Dybala ya koma Roma bayan da yarjejenirsa ya kare a Juventus

Asalin hoton, Getty Images
Roma ta dauki dan kwallon tawagar Argentina, Paulo Dybala, wanda yarjejeniyarsa ya kare a Juventus a karshen kakar da ta wuce.
Mai shekara 28 ya koma kungiyar da Jose Mourinho ke jan ragama kan kwantiragin kaka uku, bayan barin Juventus a karshen watan Yuni.
Dybala ya ci kwallo 115 a wasa 293 a kungiyar birnin Turin, wadda ya koma da taka leda daga Palermo a 2015 ya kuma dauki Serie A biyar.
Dan wasa Dybala ya zura kwallo uku a raga a karawa 34 da ya yi wa Argentina.
Babban jami'in Inter Milan ya fada cewar suna kan tattaunawa kan daukar dan kwallon sai suka ji Roma ta rigasu.
An kuma yi ta alakanta dan wasan da cewar zai koma Manchester United da taka leda ko kuma Tottenham a 2019, inda Juventus ba ta amince ta sayar da shi ba.
Roma ta kammala kakar Serie A da ta wuce a mataki na shida karkashin jagorancin Mourinho, wanda ya dauki Europa Conference League a kakar da aka kammala.
Dybala shi ne na hudu da Mourinho ya dauka a bana, bayan Nemanja Matic daga Manchester United da golan Antwerp, Mile Svilar da mai tsaron baya Zeki Celik daga Lille.
Dan kasar Argentina ya zabi saka riga mai lamba 21, wadda aka so Matic ya yi amfani da ita, sai dai dan kwallon Serbia ya dauki mai lamba takwas.











