Mu ne Zama Zama: Yadda ake fadawa hadari yayin haƙar ma'adanai ba bisa ka'ida ba a Afrika ta Kudu
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon
Suna zuwa aiki a kullum, ba su da tabbacin ko za su koma gida a raye.
Talauci ya tilasta musu shiga cikin karkashin kasa don neman zinare.
Akan kama wasu da laifin haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba. Wasunsu kuma na mutuwa.
Shirin BBC Afrika Eye ya bankaɗo yadda 'yan ci-rani ke jefa rayuwarsu cikin haɗari ta hanyar shiga ƙarƙashin ƙasa a wani wajen haƙar zinare da aka yi watsi da shi a Afrika ta Kudu domin su samu abin rayuwa.