'An tilasta min ajiye aiki saboda wallafa hotunana da ɗan kamfai'

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar jami'a mai zaman kanta da ke Kolkata a gabashin Indiya da a baya ake kira Calcutta ta faɗa cikin wata taƙaddama a watannin baya-bayan nan.
Wata tsohuwar malama da ta kai matakin mataimakiyar Farfesa a Jami'ar St Xavier ta faɗa wa BBC cewa an tilasta mata ajiye aiki ne saboda wallafa hotunanta a shafin Instagram sanye da kamfai - zargin da hukumomin jami'ar suka musanta.
Matar mai shekara 31 a duniya wadda ta buƙaci a ɓoye sunanta, ta zargi jami'an jami'ar da cin zarafinta sannan ta ce ta fuskanci tsangwama da tsauraran dokoki.
Tuni ta shigar da ƙara gaban ƴan sanda kuma an aikewa jami'ar takardar shigar da ita ƙara kuma tuni ta mayar da martani tana zargin malamar da ɓata wa jami'ar suna da kuma neman diyyar rupee 990m (kimanin $12.4m; £10.5).
'Yadda aka yi mani tambayoyin titsiye'
Mataimakiyar Farfesan ta ce ta fara aiki a sashen ranar 9 ga watan Agustan 2021 inda take koyar da Turancin Ingilishi.
Wata biyu bayan nan ne kuma aka yi sammacinta zuwa ofishin Shugaban jami'ar domin wata ganawa.
An shigar da ita wani ɗaki inda kwamitin da ya haɗa da Shugaban jami'ar Felix Raj da magatakarda Ashish Mitra da wasu mata biyar suka yi mata tambayoyi.
An sanar da ita cewa mahaifin wani ɗalibi ya yi ƙorafi a kan ta.
"Shugaban Jami'ar ya ce mahaifin ya tsinci yaronsa yana kallon hotunana a Instagram inda nake sanye da ɗan kamfai.
Ya ce hotunan sun nuna tsiraici inda ya buƙaci hukumar makarantar ta shiga lamarin."
An rarraba wata takarda ga mambobin hukumar gudanarwar haɗe da hotuna biyar zuwa shida sannan aka nemi ta tabbatar ko hotunanta ne.
'Na fahimci ana sa ka mun shakku game da kai na'
Hotunan da a ciki take sanye da ɗan kamfai, ta ɗauke sune da kanta a ɗakinta, a cewarta, inda ta bayyana cewa ta wallafa su a 'Instagram Story' abin da ke nufin hotunan za su ɓace bayan sa'a 24.
Amma kwamitin bai yi na'am da bayananta ba cewa ta saka hotunan ne a ranar 13 ga watan Yunin 2021 - kusan watanni biyu kafin ta fara aiki a jami'ar kuma kafin ta amince da buƙatar neman abota daga wasu ɗalibanta a shafin nata.

Asalin hoton, Getty Images
"Na kaɗu. Lokacin da na ga hotunan sai da zuciyata ta kaɗu, na ji wani iri cewa hotunana ne ake yaɗawa ba tare da izinina ba," kamar yadda ta faɗa min.
"Na kasa ma kallon hotunan ko sau ɗaya, yadda aka nuna min su da kuma irin maganganun da ake yi, sun sa na zama kamar ba ni da daraja. Na fara jin kamar ana min bita da ƙulli."
'Shin iyayenki sun ga hotunan?'
"An tambaye ni ko me ma ya sa na yi haka? A matsayinki na mace ba kya ganin bai dace ba?
A matsayinki na Farfesa, ba kamta ya yi ki riƙa shiga mai kyau ba? Ba ki san mata suna da nau'in shigar da ya kamata su yi ba?
Firaminista Modi ya yi kira ga Indiyawa su guji ƙyamar mata" Sun faɗa min ina kunyata jami'ar.
An tambayeni ko iyayena suna kan Instagram ko ma sun ga waɗannan hotunan? Na ji ba daɗi. "An buƙaci ta dawo washe gari tare da rahoto.
Yadda na nemi afuwa aka kuma tilasta min ajiye aiki
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Malamar ta koma ofishin Shugaban Jami'ar inda ta miƙa takardar neman afuwa, "da aka rubuta bisa shawara daga wasu mambobin sashen da suka haɗa da jami'in da ke kula da batutuwan da suka shafi jinsi," - ƴar ajinta a baya kuma mataimakiyar Farfesa a jami'ar wadda ita ma take cikin kwamitin da ya yi mata tambayoyi.
"Ina mai neman afuwa idan kun kalli hotunana a matsayin waɗanda suka ɓata mutuncin Jami'ar," kamar yadda ta rubuta.
Abin "ba daɗi" in ji ta amma ta yi tunanin maganar za ta mutu."
Amma shugaban jami'ar ya sanar da ni cewa hukumar gudanarwar ta ba da shawarar a kore ni.
Ya ce hotunanki sun karaɗe ko ina, galibin ɗalibai sun gansu kuma ba za su girmamaki ba sannan iyaye za su yi ƙorafi.
Ya ce abin da ya fi dacewa shi ne na ajiye aiki," Idantaƙi yin haka, a cewarsa, za ta je gidan gyaran hali saboda iyayen ɗalibin na son shigar da ƙara gaban ƴan sanda kuma za a kama ni."
"Na ji kamar an saka ni a kwana - kawai sai na ajiye aiki," in ji ta.
''Amma na yi matyuƙar jin haushi kuma na nemi shawarar masana shari'a. Saboda an sauke hotunana, an kuma yaɗa su ba tare da amincewa ta ba, lauya na ya bani shawarar na shigar da korafi kan cin zarafi gaban ƴan sandan da ke sauraron ƙararrakin da suka shafi laifukan intanet." kamar yadda ta faɗa.
'Ba mu nemi ta ajiye aiki ba'
Father Felix Raj yaƙi cewa komai kan ko kwamitin ya ba da shawarar a kore ta amma ya musanta duk zarge-zargen da aka yi masa da kuma jami'ar.
"Makaranta ce ta koyar da ilimi. A matsayin shugaban jami'ar, na fada mata bai kamata ta wallafa hotunan ba.
"Ya ce bai yi mata dole kan sai ta ajiye aiki ba, kawai ta ajiye aikin bisa raɗin kanta".
"Ta miƙa takardar neman afuwa ranar 8 ga watan Oktoban 2021. Mun amince da ita.
Na ɗauka mataki ne mai kyau. Amma sai ta ba da takardar ajiye aiki ranar 25 ga watan Oktoba - ranar da muka sake dawowa bayan hutun bikin Puja.
"Na yi tsammanin za ta dawo aiki bayan hutun. Ban san abin da ya wakana a tsukin makonni biyun ba ," a cewarsa, inda ya ce ko kaɗan ba su da wata matsala da ita" kuma "muna ba ta kulawa sosai".
Da aka tambaye shi kan bayanin da ta yi cewa ba lalle a ga hotunan a shafinta na Instagram ba bayan ta fara aiki a jami'ar da kuma zargin cewa ana yi mata bita da ƙulli, Father Felix Raj ya ce "shi ba ƙwararre bane a fasaha".
Matakin jami'ar ya janyo cece-kuce...
Matakin da aka ɗauka kan malamar dai ya janyo suka daga ɗalibai da dama.
Wani tsohon ɗalibin jami'ar Gaurav Banerjee ya fara maudu'in change.org - ƙorafin da aka miƙa ga ministan ilimi na jihar West Bengal, ya samu goyon bayan mutum 25,000.
Mr Banerjee ya shaida wa BBC cewa yana son jami'ar ta nemi afuwar Farfesa kuma yana neman gwamnati ta ladabtar da kwmaitin saboda yadda ya tafiyar da lamarin.
"Na ji daɗin yadda mutane suka kadu da abin da jami'ar ta yi, a cewarsa.

Asalin hoton, Getty Images
A baya-bayan nan, ɗalibai da dama na jam'iar, sanye cikin baƙaƙen kaya, sun gudanar da zanga-zangar ba-zata a gaban jami'ar domin nuna goyon bayansu ga malamar.
"Mun samu labarin abin da aka yi wa ɗaya daga cikin malamanmu," in ji daya daga cikin ɗaliban.
"Wannan sam ba za mu amince da shi ba Me ya sa wani zai damu da abin da nake yi da rayuwata? Abin da ya fi firgita ni shi ne yadda mambobin kwamitin ciki har da mata biyar ba su yi tunanin wannan a matsayin tabbatar da doka ba, ya ƙara da cewa
'Ba lalle na yi nasara ba...'
Malamar ta ce ta yi mamakin irin goyon bayan da ta samu kuma ta nuna godiya ga waɗanda suka tsaya mata.
Bayan watanni da ta shafe cikin ƙunci, na sake samun kaina ganin yadda mutane suke kallon matakin a matsayin abin dariya.
"Ta ce kundin tsarin mulkin Indiya ya bamu ikon bayyana ra'ayoyinmu kuma wannan "sa idon" ya tsallaka har zuwa wuraren aiki.
"Ta ya ya rayuwata kafin na fara aiki da jami'a ya saɓawa ƙa'idojinsu na amfani da shafukan sada zumunta? ta tambaya.
"Har yanzu ina jin ban yi ba dai-dai ba. Ba lalle na yi nasara ba amma a wajena yaƙi ne mai muhimmanci," in ji ta.











