Abin da ya kamata ku sani kan wasan Najeriya da Gabon na neman gurbi

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 8

Za a buga wasan neman gurbin shiga gasar kofin duniya ranar Alhamis tsakanin Najeriya da Gabon da na Kamaru da Jamhuriyar Congo a zagayen daf da karshe.

A tsakanin tawaga huɗun da ke neman samun gurbin shiga gasar ta FIFA, sun taɓa halarta sau 15 a baya, sai dai ɗaya kacal daga cikinsu ce ake sa ran za ta je wasannin da za a buga a Amurka da Canada da kuma Mexico a 2026.

Kamaru ce kan gaba a yawan halartar gasar cin kofin duniya daga Afirka, wadda ta halarta sau takwas.

Najeriya ta halarci gasar kofin duniya sau shida, inda ta ƙarshe da ta buga ita ce a Rasha a 2018.

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo ta shiga gasar kofin duniya a 1974 lokacin da ake kiran ƙasar Zaire, yayin da Gabon ba ta taɓa samun gurbin gasar ba a baya.

Duk da haka, dukkan tawagar huɗu kowacce tana da damar kai wa wasannin cin babban kofin duniya da za a buga a baɗi.

Najeriya za ta kara da Gabon a Rabat ranar Alhamis a zagayen daf da karshe, daga nan Kamaru ta fafata da Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo duk a ranar.

Dukkan waɗanda suka ci wasansu ranar Alahmis, za su haɗu ranar Lahadi, domin tantance, wadda za ta ci gaba da buga wasan neman cike gurbin shiga gasar kofin duniya da wasu daga nahiyoyin.

Kenan wadda ta yi nasara daga Afirka za a haɗa ta da Bolivia (CONMEBOL) da New Caledonia (OFC) tare da wata daga Asiya da Concacaf a wasannin cike gurbi tsakanin tawaga shida da za su kara daga ranar 23 zuwa 31 Maris 2026.

Daga nan za a samu biyun da za su cike gurbin tawaga 48 da za su fafata a birane 16 tsakanin Amurka da Canada da kuma Mexico da za a fara daga 11 ga watan Yuli zuwa 19 ga watan Yuli.

Africa

Asalin hoton, Getty Images

Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Najeriya da Gabon za su gwabza ranar Alhamis a wasan kusa da karshe a neman gurbi shiga Gasar Cin Kofin Duniya ta 2026.

Za kuma su kece raini a filin wasa na Complexe Sportif Prince Héritier Moulay Al Hassan da ke birnin Rabat, babban birnin Morocco.

Wannan gagarumin wasa ne da zai bai wa kowacce tawaga damar neman gurbin shiga gasar duniya, bayan rashin samun tikitin kai tsaye a fafatawar cikin rukuni da suka yi wata 23 a ana gwabzawa daga nahiyar Afirka,

Kocin Najeriya, Eric Chelle da takwaransa na Gabon, Thierry Mouyouma za suyi amfani da fitattun ƴan ƙwallon da ke kasa a fatan kaiwa zagayen karshe.

Duk wadda ta yi nasara tsakanin Super Eagles da Gabon za ta fuskanci wadda za ta kai zagayen karshe tsakanin Kamaru da Jamhuriyar Congo da za a yi ranar Lahadi a dai Morocco.

Najeriya, wadda ta je gasar cin kofin duniya sau shida, tana son guje wa sake rashin halarta karo na biyu a jere, abin da ba ta taɓa yi ba, kuma ba zai bai wa fitattun ƴan ƙwallonta halaratar babbar gasar tamaula ta duniya ba, kuma koma baya ne sosai ga fanninsu na sana'ar taka leda.

Ana kuma sa ran kociyan Najeriya, Chelle da Mouyouma za su yi salon 4-3-3, domin bai ƴan wasa damar watayawa da nuna ƙwarewarsu tare da sa ƙwazo.

Chelle, wanda bai yi rashin nasara ba a wasa hudu, bayan cin karawa uku da canjaras ɗaya, watakila ya ci gaba da amfani da mai tsaron raga, Stanley Nwabali,

Olaoluwa Aina na jinya yayin da aka dakatar da Semi Ajay, kenan zai maye gurbinsu da Benjamin Fredericks da kuma ƙyaftin William Ekong.

Calvin Bassey da Zaidu Sanusi za su tsare baya baya. A tsakiyar fili kuwa akwai yiwuwar Wilfred Ndidi da Alex Iwobi da Frank Onyeka su buga gurbin.

A gurbin masu cin ƙwallaye ana sa ran a fara da Victor Osimhen, wanda ya ci kwallo shida a wasannin neman shiga gasar kofin duniya, wanda ya ci Rwanda da Zimbabwe da kuma Jamhuriyar Benin tare da Samuel Chukwueze da kuma Ademola Lookman.

Victor Osimhen

Asalin hoton, Getty Images

Osimhen, wanda ya ci kwallo 29 a wasa 44 a Najeriya, ya na da jimillar 160 a raga da bayar da 36 aka zura a raga a wasa 275, tsakanin tawaga da ƙungiyoyi, wanda yake da hatsari da rikita duk wasu masu tsaron bayan da yake fuskanta.

Gabon ta fito a matsayin mafi kyawun na biyu daga rukuni tara na Afirka, kuma tana fatan samun nasara ta hannun tsohon dan gaba mai shekara 36, Pierre-Emerick Aubameyang, wanda ya taba bugawa Arsenal (Ingila) da Borussia Dortmund (Jamus), yanzu kuma yana buga wasa a Olympique Marseille ta Faransa.

Mahaifinsa, Pierre-François Aubameyang, ya wakilci Gabon a gasar cin kofin Afirka ta 1994 a Tunisia, inda Gabon ta yi rashin nasara da ci 0-3 a hannun Najeriya a wasanta na farko, kuma Super Eagles suka ci gaba da lashe kofin a wancan lokaci.

Mouyouma zai iya ci gaba da amfani da tsarin da ya saba, inda Loyce Mbaba zai tsare raga, tare da Jacques Ekomie, Bruno Manga, Mick Omfia, da Anthony Oyono a baya, sannan Guélor Kanga, Mario Lemina, da Didier Ndong su rike tsakiyar fili.

A gaba kuwa, Aubameyang wanda ya ci kwallaye hudu a nasarar da suka yi kan Gambia, zai yi aiki tare da Denis Bouanga da Noah Lemina.

Gabon

Asalin hoton, Getty Images

Mouyouma ya bayyana cewa 'yan wasansa za su buga salon wasan sauri da kai ƙwallo cikin da'irar Najeriya da bani in baka kusa da kusa tsakanin ƴan wasa da nufin gajiyar da ƴan ƙwallon Super Eagles, shi kuwa kociyan Najeriya bai fayyace salon da zai yi ba.

Najeriya ta samu nasara a wasa biyar daga cikin haduwar su tara da Gabon tun sama da shekaru 60 da ta wuce.

Sun yi wasa biyu a Libreville, inda Najeriya ta yi nasara ɗaya da canjaras ɗaya. Nasara daya tilo da Gabon ta taba samu ita ce a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya ranar 25 ga watan Yuni 1989, inda ta doke Najeriya 2-1 — hakan ya hana Super Eagles zuwa gasar kofin duniya da aka yi ta Italia '90, sakamakon da Najeriya ta kasa yin canjaras da ake bukata a wasan karshe da Kamaru a Yaounde.

An tashi canjaras a wasa uku daga cikin haduwar su tara, ciki har da na neman gurbin shiga gasar kofin duniya ta Jamus 2006.

Amma wannan fafatawar ta Alhamis babu batun canjaras, domin dole sai an samu tawaga daya tilo da za ta tsallaka zuwa karawar karshe da za a yi ranar Lahadi.

Ƴan wasan da ke sansanin Super Eagles

Super Eagles

Asalin hoton, The NFF

Wasannin da aka yi a tsakanin Najeriya da Gabon

  • Sada zumunta ranar 28 ga watan Agusta 1965: Gabon 2-2 Najeriya
  • Sada zumunta ranar 29 ga watan Agusta 1965: Gabon 1-4 Najeriya
  • Sada zumunta ranar 2 ga watan Maris 1983: Gabon 0-0 Najeriya
  • Neman shiga kofin duniya ranar 7 ga watan Janairu 1989: Najeriya 1-0 Gabon
  • Shiga kofin duniya ranar 25 ga watan Yunin 1989: Gabon 2-1 Najeriya
  • Kofin nahiyar Afirka ranar 26 ga watan Maris 1994: Najeriya 3-0 Gabon
  • Sada zumunta ranar 21 ga watan Nuwambar 1999: Gabon 0-2 Najeriya
  • Neman shiga kofin duniya ranar 9 ga watan Oktoba 2004: Gabon 1-1 Najeriya
  • Neman shiga kofin duniya ranar 26 ga watan Maris 2005: Najeriya 2-0 Gabon

Wasu ƴan ƙwallon Kamaru da ke jinya

Kamaru

Asalin hoton, Getty Images

Kamaru na fama da wasu ƴan wasan da ke jinya, bayan da take fatan zuwa wasannin cike gurbin shiga gasar cin kofin duniya da za ta kece raini da Jamhuriyar Congo.

Tuni aka sanar cewar Eric Maxim Choupo-Motingda Andre-Frank Zambo Anguissa ba za su buga wasan da za a yi a birnin Rabat ba ranar Alhamis.

Haka kuma hukumar ƙwallon kafa ta Kamaru ta sanar da cewar da kyar ne idan Andre Onana zai yi karawar, amma ana ci gaba da auna koshin lafiyarsa.

Choupo-Moting ya ji rauni a gwiwa, yayin da Zambo Anguissya hakura da yin atisaye ranar Talata, sakamakon raunin nan na tsagewar tsokar cinya.

Ɗan wasan wanda ya cika shekara 30 ranar Lahadi, ya ci wa Napoli ƙwallo huɗu a Serie A a kakar nan.

Tawagar Kamaru ta halarci gasar kofin duniya karo takwas jimilla, ita ce kan gaba a yawan halartar wasannin daga Afirka.

Kamaru ta je Morocco da ƴan wasa 28

Tawagar Kamaru ta je Morocco da ƴan wasa 28 a karawar neman shiga gasar kofin duniya da za a yi a baɗi

Duk da cewa Kamaru ta kare a mataki na biyu a rukuni na huɗu, bayan da aka samu tawaga taran da suka samu gurbi kai tsaye, itama tana da damar kai wa wasannin da za a yi a Amurka da Canada da kuma Mexico.

Kocin Kamaru, Marc Brys ya gayyaci, Yvan Neyou da Jean Onda kuma Wilitty Younoussa da Enzo Boyomo da kuma Darlin Yongwa, sai dai ya ajiye Brice Ambina da Samuel Kotto da kuma Junior Tchamadeu.

Wannan tawagar da kociyan Kamaru ya haɗa na shirin halartar gasar cin kofin nahiyar Afirka da su da za a yi a Morocco daga cikin Disamba zuwa Janairun 2026.

A gasar ta kofin Afirka, Kamru tana rukuni da ya haɗa da Gabon da Mozambique da mai rike da kofin Côte d'Ivoire.

Ƴan wasan tawagar Kamaru:

Masu tsare raga: Devis Epassy (Dinamo Bucharest, Romania), Simon Omossola (St Eloi Lupopo, DR Congo), André Onana (Trabzonspor, Turkey)

Masu tsare baya: Malcolm Bokele (Goztepe, Turkey), Enzo Boyomo (Osasuna, Spain), Jean-Charles Castelletto (Al Duhail, Qatar), Mahamadou Nagida (Stade Rennais, France), Michael Ngadeu-Ngadjui (Beijing Guoan, China), Jackson Tchatchoua (Wolverhampton Wanderers, England), Nouhou Tolo (Seattle Sounders, USA), Darlin Yongwa (Lorient, France)

Masu buga tsakiya: Arthur Avom (Lorient, France), Carlos Baleba (Brighton & Hove Albion, England), Martin Hongla (Granada, Spain), Daniel Namaso (AJ Auxerre, France), Yvan Neyou (Getafe, Cameroon), Jean Onana (Genoa, Italy), Wilitty Younoussa (Rodez, France), Franck Zambo Anguissa (Napoli, Italy)

Masu cin ƙwallaye: Vincent Aboubakar (Neftchi Baku, Azerbaijan), Christian Bassogog (Al Okhdood, Saudi Arabia), Eric Maxim Choupo Moting (New York RB, USA), Karl Etta Eyong (Levante, Spain), Frank Magri (Toulouse, France), Bryan Mbeumo (Manchester United, England), Georges-Kévin Nkoudou (Al Diriyah, Saudi Arabia), Patrick Soko (Almeria, Spain).