Mahaifin matashiyar da ta mutu a hannun 'yan Hizban Iran ya ce an masa ƙarya

Mahsa Amini

Asalin hoton, MAHSA AMINI FAMILY

Bayanan hoto, Mahsa Amini ta mjutu ranar Juma'a, kwana uku bayan ta fadi a ofishin 'yan Hisbah inda take tsare

Mahaifin Mahsa Amini, matashiya 'yar shekara 22 wadda mutuwarta ta janyo jerin zanga-zanga a fadin ƙasar Iran, ya zargi hukumomi da tafka ƙarya.

Yayin zantawa da Sashen BBC Persian, Amjad Amini ya ce ba a bar shi ya ga rahoton binciken sanadin mutuwar 'yarsa ba, kuma ya musanta cewa da ma Mahsa ba ta da lafiya.

Ya ce shaidu sun fada wa dangin matashiyar cewa 'yan Hizban sun lakada mata duka lokacin da take hannunsu.

Hukumomin Iran sun musanta haka.

An tsare Mahsa Amini bisa zargin karya dokokin sa hijabi.

Matar wadda 'yar ƙabilar Kurdawa daga birnin Saqez na arewa maso yamma ce, ta mutu a asibiti cikin birnin Tehran ranar Juma'a, bayan ta shafe tsawon kwana uku a sume.

Kame Hukumomin Iran sun ce ba a ci mutuncin Mahsa Amini ba, kawai dai ta gamu da "bugawar zuciya ne haka kwatsam" bayan 'yan Hizban Iran sun tsare ta a birnin Tehran.

Sai dai mahaifin matashiyar ya ce an fada wa ƙaninta, Kiarash dan shekara 17 da ke wurin lokacin da aka tsare ta cewa an doki 'yar'uwar tasa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Suna tare da dana. Wasu shaidu sun fada wa dan nawa cewa an doki yayarsa a cikin mota da kuma a ofishin 'yan Hizba," a cewarsa.

"Dana ya roke su kada su tafi da ita, amma shi ma suka doke shi, aka kyakketa masa tufafi.

"Na tambaye su ko za su nuna min abin da ya faru a bidiyon kyamarorin da 'yan Hizban ke maƙalawa? Sai suka ce baturan kyamarorin sun mutu a lokacin."

Hukumomin Iran sun ce Mahsa Amini na sanye da tufafin da bai dace ba a lokacin da aka kama ta.

Sai dai Mahaifin Mahsa ya ce 'yarsa a ko da yaushe tana yafa doguwar abaya.

Dakatarwar ma'aikatan lafiya

Amjad Amini ya kuma ce ma'aikatan lafiya sun sha hana shi zuwa ganin gawar 'yarsa bayan mutuwarta.

"Na so ganin 'yata, amma ba su bar ni na shiga ba," in ji shi.

Ya ce lokacin da ya tambaya don a ba shi rahoton binciken sanadin mutuwar 'yarsa, sai likitoci in ji, suka ce: "Na je na yi duk abin da zan yi, don kuwa babu abin da zan iya da rahoto."

Zanga-zanga kan mutuwar Mahsa Amini ta watsu zuwa fiye da birane 20 na kasar Iran

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zanga kan mutuwar Mahsa Amini ta watsu zuwa fiye da birane 20 na kasar Iran

Ya ce babu bayani game da rahoton binciken sanadin mutuwar da aka bai wa iyayen matashiyar.

Amjad Amini kawai ganin gawar 'yarsa ya yi bayan an kammala yi mata sutura, za a binne ta, a lokacin kuma kafafuwa da fuskarta kawai ake gani.

"Akwai ƙwarzane da dama a kafafuwanta," in ji shi. "Na tambayi likitoci su bincika kafar."

Ya ce hukumomi sun yi alƙawarin yin bincike kan sanadin raunukan amma ban sake jin komai daga gare su ba.

"Sun yi biris da ni. A yanzu na tabbatar ƙarya suke yi."

A wata sanarwar da aka fitar kafin nan, Mehdi Faruzesh, babban daraktan aikin likitancin binciken laifuka a lardin Tehran, ya ce: "Babu alamun raunuka daga kanta har zuwa fuska, babu ƙwarzane a kusa da idanunta ko wata karaya da aka gani a tushen kwanyar matashiyar."

Hukumomi sun ce babu alamun jin raunuka a cikin cikinta.

Zarge-zargen Lafiya

Amjad Amini ya kuma soki lamirin iƙirarin cewa 'yarsa na da rashin lafiyar da ta zama sanadin mutuwarta.

Babban daraktan likitancin binciken laifuka na lardin Tehran ya ce Mahsa Amini an taba yi wa Mahsa tiyata a ƙwaƙwalwa tun tana da shekara takwas.

Amjad Amini ya ce "ƙarya suke yi".

"Ba a taba kai ta wani asibiti a cikin shekara 22 ba, in ban da rashin lafiya ƙalilan da ta riƙa yi masu alaƙa da mura".

"Ba ta taba samun wata babbar larura ba, ba a taba yi mata tiyata ba."

Mutuwar Mahsa Amini ta janyo zanga-zanga a Iran da wasu sassan duniya

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutuwar Mahsa Amini ta janyo zanga-zanga a Iran da wasu sassan duniya

BBC ta zanta da ƙawayen Mahsa Amini guda biyu wadanda suka ce ba su da masaniyar an taba kwantar da ita a asibiti.

Amjad Amini ya kuma musanta wani iƙirari game da lafiyar 'yarsa Mahsa kuma ta sha yanke jiki tana faduwa kuma kwanan nan ta taba suma lokacin da ta je sayayya a kanti, inda ya ce duk "labaran ƙarya ne".

Burin Shiga Jami'a

A cewar iyayenta, Mahsa Amini cikin makon gobe ya kamata ta fara karatu a jami'a.

Tafiyarsu zuwa Tehran kamata ya yi ta kasance ta hutunta na ƙarshe kafin ta fara karatun kwas dinta.

"Tana son ta karanci kimiyyar 'yan ƙanƙanan halittu (microbiology)," in ji Amjad.

"Tana son ta zama likita - burinta ke nan da ba zai taba cika ba.

"Mahaifiyarta tana fama da tsananin rashin lafiya, duka kuma muna kewar ta.

"Ranar Larabar da ta wuce ta cika shekara 23 da haihuwa."