Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kungiyar ASUU ta janye yajin aiki
Kungiyar malaman jami'a a Najeriya, ASUU ta sanar da janye yajin aikin da mambobinta suka shafe wata takwas suna yi.
Dokta Chris Piwuna, mataimakin shugaban kungiyar ta ASUU ya tabbatar wa BBC labarin, inda ya ce an janye yajin aikin ne da sanyin safiyar Juma'a, bayan da shugabannin kungiyar suka gana jiya da daddare a Abuja babban birnin kasar.
Kazalika a sanarwar da shugaban ASUU Farfesa Emmanuel Osodeke ya sanya wa hannu, ya ce sun janye yajin aikin ne duk da yake "ba a warware batutuwan da ake jayayya a kansu ba."
Tun da farko, kotun daukaka kara a Najeriya ta umarci kungiyar ta janye yajin aikin gabanin ta saurari daukaka karar da ta yi a gabanta.
Tun ranar 14 ga watan Fabrairun wannan shekarar malaman jami'o'in gwamnatin tarayyar Najeriya suka tsunduma cikin yajin aiki, suna neman gwamnatin ta biya musu wasu bukatu.
Buƙatun ASUU
An daɗe ana kai ruwa-rana tsakanin gwamnatin Najeriya da ASUU kan biyan buƙatun da ƙungiyar ke son a biya mata kafin komawa bakin aiki.
Bukatun sun ƙunshi samar da wadatattun kuɗi wanda za a yi ayyuka domin farfado da jami'oi.
Akwai buƙatar biyan alawus na malamai wanda ya taru har ya kai shekaru ba a biya su ba.
Akwai batun samar da wani kwamiti da zai rika ziyartar jami'o'in gwamnatin tarayyar domin ganin irin ayyukan da suke yi don gano nasarori da ma matsaloli da aka samuDa saɓani kan sabon tsarin biyan albashi na bai-daya da gwamnati ta ɓullo da shi na IPPIS.