Ibrahim Shekarau: Manyan dalilan da suka sa tsohon gwamnan Kano ya fita daga APC ya koma NNPP
Danna hoton da ke sama domin kallon bidiyon:
Tsohon gwamnan Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, Sanata Ibrahim Shekarau, ya ce ya fita daga jam'iyyar APC zuwa jam'iyyar NNPP ne domin ceto Jiharsa daga mawuyacin halin da take ciki.
Tsohon gwamnan wanda kuma tsohon Minista ne, ya shaida wa BBC Hausa cewa "mun dade muna tattaunawa da dan uwana Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso, muna nuna damuwarmu ga makomar Kano" shi ya sa suka hada gwiwa domin ganin sun fitar da Jihar daga matsalolin da take fama da su.
"Mun tattauna mun gaya wa kanmu cewa wajibi mu kawo sauyi a Kano...idan ba mu waiwayi al'ummarmu mun sama wa Kano mafita ba, Allah zai tuhume mu. Damuwarmu ita ce ci gaban al'ummar Kano da Najeriya," in ji Sanata Shekarau.
Ya kara da cewa sun bar APC ne domin ba a yi musu adalci don haka suke ganin komawarsu NNPP ita ce hanyar da za su kawo sauyi ga al'ummarsu.
Sanata Shekarau ya ce "ni a ganina siyasa mu'amala ce. Shi ya sa nakan ce duk jam'iyyun nan uwarsu daya, ubansu daya. Ba sunan jam'iyyar muke bi ba, abin da muke bi shi ne inda za su samu mutunci da walwala" yana mai cewa samun mukami ba shi ne babban burinsu ba domin kuwa "wannan a hannun Allah yake".
'Matsalata da gwamnatin Ganduje'
Shekarau ya bayyana cewa gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ba ta yi musu adalci ba duk da kokarin da suka yi wajen ganin ta yi nasara a zabukan jihar.
"Abin da ya jawo jayayyarmu shi ne tun da aka yi zaben 2019, kujera daya Gwamna ya ba mu (na Kwamishinan Kudi Shehu Na'allah Kura), duk da gudunmawar da muka bayar. Mun taho da miliyoyin mutane wadanda suke mana hidima kusan shekara ashirin amma ba a yi musu komai ba," in ji shi.
Makomar siyasar Jihar Kano

Asalin hoton, Facebook/Hon Saifullahi Hassan
Shigar Sanata Shekarau da tawagarsa cikin jam'iyyar NNPP wani babban kalubale ne ga jam'iyyar APC mai mulkin kasar, a cewar masana harkokin siyasa.
Farfesa Kamilu Sani Fagge, Malami a Tsangayar Nazarin Siyasa a Jami'ar Bayero da ke Kano, ya shaida wa BBC cewa babu wanda ya fi Sanata Kwankwaso da Sanata Shekarau magoya baya a siyasar Kano, don haka hadewarsu tamkar kawo karshen APC ne a Jihar.
"Tasirin da kowanne yake da shi shi ne dimbin mabiya - don haka hada karfirsu zai sa su kayar da APC warwas idan aka gudanar da zabe cikin adalci. Idan kuma aka yi karfa-karfa mai yiwuwa su ci kasa," in ji Farfesa Fagge.
Shi kuwa Malam Kabiru Sa'idu Sufi, mai koyar da Harkokin Siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Kano, ya ce karbuwar jam'iyyar NNPP a wurin al'ummar Jihar ta Kano ita ce za ta nuna irin "tasirinta a zabukan da ke tafe."












