Jami'an Hisban da ke tabbatar da mata sun bi dokar saka Hijabi a Iran

/

Asalin hoton, Getty Images

Rasuwar matashiyar nan mai shekara 22 mai suna Mahsa Amini wadda ta rasu a hannun jami'an tsaro ya jawo zanga-zanga matua a ƙasar Iran, inda aka ga mata suna fitowa suna ƙona kallabi.

Suna ƙona kallabin ne domin nuna turjiya kan dokokin saka kaya da gwamnatin Musulunci ta ƙasar ta saka.

Yan sandan Gasht-e Ershad waɗanda yan sanda ne na musamman da aka ɗora wa alhakin kula da tarbiyyar Musulunci da kuma kama duk wanda ya yi kunnen ƙashi su ne suka kama yarinyar.

A ƙarƙashin dokokin ƙasar Iran waɗanda an kafa su ne bisa turbar Addinin Musulunci, an umarci mata da su rufe kansu da kallabi da kuma saka dogayen kaya waɗanda ba su ɗame jiki ba.

Ana zargin Ms Amini ta bar gashinta ya fito a ƙarƙashin kallabinta a lokacin da jami'an hisban ƙasar suka kamata a Tehran a ranar 13 ga watan Satumba.

Ta yi doguwar suma bayan ta fadi a wurin da ake tsare da ita inda bayan kwana uku ta kuma rasu a asibiti.

Yan sandan Hisban sun musanta zargin da ake yi kan cewa sun daki kanta da katako kuma sun buga kanta a jikin mota.

...

Asalin hoton, Mahsa Amini family

A wata tattaunawa da ba su saba yi ba, ɗaya daga cikin ƴan sandan hisban ƙasar ya yi hira da BBC a ɓoye kan yanayin aikin nasu.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Sun shaida mana dalilin da ya sa muke aiki da hisban ƙasar shi ne mu kare mata, in ji shi. " Saboda idan ba su yi shiga mai kyau ba, ran maza zai iya ɓaci su illata su."

Sun ce suna yawo ne mutum shida-shida, kowane rukuni kan ƙunshi maza huɗu da mata biyu kuma sun fi mayar da hankali ne kan wuraren da ake tafiya da ƙafa da kuma wurare da jama'a suke taruwa.

"Wani abu ne bambaraƙwai sakamakon idan aikinmu shi ne mu nuna wa jama'a hanya, mene ne amfanin zuwa wuraren da ake samun cunkoson jama'a wanda hakan ke nufin za mu kama ƙarin magana?"

"Wannan na nufin za mu tafi farauta ne kenan."

Jami'in na hisbah ya bayyana cewa kwamandansa na yawan ce masa ba ya aiki da kyau idan bai gano mutane da dama ba waɗanda suka saɓa dokar saka kaya, kuma yana fuskantar ƙalubale matuƙa idan mutane suka ƙi yarda a kama su.

"Ana so idan mun kama mu tura su ƙarfi da yaji cikin mota. Kun san ko sau nawa na zubar da hawaye idan ina hakan?

"Ina so na shaida musu cewa ba na cikinsu. Akasarinmu sojoji ne kawai da muke aikinmu na soja wanda aka tilasta mana. Ba na jin daɗi."

Dokokin da aka yi bayan juyin-juya hali

An soma yaƙi da saka kayan da ba su dace ba a Iran tun a 1979 bayan da aka yi juyin-juya hali na Iran, wanda a lokacin ake so mata su rinƙa shiga ta mutunci.

Duk da cewa a lokacin akwai mata da dama da ke rufe jikinsu, batun saka gutun siket da barin kai a buɗe ba abu bane da aka saba gani ba a kan titunan Tehran kafin da aka hamɓarar da gwamnatin Shah Mohammad Reza Pahlavi

..

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zangar da wasu mata a Iran suka yi a 1979 da kansu a buɗe

Sai dai watanni bayan kafa Jamhuriyyar Musulunci a Iran, dokokin da suka rina kare hakkin mata waɗanda aka yi a lokacin mulkin Shah sai aka rinƙa soke su.

"Ba wai a dare ɗaya aka yi hakan ba, an bi matakai daki-daki" in ji Mehrangiz Kar, mai shekara 78, wanda lauyan kare haƙƙin bil adama ne kuma ɗan gagwarmaya wanda ya taimaka wurin shirya zanga-zangar yaƙi da saka hijabi.

"Bayan juyin-juya halin, an samu maza da matan da suka fito kan tituna suna bayar da kallabi kyauta ga mata."

..

Asalin hoton, Getty Images

A ranar 7 ga watan Maris, shugaban juyin-juya halin, Ayatollah Ruhollah Khomeini ya saka doka kan cewa dole ne mata su saka hijabi domin zuwa wuraren aiki kuma duk macen da ba ta rufe jikinta ba tamkar tsirara take.

"Waɗannan kalaman sun shiga kunnuwan masu juyin-juya hali da dama inda suka yi amfani da kiran a matsayin umarni domin tilasta wa mata saka hijab," in ji Mrs Kar, wanda ke zaune a Washington.

"Da dama sun ɗauka wannan lamarin zai faru ne kawai a dare ɗaya, kawai sai mata suka soma nuna turjiya."

Sama da mutum 100,000 waɗanda akasarinsu mata ne suka taru a kan titunan Tehran washe gari - a Ranar Mata ta Duniya domin yin zanga-zanga.

'Mun ƙirƙiro da sabon salo'

Duk da umarnin da Ayatollah Khomeini ya bayar, an ɗauki lokaci kafin hukumomi suka yanke shawarar kan abin da za a kira shigar da ta dace.

"Babu wani takamaimain umarnin da aka bayar, sai suka rinƙa fitowa da hotuna da manyan alluna.

Sai suka ce lallai ne mata su bi wannan umarnin da aka bayar ko kuma ba za su iya shiga ba," in ji Mrs Kar.

..

Asalin hoton, Getty Images

Zuwa 1981, sai aka buƙaci a hukumance mata da ƴan mata su saka kaya na mutunci. A taƙaice hakan na nufin su saka doguwar riga wadda a wani lokaci take ɗauke da ɗankwali wadda za ta rufe har da hannuwansu.

"Duk da haka sai muka ci gaba da faɗa kan saka hijabi. Sai da kanmu muka ƙirƙiro saka ɗankwali ko kuma ƙin rufe kanmu da kyau," In ji Mrs Kar.

"Duk lokacin da suka tare mu, muna yin fada da su."

A 1983, sai majalisa ta yi doka kan duk macen da ba ta rufe kanta da kyau ba za a yi mata bulala 74. A ƴan kwanakin nan ma sai aka ƙara da hukuncin zaman gidan yari na kwanaki 60.