Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu a wasan neman gurbin kofin duniya

...

Asalin hoton, Getty Images

Tawagar Super Eagles ta Najeriya za ta kara da Afirka ta Kudu da Benin da Rwanda da Zimbabwe da kuma Lesotho a wasan rukuni na uku na gasar cin kofin duniya da za a yi a shekara ta 2026.

A ranar Alhamis ne aka gudanar da bikin fitar da jadawalin wasannin a birnin Abidjan na ƙasar Ivory Coast.

Sau 14 dai kasashen Najeriya da Afirka ta Kudu suka fafata tsakanin su, inda Super Eagles ta yi nasara sau bakwai sannan suka yi canjaras biyu.

A karo na ƙarshe da Najeriya ta kara da Bafana Bafana a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya shi ne kafin gasar 2010.

Super Eagles ta samu nasara a wasanni biyu da suka fafata, amma Afirka ta Kudu ta samu gurbin shiga gasar la’akari da matsayin mai masaukin baki.

Senegal, zakarun Afirka, na rukunin na biyu ne tare da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango da Togo da Mauritania da Sudan da kuma Sudan ta Kudu.

Morroco - wadda ta kai wasan dab da ƙarshe a gasar Kofin Duniya da aka buga a Qatar - ta samu kanta a rukuni na biyar inda za ta kara da Zambia da Tanzaniada Congo Brazzaville da Jamhuriyar Nijar da kuma Eritrea.

Ghana tana rukuni na daya tare da Mali, da Madagascar da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, da Comoros da kuma Chadi.

Cikakken jaddawalin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Rukuni na A: Masar, Burkina Faso, Guinea-Bissau, Saliyo, Ethiopia, da kuma Djibouti

Rukuni na B: Senegal, Democratic Republic of Congo, Togo, Mauritania, Sudan da kuma Southern Sudan

Rukuni na C: Najeriya, Afirka ta Kudu, Benin Republic, Zimbabwe, Rwanda da kuma Lesotho

Rukuni na D: Kamaru, Cape Verde, Angola, Libya, Eswatini da kuma Mauritius

Rukuni na E: Morroco, Zambia, Tanzania, Congo Brazzaville, Nijar da Eritrea.

Rukuni na F: Ivory Coast, Gabon, Kenya, Gambia, Burundi, da kuma Seychelles

Rukuni na G: Algeria, Guinea, Uganda, Mozambique, Botswana, Somalia

Rukuni na H: Tunisia, Equatorial Guinea, Namibia, Malawi, Liberia, Sao Tome e Principe

Rukuni na I: Ghana, Mali, Madagascar, the Central African Republic, Comoros and Chad.

Za a fara buga wasannin daga ranar 3 ga watan Nuwamban 2023, zuwa ranar 18 ga watan Nuwamban 2025.

Kasashen Afirka na da gurbi tara, bayan da aka kara adadin kasashen da za su shiga gasar da za a buga a shekarar 2026 zuwa 48.

Za dai a buga gasar a kasashen Amurka da Mexico da kuma Canada daga ranar 11 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yulin 2026.

Kasar Argentina ce dai ke rike da kofin gasar da ta dauka a shekarar 2022 da aka buga a Qatar