko kuma Champions League.
Wasa biyu Benfica ta yi rashin nasara daga 19 baya a gasar Zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Netherland, yayin da ta ci tara da canjaras takwas.
Ƙungiyar da Jose Mourinho ke jan ragama ba ta ci ƙwallo ba a karawa uku baya a Champions League.
Galatasaray da Union Saint-Gilloise

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shi ne karon farko da ƙungiyoyin biyu za su kara a gasar Zakarun Turai a tsakaninsu.
Sai dai Galatasaray ta zura ƙwallo 29 a wasa 31 baya a gasar Zakarun Turai, kuma Victor Osimhen ya ci ƙwallo a dukkan karawa takwas baya tun daga bara.
Ɗan wasan tawagar Najeriya ya zura 12 a raga.
Ƙungiyar ta Turkiya na fatan lashe wasa biyu a jere a Champions League a karon farko a tarihin gasar.
Ba a doke ta ba a wasa bakwai a gida, a baya-bayan nan a gasar, da rashin nasara biyu daga fafatawa 12 a cikin rukuni.
Wannan ne karo na huɗu da Union SG za ta fuskanci ƙungiyar Turkiya a gasar Zakarun Turai.
Wasa ukun da ta yi duk ta kara ne da Fenerbahce, wadda ta ci karo daya da rashin nasara biyu - na baya-bayan nan 2-1 da aka doke ta a 2024/25.
Dukkan wasa huɗu baya da ƙungiyoyin Belgium ke yi a Champions League na cin ƙwallo huɗu.
Union SG ta sha kashi a karawa uku a Champions League.
Borussia Dortmund da Villarreal

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan shi ne karon farko da ƙungiyoyin za su kara a tsakaninsu a Champions League, duk da cewa Borussia Dortmund ta fuskanci ƙungiyar Sifaniya karo 44, ita kuwa Villareal ta kece raini da na Jamus sau 14 a gasar Zakarun Turai.
Dortmund na bukatar cin ƙwallo biyu su zama 350 da ta zura a raga ko dai a European Cup ko kuma Champions League.
An ci ƙwallo 43 a wasa 10 da Dortmund ta fuskanci kungiyoyin Sifaniya a gasar Zakarun Turai.
Wasa ɗaya ƙungiyar ta Jamus ta yi rashin nasara daga 19 baya da ta yi a gida a Champions League da yin nasara 12 da canjaras shida.
Serhou Guirassy na Dortmund ya zura ƙwallo 10 a raga a wasannin gida a Champions League.
Villareal ba ta yi rashin nasara ba a wasa shida da ta kece raini da ƙungiyar Jamus a gasar Zakarun Turai da cin biyu da canjaras hudu - kuma karawa uku baya aka doke ta a wasa 14 baya da cin shida da canjaras biyar.
To sai dai ƙungiyar ta Sifaniya ba ta ci wasa ba a karawa bakwai baya ba, a Champions League da canjaras biyu da rashin nasara biyar.
Chelsea da Barcelona

Asalin hoton, Getty Images
Chelsea da Barcelona sun haɗu karo 14 a gasar Zakarun Turai, kowacce ta yi nasara hudu da canjaras shida.
Wannan shi ne karon farko da za su kara tun bayan 2017/18 a Champions League zagayen ƴan 16, bayan da Barcelona ta kai zagayen gaba da cin 4-1 gida da waje, bayan tashi 1-1 a Stamford Bridge, sannan ta ci 3-0 a Sifaniya.
Wasa ɗaya ne aka doke Chelsea daga bakwai baya a gasar Zakarun Turai a gida da ta fuskanci Barcelona, wadda ta yi ci hudu da canjaras biyu a Stamford Bridge.
Haka kuma Chelsea ta kasa cin wasa biyu a fafatawa 61 baya a gasar Zakarun Turai a gida, sannan ba ta yi rashin nasara ba a fafatawa 16, wadda ta ci 12 da canjaras huɗu - tun bayan doke ta 1-0 a hannun Valencia a Champions League a cikin Satumbar 2019.
Barcelona ta yi rashin nasara uku daga wasa 20 a Champions League da ta fuskanci ƙungiyar Ingila, bayan cin 13 da canjaras huɗu da kuma rashin nasara ɗaya daga fafatawa 11 baya ga cin karawa takwas da canjaras biyu daga ciki.
Lamine Yamal, wanda zai cika shekara 18 da kwana 135 ranar Talata ya ci ƙwallo bakwai a Champions League kafin ya cika shekara 19 da haihuwa.
Yana buƙatar zura uku a raga ya yi kan-kan-kan da tarihin Kylian Mbappe.
Barcelona ta zura ƙwallo 96 a raga a wasa 20 baya a Champions League.
Bodø/Glimt da Juventus

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shi ne karon farko da za a kece raini tsakanin ƙungiyoyin a gasar Zakarun Turai.
Bodø/Glimt ta yi nasara huɗu a gasar Zakarun Turai a gida da ta karbi bakuncin kungiyoyin Italiya.
Ita kuwa Juventus, ba ta yi rashin nasara ba a wasa takwas a gasar Zakarun Turai da ta kara da ƙungiyoyin Norway, inda ta yi nasara hudu a Italiya da cin huɗu a Norway.
Mai masaukin baƙi na fatan zama ta farko daga Norway da za ta ci wasa a Champions League tun bayan bajintar Rosenborg da ta yi nasara biyu a jere a kan Valencia a fafatawar cikin rukuni a 2007/08.
Juventus na buƙatar cin ƙwallo biyu nan gaba ta zama ta farko da za ta sharara na 500 a gasar European Cup ko kuma a Champions League.
Manchester City da Leverkusen

Asalin hoton, Getty Images
Wannan shi ne karon farko da za su ɓarje gumi a tsakaninsu
Wasa ɗaya aka ci Manchester City a karawa 24 baya a gasar Zakarun Turai da ta fuskanci ƙungiyoyin Jamus, da yin nasara 19 da canjaras huɗu.
Ita kuwa Leverkusen nasara ɗaya ta yi daga wasa 12 da ta kai ziyara ga ƙungiyoyin Ingila daga ciki aka doke ta takwas da canjaras uku.
City, wadda har yanzu ba ta yi rashin nasara ba a wasa 23 a Etihad, ta ci karawa 20 da canjaras uku a gasar ta Zakarun Turai, inda take neman ƙwallo uku a raga su cika 300 da za ta zazzaga a Champions League.
Erling Haaland ya ci ƙwallo a dukkan wasa biyar a Champions League kuma karo na uku a tarihinsa na taka leda.
Yana fatan cin ƙwallo karo na shida a jere, kuma a karo na biyu, bayan da ya taɓa yin wannan bajintar tsakanin ranar 20 ga watan Oktoban 2020 zuwa Satumbar watan Maris ɗin 2021 lokacin yana taka leda a Dortmund.
Haka kuma ya ci ƙwallo 10 a wasa tara a Champions League da ya fuskanci ƙungiyoyin Jamus.
Leverkusen ta sha kashi karo uku a wasa 20 baya a Champions League da yin nasara 12 da canjaras biyar daga ciki.
Idan har Leverkusen ta ci City, zai zama karo na 50 da ƙungiyar ta Jamus ta yi nasara a wasannin Champions League a tarihi.
Har yanzu Claudio Echeverri na Leverkusen na fatan cin ƙwallo a karon farko a Champions League, wanda ke buga wasannin aro daga Manchester City.
Ya buga wa kungiyar Jamus wasan Bundesliga huɗu a kakar nan.
Marseille da Newcastle United

Asalin hoton, Getty Images
Wasa na uku kenan da ƙungiyoyin za su fafata a tsakaninsu.
Sun kara a zagayen daf da karshe a 2003/04 a UEFA Cup, sun kuma tashi ba ci a Ingila, amma a karawa ta biyu a Faransa, Marseille ta ci 2-0 ta kai zagayen karshe.
Marseille ba ta ci wasa ba daga fafatawa 12 a gasar Zakarun Turai da ta kece raini da ƙungiyoyin Ingila, daga ciki aka doke ta a tara da canjaras uku.
Wasa 24 baya da Marseille ta buga ba canjaras a Champions League tun bayan da ta tashi 0-0 da Arsenal ranar 1 ga watan Nuwambar 2011.
Wasa biyu ne Newcastle ta rasa daga tara baya a gasar Zakarun Turai da ta fafata da ƙungiyoyin Faransa, inda daga ciki ta yi nasara uku da canjaras huɗu.
Haka kuma Newcastle United ta yi nasara uku a Champions League ba tare da ƙwallo ya shiga ragarta ba, amma ba ta taɓa cin wasa huɗu ba a jere a gasar.
Kuma karawa biyu aka ci Newcastle a wasa 13 a gasar Zakarun Turai a fafatawar gida, wadda ta yi nasara biyar da canjaras shida.
Slavia Praha da Athletic Club
Wasan da suka fuskanci juna a tsakaninsu a gasar Zakarun Turai tsakanin Slavia Praha da Athletic Club an yi shi a 2024/25 a Europa League, inda Athletic Club ta yi nasarar cin 1-0 a gida.
Slavia Praha ba ta ci wasa ba a fafatawa 15 baya ba a Champions League, inda daga ciki ta yi canjaras shida aka doke ta sau tara tun daga watan Satumbar 2007.
Ƙungiyar ta Jamhuriyar Czech ta ci wasa biyu daga 15 a gasar Zakarun Turai da ta kece raini da na Sifaniya da yin canjaras shida da rashin nasara bakwai.
Athletic Club ta ci wasa biyu baya a gasar Zakarun Turai da ƙungiyar Jamhuhiyar Czech, kuma duka a bara a Europa League.
Athletic Club ta yi rashin nasara shida a gasar Zakarun Turai da cin wasa ɗaya. Haka kuma ba ta ci wasa ba a fafatawa shida da ta yi a waje ba, da canjaras ɗaya aka doke ta a biyar daga ciki.
Napoli da Qarabağ

Asalin hoton, Getty Images
Wannan ne karon farko da za su fuskanci juna a tsakaninsu, kuma karon farko da Napoli za ta kece raini da ƙungiya daga Azerbaijan.
Napoli ta yi rashin nasara ɗaya a karawa 19 baya a Champions League a gida da cin 11 da canjaras bakwai.
Idan har Napoli ba ta ci ƙwallo ba ranar Talata, zai zama karo biyu a jere ba ta zura ƙwallo ba a Champions League a tarihi.
Qarabag ta yi wasa shida ba tare da nasara ba a gasar Zakarun Turai da ƙungiyoyin Italiya da yin canjaras daya daga ciki aka doke ta a biyar - an kuma doke ta a dukkan wasa uku da ta buga a waje.
Leandro Andrade ya ci ƙwallo a dukkan wasa biyar da ya buga wa Qarabağ a fafatawa shida baya a gasar ta Zakarun Turai.
Sai dai an doke ƙungiyar ta Azerbaijan wasa biyu a karawa 10 a gasar Zakarun Turai a kakar nan.










