Abinci loma uku, duka da sanda: Rayuwa a dabar ƴan fashin dajin Zamfara

Ɗan fashi a dajin Zamfara, arewa maso yammacin Najeriya
Lokacin karatu: Minti 4

Wasu mutanen da aka ceto bayan shafe sama da wata ɗaya hannun masu garkuwa da mutane a jihar Zamfara sun bayyana yadda suka fuskanci uƙuba da cin zarafi iri-iri a hannun 'yanbindigar da suka yi garkuwa da su.

Zamfara, kamar sauran jihohin arewa maso yammacin Najeriya na fama da ayyukan ƴan fashin daji masu kisa da garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, lamarin da ya haifar da asarar rayuka da durƙusar da ayyukan tattalin arziƙi.

A yammacin Talata ne ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro ya miƙa mutane 128 ga gwamnatin jihar ta Zamfara bayan nasarar ceto su daga hannun 'yanfashin daji.

Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya faɗa wa BBC cewa dakaru sun ceto mutanen ne bayan garkuwa da su a ƙaramar hukumar Kaura.

Da yake gabatar da su ga manema labarai, Ribadu ya ce rukunin farko na mutanen sun kai 42, waɗanda aka ceto ranar 14 ga watan Agusta. Sai kuma rukuni na biyu su 88 da aka kuɓutar ranar 19 ga watan na Agusta.

Wasu daga cikinsu sun faɗa wa BBC cewa sun shafe sama da wata ɗaya a hannun masu garkuwar, waɗanda suka addabi kusan duka jihohin arewa maso yammacin ƙasar.

Mutanen da suka kuɓuta daga hannun 'yanbindigar sun sha bayyana yadda a wani lokacin ma masu garkuwar kan sayar da su ga wani gungun ƴan daban, ko kuma ma a ƙwace su da ƙarfin tsiya.

Duk da nasarar da gwamnatin Najeriya ke cewa tana samu a yaƙi da 'yanfashin, har yanzu sukan sace tare da ƙona gidaje masu yawa, kamar yadda suka yi 'yan kwanaki da suka wuce yayin wani hari kan masallaci a Malumfashi.

'Abinci loma uku ake ba mu'

Wasu daga cikin mutanen da gwamnatin Najeriya ta ce ta kuɓutar daga hannun masu garkuwa a jihar Zamfara ranar 14 da 19 ga watan Agusta.

Asalin hoton, Nigerian Government

Mutanen da suka ƙunshi mata da maza da yara, sun faɗa wa BBC yadda ake ɗaure su da igiya, da barin su da yunwa, da kuma kwana a fili yayin da ake zabga ruwan sama.

Wani namiji da muka ɓoye sunansa ya ce ɗauri nau'i uku ake yi musu idan dare ya yi.

"Cikin sagagi ake kurɗa mu a ɗaɗɗaure. Idan dare ya yi kuma ɗauri uku ake yi mana; a ɗaure hannaye, a ɗure ƙafafuwa," in ji shi.

Game da abinci kuma, ya ce ba kullum ake ba su ba.

"Da magariba akan ba mu loma uku, da safe kuma yakan ɗan ɗara loma uku kuma akwai ranar da ba su ba mu."

'Duka da sanda'

Wata mace kuma ta bayyana yadda aka riƙa dukansu da sanda, sannan ta jaddada da yadda ake barin su da yunwa.

"An sha dukan mutane, ni ma sau biyu ana duka na da sanda," a cewarta. "Akwai takura tun da ba abinci ake ba mu ba. Idan aka ba mu sau biyu shikenan."

Haka nan, wata daban ta ce a wasu lokutan kaɗan an kai su wata baranda domin fakewa idan ana ruwan sama, amma a mafi yawan lokuta ruwan saman yana ƙarewa ne a kansu.

A gefe guda kuma, wani dattijo da ya ce ya shafe kwana 31 a hannun masu garkuwar, ya ce ko kwanciya zai yi sai ya nemi izinin 'yanbindigar.

"Sun azabtar da mu da yunwa da ƙishin ruwa. Ko kwantawa zan yi sai na nemi izini. Amma yanzu dai mun gode wa Allah."

'Kisa, fyaɗe, rashin imani'

A baya ma an sha samun rahotannin yadda masu garkuwa da mutane ke aikata miyagun abubuwa kan mutanen suke garkuwa da su a arewa maso yammacin Najeriya.

Wani bayani na kwalejin London School of Economics ya bayyana cewa irin waɗannan ƴan fashin daji sun riƙa amfani da fyaɗe a matsayin makami a jihohi irin su Neja da Zamfara.

Ko a cikin watan Yuli ƴan fashin dajin sun yi wa mutum 38 yankan rago, daga cikin mutum 56 da suka yi garkuwa da su sakamakon gaza cika kuɗin fansa da ƴanbindigar suke nema.

Shugaban ƙaramar hukumar Ƙauran Namoda a jihar ta Zamfara, inda abin ya faru ya shaida wa BBC cewa "ƴanbindigar sun nemi kuɗin fansa na naira miliyan 50 kuma an ba su amma duk haka suka zaɓi su kashe mutum 38. Su sukan san dalilin kashe su."

Ba za mu ƙyale 'yanbindiga ba - Ribadu

Nuhu Ribadu

Asalin hoton, ONSA

Nuhu Ribadu ya ce jimillar mutum 128 da suka kuɓutar sun shafe fiye da mako ɗaya suna samun kulawar likitoci a hannunsu.

Ya ƙara da cewa akwai ƙaramin yaro ɗaya da ya rasu a asibitin sakamakon raunukan da ya ji, yana mai cewa sun samu nasarar kuɓutar da su ne ba tare da biyan ko kwabo ba.

"Babu wanda muka bai wa wani abu domin kuɓutar da waɗannan mutane," a cewarsa. "Har yanzu akwai kusan mutum biyar da ke asibiti."

Babban jami'in a harkokin tsaro ya ce suna ci gaba da bin sawun 'yanbindigar da suka kashe sama da mutum 30 a garin Malumfashi na jihar Katsina.