Super Falcons ba ta yi atisaye ba ranar Laraba

'Yan wasan tawagar mata ta Najeriya sun ki zuwa filin a tisaye ranar Laraba, kwana guda gabannin wasa neman mataki na uku a gasar cin kofin Afrika ta mata da ke gudana a Morocco.
Jagororin Super Falcons a Morocco ba su bayyana dalilin da 'yan wasan suka ki zuwa atisayen ba da ya kamata su yi a Maula El Bachir da ke Casablanca.
Sai dai majiyoyi da dama suna cewa matsalar rashin biyan alawus ce ta hanasu zuwa atisayen to sai da BBC ba ta tabbatar da hakan ba.
A ranar Juma’a ake sa ran Super Falcons za ta buga wasanta na neman mataki na uku da ya kamata ta ti da Zambia.
A ranar Litinin ne Falcons ta buga wasan daf da karshe da mai masaukin baki Morocco, wadda ta yi nasara a kan Najeriya a bugun fenareti da ci 4-5, bayan da suka tahi 1-1.
Matsalar rashin biyan alawus dai ba bakon abu ba ne a wajen yan wasan Najeriya, kasar da ta fi kowa yawan lashe gasar kwallon kafa ta mata ta Afirka a tarihi







