Afcon 2024: Najeriya ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka

NFF

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta samu gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a buga a 2024 a Ivory Coast.

Super Eagles ta doke Saliyo 3-2 a wasa na biyar-biyar a cikin rukuni da suka kece raini ranar Lahadi a Liberiya.

Najeriya ta fara cin kwallo ta hannun Victor Osimhen a minti na 19 da fara wasa, sannan ya kara na biyu minti 13 tsakani.

Daf da za su je hutu Saliyo ta zare daya ta hannun Mustapha Bundu, bayan da suka koma zagaye na biyu ta farke na biyu ta hannun Augustus Kargbo.

Sai dai kuma daf da lokacin da alkalin wasa, Mahmood Ismail ke shirin busa tashi ne Super Eagles ta kara na uku ta hannun Kelechi Iheanacho.

Da wannan sakamakon Super Eagles ce ta daya a rukunin farko da maki 12, sai Guniea Bissau ta biyu mai maki 10, kenan su biyun sun samu zuwa Afcon 2024.

Saliyo ce ta uku a rukunin farko da maki biyar da kuma Sao Tome And Principe mai maki daya kwal ta hudu a rukunin.

Nageria ta hada maki 12 ne bayan da ta ci Saliyo da Sao Tome And Principe, amma Guinea Bissau ta doke ta.

Daga baya Super Eagles ta dauki fansa a kan Guinea Bissau da wanda ta ci Saliyo ranar Lahadi.

Ranar 4 ga watan Satumba za a buga wasan karshe na shida-shida a cikin rukuni, inda Super Eagles za ta karbi bakuncin Sao Tome And Principe.

A kuma ranar Saliyu za ta ziyarci Guinea Bissau.