Shin NNPP za ta kwace ragamar siyasar Jihar Kano ne?

Matasa

Asalin hoton, Facebook/Kwankwasiyya Reporters

Bayanan hoto, Kwankwasiyya ita ce rushin jam'iyyar NNPP inda matasa suke kan gaba wajen tallata ta

Tun lokacin da fitaccen dan siyasar nan na Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya fita daga jam'iyyar PDP mai hamayya a kasar sannan ya shiga jam'iyyar New Nigeria People Party, NNPP, masu nazari kan harkokin siyasa suka soma hasashen irin tasirin da jam'iyyar za ta yi musamman a Jihar Kano, inda ya fi karfi a siyasance.

A ranar Talata 29 ga watan Maris tsohon gwamnan kuma tsohon Ministan Tsaro a kasar ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa sabuwar jam'iyya ta NNPP.

Ya fice daga PDP ne bayan rikicin cikin-gidan jam'iyyar ya ki ci ya ki cinyewa.Kuma a yayin da yake jawabi bayan shiga NNPP, Kwankwaso ya ce babban burinsa shi ne ceto Najeriya daga mawuyacin halin da ta fada a ciki.

Jim kadan bayan hakan ne kusan daukacin magoya bayansa da ke Majalisar Dokokin Jihar suka fita daga jam'iyyar PDP, wadda ita ce babbar jam'iyyar hamayya a jihar kafin fitarsa, inda suka bi shi NNPP.

Baya ga wannan, wasu jiga-jigan jam'iyyar - kama daga kansiloli zuwa tsoffin shugabannin kananan hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki a kungiyar Kwankwasiyya a Jihar sun tsunduma cikin jam'iyyar ta NNPP.

Sai dai duk da haka akwai magoya bayan Sanata Kwankwaso da suka rage a jam'iyyar PDP, abin da masana harkokin siyasa suke fassarawa a matsayin wata dabara ta siyasa ta tsohon gwamnan na Jihar Kano.

Don haka a yanzu, jam'iyyar ta NNPP ita ce babbar jam'iyya a Jihar Kano, kamar yadda wani jigo a NNPP, Ali Bukar Ahmad, wanda shi ne Sakataren Tsare-Tsare na kungiyar Kwankwasiyya, ya shaida wa BBC Hausa.

Ya kara da cewa: "Tun da shugabanmu Sanata Kwankwaso ya shiga NNPP, kusan daukacin 'yan majalisar dokokin Jiha na PDP idan ban da mutum biyu, sun koma NNPP."

A cewarsa, su ma 'yan majalisar dokokin tarayya wadanda a karshen makon jiya suka bayyana ficewa daga jam'iyyar APC, sun soma tuntubar shugabannin jam'iyyar NNPP da zummar shiga cikin jam'iyyar.

Tuni dai wasu manyan 'ya'yan jam'iyyar APC da suka hada da 'yan majalisar dokokin tarayya irin su Kabiru Alhassan Rurum da Abdulmumi Jibrin suka bayyana ficewa daga APC, ko da yake ba su fayyace jam'iyyar da za su shiga ba.

Kazalika wasu bayanai sun nuna cewa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Ibrahim Shekarau da wasu na-hannun-damansa da ma karin 'yan majalisun dokokin suna shirin komawa NNPP.

Sai dai shugabannin jam'iyyar ta APC sun soma daukar matakan hana wadannan 'yan siyasa komawa wasu jam'iyyu kamar yadda suka bayyana a wani sako da shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Abbas, ya fitar a karshen mako jim kadan bayan Honorabul Abdulmumin ya bayyana aniyarsa ta ficewa daga jam'iyyar ta APC.

'Zabin da ya rage'

Masana harkokin siyasa da dama na ganin jam'iyyar NNPP za ta ci moriyar rikicin da ke faruwa a cikin APC da ma PDP, musamman bayan an kammala zabuka fitar da gwani a karshen watan nan.

Malam Kabiru Sa'idu Sufi da ke Koyar da Harkokin Siyasa a Kwalejin Share Fagen Shiga Jami'a ta Jihar, ya shaida wa BBC cewa NNPP "za ta kasance zabin da ya rage wa wasu 'yan siyasar APC da PDP a jihar Kano idan ba su samu abin da suke neman ba a zaben fitar da gwani."

"Misali, yanzu kusan daukacin 'yan majalisar dokokin jiha na jam'iyyar PDP sun narke a NNPP, sannan su Sanata Kwankwaso sun bar shugabannin PDP suna ci gaba da rike mukamansu a matsayin wata dabara ta siyasa.

Bayan haka, kusan duk wanda bai samu abin da yake so ba a APC a Kano zai iya tafiya NNPP domin biyan bukatarsa. Ka ga kuswa hakan zai kara wa jam'iyyar karfi sosai ta kasance babbar barazana ga jam'iyyar mai mulki."

Masanin siyasar ya ce ita kanta NNPP za ta fuskanci kalubale idan ba ta iya tafiyar da harkokinta ba.