'Osimhen zai iya kai ƙololuwar nasara'

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Emmanuel Akindubuwa and Isaiah Akinremi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa, Lagos
Shahararren tsohon ɗan wasan Najeriya, Emmanuel Amunike ya ce Victor Osimhen na da sauran bajintar da zai nuna nan gaba bayan ɗan wasan na Super Eagles ya ƙare a matsayi na takwas a jerin sunayaen kyautar Ballon d'Or ta maza a 2023.
Ɗan wasan mai shekaru 24 ya kasance babban ɗan wasan Afirka kuma ya zama ɗan Najeriya da ya fi ƙoƙari wajen neman kyautar a duniya tun bayan samar da ita a shekarar 1956, bayan rawar-gani da ya taka a kakar wasa ta 2022-23 tare a da Napoli, inda ya ci ƙwallaye 26 a gasar Serie A, lamarin da ya kai ga ƙungiyar ta lashe gasar karo na farko cikin shekaru 33.
Osimhen ya kuma zama ɗan Afirka mafi yawan zura ƙwallaye a gasar Seria A, inda ya karya tarihin wanda ya taɓa lashe kyautar Ballon d'Or a shekarar 1995 George Weah, wanda yanzu ya zama shugaban ƙasar Laberiya.
Amunike, wanda ya horas da Osimhen a lokacin da yake horar da 'yan ƙasa da shekaru 17 na Najeriya, ya shaida wa BBC cewa "Babu shakku game da halinsa, ta fuskar neman cimma burinsa na yin nasara."
"A matsayina na mai horar da 'yan wasa a matakin matasa, wannan wani abu ne da ya sanya ni sha'awar shi. Wannan yana ɗaya daga cikin mafi kyawun halayen da ɗan wasa ke bukata ya kai ga matakin ƙoli."
Bayan lashe gasar Seria A da Napoli, Osimhen ya kuma ƙare a matsayin wanda ya fi zura ƙwallaye a gasar neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika (Afcon) na 2023 da ƙwallaye 10, alamu masu ƙarfi da ke nuna cewa Osimhen zai lashe kyautar gwarzon ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Afirka na 2023.
Tsohon ɗan wasan Wolfsburg da Lille din na cikin jerin 'yan wasa 30 da aka lissafa za su iya lashe kyautar tare da ɗan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah, da mai tsaron gidan Manchester United da Kamaru, Andre Onana da kuma ɗan wasan baya na gefen dama na Morocco Achraf Hakimi, wanda ke taka leda a ƙungiyar Faransa, Paris St-Germain.
Za a sanar da wanda ya yi nasara a watan Disamba a wani biki da za a yi a Marrakech na ƙasar Morocco, kuma Osimhen na iya kasancewa ɗan Najeriya na farko da ya lashe kyautar tun bayan tsohon ɗan wasan Arsenal, Nwankwo Kanu a shekarar 1999.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Muna fatan ya lashe kyautar Caf sakamakon abubuwan da ya yi wa kulob ɗinsa da kuma tawagar Najeriya," in ji Amunike, wanda shi kansa ya zama gwarzon ɗan ƙwallon Afrika a shekarar 1994.
"Duk da cewa ya rasa buga gasar cin kofin duniya (Qatar 2022), ya samu damar kafa kansa a matsayin wanda ya cancanta ya lashe kyautar."
Duk da ci gaba da samun nasara a kulob da kuma ƙasarsa, Amunike, wanda ya taka leda tare da kocin Manchester City, Pep Guardiola a Barcelona, ya tuna yadda matashin Osimhen ya kusan rasa samun gurbi a tawagar Najeriya a gasar cin kofin duniya na U17 a 2015.
Sai daga ƙarshe aka zaɓe shi don tafiya ƙasar Chile kuma ya kafa tarihi inda ya zura ƙwallaye 10 yayin da Golden Eaglets ta lashe gasar a karo na biyar.
Amunike, mai shekaru 52 a yanzu, ya ce "A gaskiya muna da 'yan wasan gaba da suka halarci atisayen tantancewar."
"Na sanya kowane ɗan wasa a rukuni kuma rukunin da yake ciki ba su yi ƙoƙari ba, na riga na yi watsi da Victor da 'yan wasan da ke rukuninsa amma masu taimaka mun sun ja hankalina game da shi.
"Na sake ba shi dama kuma ya nuna kansa har ya samu gurbi a tawagar."
Najeriya za ta iya lashe gasar Afcon 2023

Asalin hoton, Getty Images
Amunike, wanda yanzu ke zaune a birnin Santander na ƙasar Sifaniya, ya yi amannar cewa Osimhen da Super Eagles na da damar lashe gasar cin kofin ƙasashen Afrika ta 2023 da za a yi a Ivory Coast a shekara mai zuwa.
'Yan Yammacin Afrikan sun kasance zakarun Nahiyar har sau uku, inda nasarar da suka samu a baya-bayan nan ta kasance ƙarƙashin marigayi Stephen Keshi a shekarar 2013 a Afirka ta Kudu.
"An albarkace mu da 'yan wasa masu hazaka, amma ba za mu je gasar da tunanin za mu yi nasara kawai ba, sai dai za mu iya yin nasara saboda muna da 'yan wasa nagari," in ji Amunike.
"Nasarar Afcon ba game da 'yan wasa ba ne - akwai abubuwa da yawa da za a tsara a kuma aiwatar."
Sai dai Amunike, wanda ya zura ƙwallaye biyu a wasan ƙarshe da ƙasar Zambia wanda ya taimaka wa Najeriya lashe kofin gasar cin kofin nahiyar Afrika karo na biyu da aka yi a Tunisia a shekarar 1994, yana son kocin Super Eagles na yanzu Jose Peseiro ya magance raunin da ƙungiyar ke da su a halin yanzu.
Ya ƙara da cewa 'yan wasan gaba ya kamata su riƙa taimaka wa masu tsaron baya, musamman idan ba su da ƙwallo a hannunsu," in ji shi.
"Ya kamata kociyan ya duba ƙungiyarsa gaba daya tare da samar da mafita domin ganin sun fafata da sauran ƙungiyoyi."
Najeriya wadda ta kasance a rukunin A tare da mai masaukin baƙi Ivory Coast da Equatorial Guinea da kuma Guinea-Bissau, an fitar da ita ne a zagaye na biyu a gasar Afcon na baya-bayan nan da aka yi a Kamaru.











