Yadda ake cinikin hotunan tsiraicin mata a asirce

.

Mata na fuskantar barazana daga gungun mutane bayan an wallafa wasu bayanansu da hotunan tsiraicinsu da bidiyo a shafin sada zumunta na Reddit.

BBC ta bankaɗo mutumin da ke jan ragamar ɗaya daga cikin ƙungiyoyin, sakamakon hasken abin kunna sigari.

"Ku biya £5 idan kuna son tsiraicinta." "Ina da wasu bidiyonta da za su yi kasuwa." "Me za mu yi mata? "Na kaɗu sosai a lokacin da nake duba hotunan da irin martanin da ake yi a kai,” in ji wani mai tallan irin wadannan hotuna.

Akwai dubban hotuna. Hotunan mata tsirara ko sanye da kaya marasa kamala.

Ƙarƙashin hotunan, maza ne ke bayyana ra'ayoyinsu kan matan har da yi musu barazanar fyade.

Ba za a iya wallafa akasarin abin da na gani ba. Wani haske da ƙawata ta ba ni ne ya kai ni ga ganin waɗannan bidiyoyin.

Ɗaya daga cikin hotunan an kwafo shi ne daga Instagram aka kuma wallafa a Reddit.

Ba wai hoton tsiraici ba ne amma sai da aka faɗi abin da bai dace ba kan hoton.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ta damu da halin da take ciki da sauran mata. Abin da na gani ya yi kama da kasuwa.

Ɗaruruwan shafuka aka mayar da su na watsawa da cinikin hotunan mata - kuma ga dukkan alamu ana haka ne ba tare da izinin masu hotunan ba.

Ya yi kama da wani sabon salo da samari da ƴan mata da suka ɓata ke amfani da shi na wallafa hotunan tsiraici ba tare da izini ba.

An yaɗa hotunan ga dubban mutane, amma maza da ke ɓoye kansu na haɗuwa domin fallasa waɗannan matan.

Ana musanyen adireshi da lambar waya da shafukan sada zumunta ta intanet - sai a riƙa yi wa matan barazana.

Sai na ji kamar na shiga wani surƙuƙin duhu a shafin intanet amma duka wannan na faruwa ne a babban shafin sada zumunta na Reddit.

Reddit yana da kusan mutum miliyan 50 da ke amfani da shafin - kusan miliyan huɗu suna Burtaniya - inda mutane suke buɗe dandali da ake kira "subreddits", wanda a ciki ake tattaunawa kan batutuwa da dama.

Ba a cutarwa a akasarin waɗannan dandali amma Reddit na da tarihin zama dandalin tattauna batutuwa masu cike da taƙaddama.

A 2014, an yaɗa jerin hotunan tsiraici na wasu fitattu a shafin Reddit kuma shekara huɗu bayan nan ne kuma shafin ya rufe wata ƙungiya da ke wallafa bidiyon ƙarya.

Kamfanin na Amurka Reddit ya ɗauki wasu tsauraran matakai inda ya ƙarfafa matakinsa na haramta wallafawa ko tilastawa wani wallafa wasu hotunan tsiraici ba tare da izinin masu su ba.

Ina son na fahimci abin da ya sa har yanzu ake yaɗa hotunan tsiraici na mata a Reddit da kuma yadda hakan ya shafi matan.

Sannan ina son na gano wanda ke da hannu a kai.

Ina ganin haramcin da Reddit ya ƙaƙaba ba ya tasiri. Mun gano wasu dandali da a cikinsu ake yada hotunan tsiraici na mata daga sassan Burtaniya.

Dandalin farko da idona ya gani na wasu ƴan Kudancin Asiya ne kuma akwai mabiya fiye da 20,000, akasarinsu maza ne daga yanki ɗaya, inda suke bayyana ra'ayoyinsu a Turancin Ingilishi da Hindi da Urdu da Punjabi.

Na gane wasu daga cikin matan saboda suna da mabiya da dama. Wasu ma na musu farin sani.

Akwai sama da hotuna 15,000. Mun kalli dubbai kuma mun samu hotunan tsiraici na mata 150.

Dukkansu sun sha suka daga masu bayyana ra'ayinsu kan hotunan. Na san tabbas babu wata mace da za ta amince a wallafa hotonta a dandalin.

Wasu, kamar wanda ƙawata ta gano hotonta a ciki, hotuna ne da aka samo su daga shafukan matan kuma ba cikin tsirara ba. Amma duk da haka sai da aka caccake su tare da yi musu barazana wani lokacin ma har da neman yi wa mai hoton kutse a waya ko a kwamfuta.

Wata da muka tuntuɓa ta ce a yanzu tana samun saƙonni marasa daɗi a kowace rana bayan da aka wallafa hotonta da aka samo daga Instagram tare da wasu ra'ayoyi na barazanar yi mata fyaɗe.

Mazan da ke dandalin na Subreddit suma suna yaɗawa da cinikin hotunan tsiraicin mata. Waɗannan hotunan sun yi kama da na ɗauki da kanka da ake turawa abokan soyayya ba wai an tura su domin ganin jama'a ba.

Akwai kuma bidiyon da suka fi muni da a ciki ke nuna alamun matan an naɗe su cikin sirri suna tarayya.

'Zan nemo ki'

Wani ƙunshin saƙonni ya nuna hotunan wata mata babu kaya. "Shin akwai mai bidiyon wannan? in ji wani mai amfani da shafin, yana mai amfani da munanan kalmomi a kanta. "Ina da ƙunshin hotunanta a kan £5, a ɗauke ni hoto, in ji wani.

"Ya sunan shafinta, in ji wani mai amfani da shafin. Ayesha - ba sunanta na asali ba - ta gano wasu bidyoyinta da aka sa a dandalin subreddit a shekarar da ta gabata.

Tana tunanin tsohon saurayinta ne ya naɗi bidiyonta cikin sirri. Ta kuma fuskanci cin zarafi da barazana a kafafen sada zumunta ba ma kawai zafin cin amanar da tsohon saurayin nata ya yi mata ba.

"Idan har baki sadu da ni ba, zan tura wa iyayenki bidiyonki. Zan nemo ki... Idan ba ki amince da buƙatata ba , zan yi miki fyaɗe."Masu cin zarafinta sun yi ƙoƙarin yi mata barazana kan wasu hotunan.

''Kasancewa mace 'yar Pakistan, ba daidai ba ne a tsakanin al'ummarsu wata ta sadu da namiji kafin aure ko kuma wani abu makamacin hakan - abin alla-wadai ne,'' a cewarta.

Ayesha ta daina shiga jama'a da fita daga gida, akwai lokacin ma da ta yi yunƙurin kashe kanta.

Bayan ƙokarin hallaka kanta, sai ta yanke shawarar shaidawa iyayenta abin da ya same ta. Mahaifiyarta da mahaifinta duk sun shiga matsananciyar damuwa, a cewarta.

''Na yi matukar jin kunyar kaina saboda abin da ya faru da kuma jefa su a cikin wannan yanayi,'' a cewar Ayesha.

Ayesha ta tuntuɓi Reddit sau shurin masaƙi. A wani lokaci ta yi sa'a har aka goge wani bidiyonta nan take amma ta shafe wata hudu tana tuntuba kafin a cire wani bidiyon na daban. Kuma ba a nan kadai abin ya tsaya ba.

Bidiyon da aka goge an riga an yaɗa shi a shafukan sada zumunta, wasu kuma suka sake dauko shi su ka dawo da shi inda aka soma wallafa shi bayan wata guda, a subreddit.

Subreddit da ya jefa Ayesha cikin kunya da tsangwama an samu wani mai suna Zippomad da ke kula da irin wadannan harkoki - wannan suna na iya taimakawa wajen gano shi.