Super Eagles ta koma ta ukun teburi bayan Rwanda ta ci Afirka ta Kudu

Super Eagles

Asalin hoton, The Nff

Tawagar Rwanda ta yi nasarar doke ta Afirka ta Kudu 2-0 a wasa na biyu cikin rukuni na uku a neman shiga gasar cin kofin duniya da za a yi a 2026.

Minti 12 da fara wasa, sai Rwanda ta zura kwallo a raga ta hannun Innocent Nshuti, sannan Gilbert Mugisha ya kara na biyu a raga.

Ranar 15 ga watan Nuwamba, Rwanda da Zimbabwe sun tashi canjaras 0-0 a wasan farko cikin rukuni, yayin da Afirka ta Kudu ta doke Benin 2-1 a ranar Asabar 18 ga watan Nuwamba.

Daya wasan na rukuni na uku da aka buga ranar Talata, an tashi 0-0 tsakanin Lesotho da Benin.

Super Eagles ta buga 1-1 a wasa biyu da ta buga cikin rukuni na uku da ta yi da Lesotho da kuma Zimbabwe.

Da wannan sakamakon Rwanda tana matakin farko da maki hudu, sai Afirka ta Kudu da maki uku da kuma Najeriya mai maki biyu ta ukun tebur.

Sauran da ke da maki bi-biyu a rukuni na ukun sun hada da Lesotho da Zimbabwe, yayin da Benin ke da maki daya kwal.

Ranar Laraba 5 ga watan Yunin 2024, za a ci gaba da wasa na uku-uku a rukuni, inda ake sa ran tawaga tara za ta wakilci Afirka a gasar ta 2026.

Super Eagles ba ta je gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar ba cikin shekara ta 2022.