Likitan da ya gane wa idonsa abu mai kama da 'tashin duniya' a Gaza

Asalin hoton, Foreign Office
- Marubuci, Angela Ferguson & Roger Johnson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Greater Manchester
- Lokacin karatu: Minti 3
Wani likita daga Manchester a Birtaniya ya bayyana abubuwan da idonsa suka gani na yadda aka yi "raga-raga" da Gaza a lokacin da yake aikin kiwon lafiya a yankin.
Dokta Matt Newport, wanda ɗan asalin Ramsbottom ne, likita ne a asibitin Royal Blackburn da ke Ingila, sannan ya kasance ya je yankin wanda yaƙi ya ɗaiɗaita sau uku a bana, inda yake zuwa domin aiki tare da gidauniyar UK-Med.
Ya ce kashi 40 na waɗanda suke jinya a asibitin UK-Med ƙananan yara ne.

Asalin hoton, Foreign Office
Dr Newport ya ce abubuwan da ya gani sun sa ya ƙara ƙaunar ƴarsa, wanda ya sa yake rumgume ta, "sosai."
Ma'aikacin kiwon lafiyar ya ce yana yawan duba marasa lafiya da suke jinyar raunukan harbin bindiga.
"Yara ƙanana da mata da dama ne ake kawo mana da suka ji rauni na harbin bindiga da suka taɓa ni sosai."
"A matsayina na mahaifi, mai yarinya ƴar shekara biyu, ganin ƙananan yara cikin fargaba da damuwa ya matuƙar ɗaga min hankali," in ji shi.
Shi da abokan aikinsa sun riƙa gudanar da aiki yayin da rugugin bindigogi ke tashi.
Dr Newport mai shekara 37, ya ce akwai buƙatar a "kawo ƙarshen yaƙin," bisa yadda ake cutar da fararen hula ba tare da sun yi laifin komai ba.
Ya ce aiki a Gaza ya sa ya ƙara fahimtar amfanin inshorar kiwon lafiya.
Ma'aikacin lafiyar ya ce zai "cigaba da komawa ina yin abin da zan iya," sannan ya ƙara da cewa yana jin daɗin yi wa ƴarsa bayanin gane muhimmancin aikin agaji.
Gidauniyar UK-Med na cikin ayyukan agaji da gwamnatin Birtaniya take yi a yaƙin Isra'ila/Gaza.
Kakakin UK-Med ya ce yanzu gidauniyar na da asibitoci biyu a ƙasashen waje, waɗanda suke aiki a Al Mawasi da Deir El Balah, waɗanda zuwa yanzu suka yi sama da mutum 100,000 jinya a Gaza.
Ma'aikatar Lafiya ta ƙarƙashin Hamas da ke Gaza ta ƙiyasta cewa sama da mutum 40,000 aka kashe a Gaza tun bayan ɓarkewar yaƙin bayan harin 7 ga Oktoban 2023 wanda Hamas ta kai.
Sai dai Isra'ila ta daɗe tana ɗiga alamar tambaya a kan sahihancin bayanin. A watan Mayu, Ministan Harkokin Wajen Isra'ila, Israel Katz ya bayyana labarin, "kididdigar ƙarya daga ƙungiyar ta'adda."











