Ɗan wasan da ya fi muhimmanci a kowace ƙungiya a Gasar Premier

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Flora Snelson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
- Lokacin karatu: Minti 6
"Ba za mu samu wanda zai maye gurbinsa ba," kamar yadda Pep Guardiola ya faɗa kwana ɗaya gabanin Sergio Aguero ya buga wasansa na ƙarshe a ƙungiyar Manchester City.
Bayan shekara huɗu, ko za a iya cewa City ta samu wani dodon raga mai ƙwazo da karsashi da ƙoshin lafiya?
"Idan babu shi, gaskiya za mu sha wahala," kamar yadda Guardiola ya fada bayan Haaland ya zura ƙwallo biyu da suka taimaka wa City ta doke Bournemouth 3-1 ranar Lahadi.
Ba kowace ƙungiya ce za ta iya bugun gaba ta ce tana da dodon raga kamar Haaland ba, sai dai kowace ƙungiya na da ɗan wasa ɗaya wanda ba za ta taɓa so a zo wasa babu shi ba - ko dai saboda iya jagorancinsa ko iya tsarawa ko kuma sauya yadda wasa ke gudana.
Daga ƴanwasa waɗanda suke kasancewa "ruhin ƙungiyoyinsu" zuwa "zaƙaƙurai marasa gajiya", ga jerin ƴanwasa 20 masu matuƙar muhimmanci ga ƙungiyoyinsu a gasar Premier ta Ingila - waɗanda masoya ƙwallon ƙafa suka zaɓa.
Arsenal - Declan Rice
Arsenal ta fara kakar wasar bana da ƙafar dama kuma tana ƙwazon da ke nuna alamun cewa za ta iya cimma burinta na lashe kofin Premier, wanda ta gaza sake lashewa tun daga kakar 2003-04.
Bayan wasanni 10, Gunners ta bayar da tazarar maki shida a saman tebur tsakaninta da Manchester City da ke a matsayi na biyu.
Laura Kirk-Francis ta shirin Podcast na Latte Firm ta zaɓi Declan Rice a matsayin ɗan wasa mafi muhimmanci a Arsenal.
"Akwai wani abu da Declan Rice ba zai iya yi ba?" Kamar yadda Kirk-Francis ta tambaya.
"A wannan kakar Rice ya nuna hazaƙa, ba kawai ta hanyar ɗauko ƙwallon da ake zurawa a raga ba, har ma da cin ƙwallo shi da kansa.
Ɗan wasan mai shekara 26 a duniya, wanda Arsenal ta saya daga West Ham ya taimaka wa ƙungiyarsa wajen yin wasa bakwai a jere ba tare da an zura mata ƙwallo a raga ba, inda ya bayar da gudumawa aka zura ƙwallo biyar a Premier daga farkon wannan kakar.
Aston Villa - Ollie Watkins
Aston Villa ta yi wasa biyar kafin ta samu nasara ta farko a wannan kaka, inda daga nan ta yi nasara sau hudu a jere, lamarin da ya fitar da su daga gurbin gajiyayyu zuwa tsakiyar teburi.
David Michael na shafin My Old Man Said blog na ganin cewa Watkins ne ɗan wasa mafi muhimmanci ga Villa, duk kuwa da cewa "ba ya taɓuka abin a zo a gani."
Bournemouth - Antoine Semenyo
Rawar gani da Bournemouth ke takawa daga farkon wannan kaka ta sanya ake ganin za ta iya kasancewa cikin ƙungiyoyi huɗu na saman teburi a ƙarshen kaka.
"A yanzu ɗan wasa mafi muhimmanci, babu haufi shi ne Antoine Semenyo," in ji Tom Jordan na shirin Podcast na Back of the Net.
Brentford - Mikkel Damsgaard
Bayan rasa mai horas da ƙungiyar Thomas Frank, wanda ya tafi Spurs, a yanzu Brentford na sake gano kanta a gasar Premier.
"Mikkel Damsgaard shi ne ke sanya karsashi a wasanu," in ji Ian Westbrook na Beesotted Podcast.
Ɗan wasan ya zura ƙwallo ɗaya kuma ya taimaka an zura ɗaya a gasar Premier.
Brighton & Hove Albion - Danny Welbeck

Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Brighton and Hove Albion na faɗi-tashi tun daga farkon kakar nan, sai dai bayan wasanni 10 ƙungiyar na ganin haske ba laifi, inda take ƙasan Liverpool da maki uku.
Danny Welbeck ya ci ƙallo 6 a wasa 10 na gasar Premier ta wannan kaka.
Chelsea - Moises Caicedo
Chelsea ta yi sauye-sauye a ɓangaren masu horaswa tun bayan da ta ci kofin Conference League da kuma Club World Cup a kakar farko da Enzo Maresca ya jagoranci ƙungiyar.
Bayan wasa 10 a Premier, Chelsea na a matsayi na bakwai kan teburi, inda take da maki iri ɗaya da Tottenham wadda ke a matsayi na shida.
Chelsea na rashin Cole Palmer sanadiyyar rauni, wanda ɗaya ne daga cikin manyan ƴanwasanta, amma Will Faulks na tashar Chelsea News na ganin cewa rashin Palmer ya sanya Moises Caicedo ya yunkuro.
"Cole Palmer shi ne ɗan wasa mafi muhimmanci a Chelsea, amma yanzu Moises Caicedo na biye masa daf da daf," in ji Faulks.
Ɗan wasan tsakiyar ɗan asalin ƙasar Ecuador ya ci ƙwallo uku sannan ya taimaka an ci ɗaya a wannan kakar.
Liverpool - Dominik Szoboszlai
Da farko Liverpool ta fara da karsashi a ƙoƙarin kare kambinta, inda ta lashe wasanninta biyar na farko kafin ta sha kashi sau huɗu a jere, lamarin da ya nutsar da ita ƙasa.
Zakarun na Premier a yanzu suna a matsayi na uku, maki bakwai ƙasan Arsenal.
Dominik Szoboszlai shi ne ɗan wasan Liverpool mafi muhimmanci, in ji Jordan Chamberlain.
"Shi ne zaƙaƙuri a cikin ƙungiyar da ke fama da matsaloli a wannan kaka," in ji Chamberlain.
Ɗan asalin ƙasar Hungary mai shekara 25 ya bayar da gudumawa wajen zura ƙwallo biyu a wannan kaka a gasar Premier.
Manchester City - Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images
Bayan fara wasa ba tare da nuna ƙwazo ba, yanzu Mancester City ce ta biyu da maki shida tsakaninta da Arsenal da ke saman teburi.
Ƙungiyar da ta lashe Premier sau 10 tana a wannan matsayi bayan wasa 10.
Fredde Pye na City Xtra "bayan zura ƙwallo fiye da duk sauran ƙwallayen da dukkanin ƴanwasan suka ci a dukkanin gasanni, akwai wani abu mafi muhimmanci da za a faɗa kuma a kan Erling Haaland bayan wannan?"
Babu wani ɗan wasa a gasar Premier da ya kai Haaland zura ƙwallo a wannan kakar, inda ya zura 13.
Manchester United - Casemiro

Asalin hoton, Getty Images
Da alama Manchester United na neman dawowa kan ganiya ƙarƙashin jagorancin Ruben Amorim bayan ƙungiyar ta ƙare a matsayi na 15 a kakarsa ta farko.
United na a matsayi na 8 da maki 17, maki biyu ƙasa da na Manchester City wadda ke a matsayi na biyu.
Alex Turk na Turk Talks FC ya ce ɗan wasan tsakiyar ɗan asalin Brazil shi ne ɗan wasa ɗaya da Manchester ba za ta so a ce babu shi ba.
"Bruno Fernandes ne aka fi jin ɗuriyarsa, Bryan Mbeumo kuma da Matheus Cunha tauraruwarsu na haskawa, to amma Casemiro shi ne ruhin ƙungiyar," in ji Turk.
Sauran ƴanwasan da aka zaɓa a matsayin masu matuƙar muhimmanci ga ƙungiyoyinsu su ne:
Burnley - Martin Dubravka
Crystal Palace - Daniel Munoz
Everton - Jack Grealish
Fulham - Ryan Sessegnon
Leeds - Noah Okafor
Newcastle - Sandro Tonali
Nottingham Forest - Neco Williams
Sunderland - Granit Xhaka
Tottenham Hotspur - Cristian Romero
West Ham - Jarrod Bowen
Wolves - Joao Gomes











