Yadda rashin saka hijabi ya janyo mutuwar matashiya a hannun ƴan sandan Iran

.

Asalin hoton, MAHSA AMINI FAMILY

Bayanan hoto, Ƴan sanda sun ƙaryata rahotannin shaidu cewa an yi wa Mahsa Amini duka

Wata matashiya ƴar Iran mai shekara 22 ta mutu ƴan kwanaki bayan ƴan sandan tabbatar da ɗa’a sun tsare ta saboda zarginta da rashin mutunta dokokin da suka shafi rufe kai.

Shaidu sun ce an yi wa Mahsa Amini duka cikin motar ƴan sandan a lokacin da suka ɗauke ta a Tehran ranar Talata.

Ƴan sanda dai sun musanta zarge-zargen inda suka ce Ms Amini ta gamu da matsalar ciwon zuciya ɓakatatan.

Wannan dai shi ne lamari na baya-bayan nan a jerin rahotannin cin zarafin mata da hukumomi suka yi a Iran a makonnin da suka gabata.

Iyalan Ms Amini sun ce matashiya ce mai ƙoshin lafiya kuma ba ta da wata larura da za a iya cewa kwatsam ta janyo mata ciwon zuciya.

Sai dai an faɗa musu cewa an kai ta asibiti ƴan sa’oi bayan kama ta inda ƴan uwan nata suka ce ta kasance cikin yanayin doguwar suma kafin mutuwarta ranar Juma’a.

Ƴan sanda a Tehran sun ce an cafke Ms Amini saboda hijabi, suturar da ta zama dole mata su sanya.

Mutuwarta ta zo ne dai-dai lokacin da ake samun ƙaruwar rahotannin cin zarafin mata ciki har da waɗanda ake zargi da rashin suturta jikinsu bisa tsarin addinin musulunci da ake hana su shiga ofisoshin gwamnati da bankuna.

Iraniyawa da dama, har da masu goyon bayan gwamnati na bayyana fushinsu a kafafen sada zumunta game da jami’an sintirin da aka yi wa laƙabi da Guidance Patrols inda suke amfani da maudu’ai da ke bayyana su a matsayin ƴan sintiri na kisan kai.

Hotunan bidiyo sun ɓulla a kafafen sada zumunta da ke nuna yadda jami’ai ke tsare mata, suna jan su a ƙasa kuma suna fizgarsu, su tafi da su.

Ƴan Iran da dama, kai tsaye, sun zargi Jagoran addini, Ali Khamenei. Ana ta yaɗa wani daɗaɗɗen jawabi da ya taɓa yi a shafukan sada zumunta inda a jawabin nasa yake kare rawar da 'ƴan sintirin ke takawa inda ya jaddada cewa a ƙarƙashin dokokin musulunci, dole ne a tilasta wa mata su girmama tsarin suturta jiki na musulunci.

Wannan lamari dai zai ƙara zurfafa rarrabuwar kai tsakanin ɓangaren matasan Iran da masu riƙe da madafun iko – wata ɓaraka da ake ganin za ta yi wahalar ɗinkewa.