'Yan wasan Real Madrid da suka je Amurka wasan sada zumunta

Real Madrid za ta buga wasan sada zumunta uku a Amurka, domin shirin tunkarar kakar tamaula ta bana da za a fara cikin watan Agusta.

Real Madrid za ta yi wasannin a birnin Las Vegas da San Francisco da kuma Los Angeles.

Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama za ta fafata da Barcelona a Las Vegas da Club America a San Francisco da kuma Juventus a Los Angeles.

Ga jerin 'yan wasan Real Madrid da suka sauka je Amurka:

Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da Luis Lopez da kuma Lucas Canizares.

Masu tsaron baya: Carvajal da Militao da Alaba da Vallejo da Nacho da Rudiger, da Mendy da Odriozola da kuma Tobías.

Masu wasa daga tsakiya: Kroos da Modric da Casemiro da Valverde da Lucas V. da Tchouameni da Ceballos da kuma Camavinga.

Masu cin kwallo: Hazard da Benzema da Asensio da Vini Jr. da Rodrygo da Mariano da kuma Latasa.

Jadawalin wasannin da Real Madrid za ta buga a Amurka:

Ranar 23 ga watan Yuli Real Madrid za ta fara karawa da Barcelona, wato karon battar El Clasico na farko a bana da za su kece raini a Allegiant Stadium in Las Vegas.

Ranar 26 ga watan Yuli Real Madrid da Club America a filin wasa na Orcale Park, San Francisco.

Ranar 30 ga watan Real Madrid da Juventus a filin wasa na Rose Bowl, Los Angeles