Hare-hare shida da ƴanbindiga suka kai kan masu sallah a Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Mummunan harin da ƴanbidiga suka kai wa wasu masallata a masallacin jihar Katsina tare da kashe masu ibada na ci gaba da tayar da hankali a Najeriya.
Maharan sun far wa masallatan a lokacin da suke tsaka da sallar asuba a garin Unguwar Mantau cikin ƙaramar hukumar Malumfashi tare da buɗe musu wuta.
Harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28 tare da jikkatar wasu da dama.
Wasu garuruwan yankunan arewa maso yammacin Najeriya na fama da hare-haren ƴanbindiga waɗanda a wasu lotukan kan tilasta wa mazauna garuruwa da ƙauyuka tserewa.
Sai dai a wasu lokutan maharan kan far wa masallatai a lokacin da mutane ke tsaka da ibada, tare da kashe su ko kuma sace da dama daga cikinsu.
Wasu lokuta da ƴanbidiga suka kai wa masallata hari a Najeriya
Alƙaluma daga kamfanin tsaro Beacon Security da kamfanin tsaro na Armed Conflict Location & Event Data (ACLED), sun nuna cewa akwai hare-hare da dama da ƴanbindiga suka kai kan masallatai a Najeriya.
Ga wasu daga ciki da muka zaƙulo, masu alaƙa da ƴan fashin daji, la'akari da rahotonnin da aka samu a lokacin faruwarsu.

Asalin hoton, Getty Images
Masallacin Unguwan Mantau, Katsina - 2025
A ranar Talata 19 ga watan Agustan 2025 ƴanfashin dajin suka kai hari masallacin garin Unguwan Mantau da ke yankin ƙaramar hukumar Malumfashi a jihar Katsina.
Mazauna garin sun shaida wa BBC Hausa cewa lamarin ya faru ne da asubahi.
"Muna tsaka da sallah suka buɗe mana wuta, mutum 28 muka yi wa jana'iza ciki har da mahaifina," in ji wani mutum da muka ɓoye sunansa cikin kuka da share hawaye.
"A gida suka ritsa shi [mahaifin], suka kulle shi a ɗaki, suka zuba fetur kuma suka kunna wuta."
Wani mutumin daban ya ce maharan sun ƙona mata da ƙananan yara a cikin gidaje "tare da sace kusan mutum 100".
Masallacin Tsafe, Zamfara - 2024
Haka ma a watan Fabrairun 2024, wasu mahara ɗauke da makamai a kan babura suka far wa wani masallaci a garin Tsafe na yankin ƙaramar hukumar Tsafe tare da sace masallata kimanin 30.
A lokacin harin mazauna garin sun shaida wa BBC cewa yanbindigar sun kai hari ne a lokacin da mutanen ke tsaka da sallar asuba.
Harin ya ɗauki hankali a lokacin musamman a kafafen yaɗa labarai.
A lokacin harin gwamnatin jihar Zamafar ta ce ta ɗauki matakin sanar wa jami'an tsaro halin da ake ciki, inda ta shaida wa BBC cewa tuni aka tura sojoji cikin daji da nufin kuɓutar da mutanen.
Birnin Gwari, Kaduna - 2023
Alƙaluman na Beacon Security sun nuna cewa a 2023 wasu ƴanbindiga sun kai hari masallacin Birnin gwari, inda suka kashe limamin masallacin da wasu mutum biyu.
A lokacin afkuwar harin, rahotonni sun bayyana cewa wasu ƙarin mutum biyu sun jikkata.
Lamarin ya faru ne a lokacin da mutanen ke sallar asuba a masallacin, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito a lokacin.
Bukkuyum, Zamfara - 2022
Bayanan da kamfanin Becon Security ya tattara sun nuna cewa a 2022 an samu wani hari kan masallata a ƙauyen Ruwan Jema dake ƙaramar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.
Bayanan da aka samu a lokacin harin sun bayyana cewa 'yan bindiga sun kashe mutum 18 a masallacin Juma'a na garin.
Majiya da dama daga ƙauyen sun bayyana cewa maharan sun afka ƙauyen da misalin karfe 1 na rana a lokacin da masallata ke shirin yin sallar juma'a
Masallacin Maigamji, Katsina - 2022
A watan Disamban 2022 ma wasu ƴanbindiga ɗauke da muggan makamai suka kai hari tare da sace masallata kusan 20 a wani masallaci a ƙauyen Maigamji da ke yankin ƙaramar hukumar Funtua a jihar Katsina .
Bayanan da BBC ta samu a lokacin harin sun nuna cewa maharan sun kai farmaki masallacin ne da daddare lokacin da masallatan suka taru domin gudanar da sallar Isha'i.
A lokacin harin rundunar ƴansandan Katsina ta shaida wa BBC cewa an raunata limamin masallacin tare da wani mutum guda, inda aka garzaya da su asibiti, kodayake ba su jima ba aka sallamo su.
Ƴansandan sun ce tawagar jami'an tsaro da ta ƙunshi sojoji da ƴan sanda da ƴan sa kai sun samu nasarar kuɓutar da wasu daga cikin waɗanda aka sacen
Masallacin Jibia, Katsina - 2021
Bayanai daga kamfanin Beacon Security mai nazarin harkokin tsaro a ƙasashen Afirka ya nuna cewa a shekarar 2021 wasu ƴanbindiga suka kai hari kan masallacin Jibia a jihar Katsina
Cikin watan Mayun 2021 ne wasu mahara ɗauke da makamai suka far wa masallacin Abbatuwa da ke garin Jibia tare da sace aƙalla masu ibada 40 - kodayake daga baya 30 sun kuɓuta - a lokacin da suke tsaka da sallar Tahajjud.
Bayanan da aka samu a lokacin faruwar harin sun nuna cewa maharan sun zagayen masallacin a lokacin da jama'a ke tsaka da sallah inda wasu suka shiga suka kashe na'urar amsa kuwwar da ake amfani da ita a masallacin, daga nan suka bai wa mutane umarnin fita waje, suka kuma yi awon gaba da adadin aƙalla 40.
Me ya sa ƴanbindiga ke far wa masallata?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Kabiru Adamu, shugaban Kamfanin Beacon Security, mai nazari kan al'amuran tsaro ya ce abin da ya sa ƴanbindiga ke far wa masallatai shi ne son nuna iko, domin cimma burin buƙatocinsu.
Masanin tsaron ya ce wani dalili ne shi ne masallaci wuri ne da mutane ke taruwa a duk lokacin ibada, don haka hari kan masallatan na bai wa ƴanbindigar damar sace mutane masu yawa a lokaci guda.
''haka kuma masallaci wuri ne da ba a ajiye makamai a ciki, don haka wannan nan ma na bai wa ƴanbidiga ƙwarin gwiwar zuwa su sace mutane ba tare da wata fargaba ba'', in ji shi.
Ya ƙara da cewa maharan na amfani da hari kan masallatai domin razana jama'a da son ɗaukar hankalin duniya.
Ta yaya za ku kare kanku?

Asalin hoton, Getty Images
Dakta Kabiru Adamu ya ce abin da ya kamata jama'a su yi shi ne inganta tsaro a wuraren ibadarsu.
Ya ce wanda ya wajaba ya yi shi ne gwamnati, idan ba ta yi ba sai jama'ar yanki su ɗauki makatsan tsare wuraren ibadarsu.
''A addinance akwai damar da aka bayar da raba kai zuwa gida biyu, ɗaya rukunin ya kare ɗaya yayin da ya ke sallah, in ya gama ɗayan kuma ya yi'', in ji shi.
Ya ci gaba da cewa yana da kyau jami'an tsaro su tsananta tsaro a wuraren ibada, saboda yawan maimatuwar hare-hare kan wuraren ibadar.
Haka kuma Kabiru Adamu ya ce yana da kyau malamai su ƙarfafa faɗakarwa kan muhimmancin wuraren ibada a addinance da illar kai wa wuraren ibadar hari.











