'Yan wasan Real Madrid da suka je Amurka wasan sada zumunta

Asalin hoton, Real Madrid FC
Real Madrid za ta buga wasan sada zumunta uku a Amurka, domin shirin tunkarar kakar tamaula ta bana da za a fara cikin watan Agusta.
Real Madrid za ta yi wasannin a birnin Las Vegas da San Francisco da kuma Los Angeles.
Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta fafata da Barcelona a Las Vegas da Club America a San Francisco da kuma Juventus a Los Angeles.
Ga jerin 'yan wasan Real Madrid da suka sauka je Amurka:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da Luis Lopez da kuma Lucas Canizares.
Masu tsaron baya: Carvajal da Militao da Alaba da Vallejo da Nacho da Rudiger, da Mendy da Odriozola da kuma Tobías.
Masu wasa daga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Lucas V. da Tchouameni da Ceballos da kuma Camavinga.
Masu cin kwallo: Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Rodrygo da Mariano da kuma Latasa.
Jadawalin wasannin da Real Madrid za ta buga a Amurka:
Ranar 23 ga watan Yuli Real Madrid za ta fara karawa da Barcelona, wato karon battar El Clasico na farko a bana da za su kece raini a Allegiant Stadium in Las Vegas.
Ranar 26 ga watan Yuli Real Madrid da Club America a filin wasa na Orcale Park, San Francisco.
Ranar 30 ga watan Real Madrid da Juventus a filin wasa na Rose Bowl, Los Angeles











