Ba'indiye da bashi ya yi wa katutu ya tono dutsen diamond na miliyoyin kuɗi

Raju Gound
Bayanan hoto, Raju Gound ya shafe shekara 10 yana neman ma'adanin demon
    • Marubuci, Cherylann Mollan
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Mumbai
  • Lokacin karatu: Minti 4

Kakar wani lebura Ba'indiye ta yanke saƙa dare ɗaya bayan ya yi katarin haƙo shirgegen ma'adanin demon (ko kuma lu'ulu'u) a jihar Madhya Pradesh da ke tsakiyar ƙasar.

Ya ce bashin da ake bin sa na dubban rupee zai fara biya tukunna kafin ya yi komai da kuɗin.

Ana sa ran dutsen demon ɗin mai girman 19.22-carat zai kai darajar kuɗin rupee na Indiya miliyan takwas (kwatankwacin sama da naira biliyan 12) yayin gwanjonsa da za a yi bisa sa idon gwamnati.

Raju Gound ya ce ya shafe shekara 10 yana tona ramuka da zimmar neman demon ɗin a yankin Panna.

Panna ya shahara da albarkatun ma'adanin demon, inda mutane kan karɓi hayar wuri daga gwamnati don haƙa ƙananan ramuka don neman ma'adanai masu daraja.

Diamond
Bayanan hoto, Ana sa ran dutsen demon ɗin da Gound ya samu zai kawo masa kuɗi miliyan takwas na kuɗin Indiya rupee

Hukumar kula da cigaban haƙar ma'adanai ta Indiya National Mineral Development Corporation (NMDC), ita ce ke kula da aikin haƙo duwatsun masu daraja a yankin Panna.

Kuma ita ce ke bai wa ɗaiɗaikun mutane da iyalai da kamfanoni hayar ramukan haƙar ma'adanai, waɗanda ke haƙar ma'adanan da ƙananan kayan aiki.

Duk abin da suka samu gwamnati za su bai wa, ita kuma ta tantance dutsen.

Gound ya faɗa wa BBC cewa mahaifinsa ne ya karɓi hayar mahaƙar a ƙauyen Krishna Kalyanpur Patti da ke kusa da Panna wata biyu da suka wuce.

Ya ce danginsa kan karɓi hayar mahaƙa a farkon damina lokacin da ba a noma kuma babu ayyukan yi a gonaki.

"Mu talakawa ne sosai kuma ba mu da wata hanyar samun kuɗi. Saboda haka muke yin haƙar ma'adanan da fatan samun ƴan kuɗi," in ji shi.

Gound kan yi amfani da ƙananan kayan aiki wajen haƙar dutsen demon
Bayanan hoto, Gound kan yi amfani da ƙananan kayan aiki wajen haƙar dutsen demon

Ya sha jin labarin mutanen da ke sa'ar samun demon kuma ya dinga fatan shi ma wata rana zai samu.

A safiyar Laraba, ya je wurin domin fara aikin da ya saba na haƙar ma'adanan da hannu.

"Abu ne mai wahala. Za mu haƙa rami, mu fito da dunƙulen ƙasa da duwatsu masu girma, mu tace su da rariya, sai kuma mu dinga zare ƙananan duwatsu a hankali don neman demon ɗin," kamar yadda ya bayyana.

Da tsakar wannan ranar, duk wahalar da suke sha ta biya kuma ya samu sa'a.

"Ina tsaka da laluba duwatsun sai na ga wani abu da ya yi kama da gilashi. Na ɗaga shi sama sai na ga yana walƙiya. A lokacin ne na san cewa na samu demon," a cewarsa.

Akan auna dutsen mai daraja ne a ɗakin gwaji na gwamnati
Bayanan hoto, Akan auna dutsen mai daraja ne a ɗakin gwaji na gwamnati
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai Gound ya ɗauki dutsen zuwa ofishin kula da demon ɗin na gwamnati, inda aka tantance kuma aka auna nauyinsa.

Anupam Singh, jami'in ofishin demon ɗin, ya ce zai sayar da shi a kasuwar gwanjo mai zuwa, kuma Gound za a bai wa Gound kasonsa bayan cire haraji da kuma ladan gwamnati daga cikin kuɗin.

"Akan bayar da hayar waɗannan ramuka ne kan rupee 200 zuwa 250 [na ɗan wani lokaci,", kamar yadda Mista Singh ya shaida wa BBC.

A 2018, wani lebura daga yankin Bundelkhand ya samu dutsen demon da ya kai darajar rupee miliyan 15 a wata mahaƙa a Panna. Sai dai kuma ba a fiye samun duwatsun akai-akai ba.

Mista Singh ya ce yayin da mutane kan samu ƙananan demon, wanda Gound ya samu ya sha bamban saboda girmansa.

Yanzu dai Gound na fatan gina wa iyalansa sabon gida da kuɗin, kuma ya biya kuɗin makarantar ƴaƴansa.

Amma da farko yana son ya biya bashin rupee 500,000 da ake bin sa.

Ya ce ba shi fargaba idan mutane sun san irin arzikin da ya samu, amma yana da niyyar raba kuɗin tsakanin ƴan'uwansa 19 da ke zaune tare da shi.

Amma dai a yanzu hankalinsa a kwance yake tun da shi za a bai wa kuɗin tukunna.

"Gobe ma zan koma mahaƙar ko zan samo wani," a cewarsa.