Ba ni da niyyar komawa jam'iyyar PDP - Shekarau

Asalin hoton, OTHER
Tsohon gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Malam Ibrahim Shekarau, ya ce ba shi da niyyar komawa jam'iyyar PDP mai adawa a kasar.
Shekarau ya bayyana haka ne ta bakin mai magana da yawunsa, Malam Sule Ya'u Sule, a tattaunawarsa da BBC Hausa ranar Talata.
A cewarsa, babu kamshin gaskiya a rahotannin da wasu kafafen Najeriya suka bayar cewa dan takarar shugabancin kasar na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya yi tayin ba shi manyan mukamai idan ya koma jam'iyyar.
Sule Ya'u Sule ya ce Malam Shekarau, wanda yanzu haka shi ne Sanatan da ke wakiltar Kano ta Tsakiya a Majalisar Dattawan kasar, yana nan daram a jam'iyyar NNPP.
Amma ya kara da cewa hasashen da ake yi na komawarsa PDP na da nasaba da yadda bangaren tsohon gwamnan Kano Rabi'u Kwankwaso ya gaza cika alkawuran da suka yi a yarjejeniyar da suka kulla lokacin da zai shiga NNPP.
Sule Ya'u ya ce idan ban da Sanata Shekarau babu wani daga cikin mutanensa da bangaren Kwankwaso ya bai wa wani mukami ko kujera a yarjejeniyar shigarsa jam'iyyar tasu.
Ya tabbatar da cewa wasu jiga-jigan 'yan siyasa daga jam'iyyun daban-daban na kasar suna tuntubar Sanata Shekarau domin ganin ya koma jam'iyyunsu, ko da yake ba shi da niyyar yin haka.
Ya kara da cewa cikin wadanda suka tuntube shi har da Atiku Abubakar, da dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi; da dan takarar mataimakin shugaban kasa a jam'iyyar APC, Sanata Kashim Shettima.
Shekarau ya ce Peter Obi ya neme shi ne domin ya zama mataimakinsa, yayin da shi kuma Tinubu ya nemi ya koma APC domin ya taka rawa a zaben 2023.
A cewarsa, kawo yanzu bai yanke shawara kan ko zai koma wata jam’iyya ba, yana mai cewa sai wani kwamiti mai mutum talatin ya zauna ya yi nazari kafin ya yanke hukunci kan mataki na gaba.
Ranar 29 ga watan Yuni ne Ibrahim Shekarau ya sanar da shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan ficewarsa daga jam'iyyar APC zuwa NNPP a hukumance.

Asalin hoton, Facebook/Hon Saifullahi Hassan
Sai dai tun 18 ga watan Mayu tsohon gwamnan na Jihar Kano ya fita daga jam'iyyar APC zuwa NNPP yana mai cewa ya yi hakan ne domin ceto Jiharsa daga mawuyacin halin da take ciki.
Kafin fitarsa daga APC, Shekarau ya rika zaman doya da manja tsakaninsa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, sakamakon zargin da ya yi cewa gwamnan bai iya gudanar da mulki ba.










