An fitar da 'yan takarar gwarzon kwallon kafar Afirka na 2022

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf ta fitar da 'yan takara uku maza da wasu uku mata masu takarar kyautar gwarzo da gwarzuwar kwallon kafar Afirka a 2022.

An fitar da sunayen ne daga wadanda Caf ta bayyana tun farko da ya kunci maza da mata da yawa don zabar wadanda suka fi yin fice dafa nahiyar a bana.

Za a yi bikin ranar 21 ga watan Yuli a Morocco.

Matan da ke takarar gwarzuwar kwallon kafa ta Afirka ta 2022

Ajara Nchout Njoya (Cameroon & Internazionale Milano)

Asisat Oshoala (Nigeria & Barcelona)

Grace Chanda (Zambia & BIIK Kazygurt)

Masu takarar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na 2022

Edouard Mendy (Senegal & Chelsea)

Mohamed Salah (Egypt & Liverpool)

Sadio Mane (Senegal & Bayern Munich)

Matan da ke takara masu taka leda a gida

Andile Dlamini (South Africa & Mamelodi Sundowns)

Bambanani Mbanie (South Africa & Mamelodi Sundowns)

Evelyn Badu (Ghana & Sekondi Hasaacas Ladies/Alvaldsnes)

Mazan da ke takara masu buga kwallo a Afirka

Achraf Dari (Morocco & Wydad Athletic Club)

Aliou Dieng (Mali & Al Ahly)

Mohamed El Shenawy (Egypt & Al Ahly)

Matashiyar 'yar kwallon kafa ta Afirka

Doris Boaduwaa (Ghana & Sekondi Hasaacas Ladies)

Evelyn Badu (Ghana & Sekondi Hasaacas Ladies/Alvaldsnes)

Yasmine Zouhir (Morocco & AS Saint-Etienne)

Masu takarar matashin da ba kamarsa a Afirka

Hannibal Mejbri (Tunisia & Manchester United)

Karim Konate (Cote d’Ivoire & ASEC/RB Salzburg)

Pape Matar Sarr (Senegal & Tottenham Hotspur)

Koci mace da ke takara a 2022

Bruce Mwape (Zambia)

Desiree Ellis (South Africa)

Jerry Tshabalala (Mamelodi Sundowns)

Reynald Pedros (Morocco)

Koci namji da yafi kowa yin fice a 2022

Aliou Cisse (Senegal)

Carlos Queiroz (Egypt)

Walid Regragui (Wydad Athletic Club)

Kungiyar kwallon kafa ta mata a Afirka da ta taka rawar gani

AS FAR (Morocco)

Hasaacas Ladies (Ghana)

Mamelodi Sundowns (South Africa)

Kungiyar da ba kamarta a tamaula a Afirka

Al Ahly (Egypt)

RS Berkane (Morocco)

Wydad Athletic Club (Morocco)

Tawaga ta maza da ken kan gaba a Afirka

Cameroon

Egypt

Senegal

Goal of the YearKwallon da aka zura a raga mafi kayatarwa

Gabadinho Mhango (Malawi & Orlando Pirates)

Pape Ousmane Sakho (Senegal & Simba)

Zouhair El Moutaraji (Morocco & Wydad Athletic Club)