Gaza: Ko Isra’ila ta samu biyan bukata bayan wata shida da fara yaki?

.

Kusan watanni shida ke nan da mayakan Hamas suka kutsa Isra'ila ta cikin Gaza inda suka kai harin da ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 1,200 tare da yin garkuwa da daruruwa.

A wani mataki na ramuwar gayya, Isra'ila ta dauki alwashin kakkabe Hamas da kawo karshen matsalolin da take haifarwa da kuma kubutar da wadanda aka yi garkuwa da su.

A mummunan yakin da ya biyo baya, akalla Falasdinawa 33,000 aka kashe, kamar yadda Hukumar Lafiya da Hamas ke iko da ita ta bayyana. Bugu da 'kari an lalata rabin Gaza.

Isra'ila ta ce ta kashe dubban mayakan Hamas tare da lalata mafi yawa daga cikin manyan hanyoyin 'kar'kashin 'kasa a Gaza, wadanda Hamas ke amfani da su wajen kai hare-hare.

BBC ta bincika bayanan jama'a da shafukan soshiyal midiya na dakarun Isra'ila domin tabbatar da wannan rahoto na Isra'ila.

Shugabannin Hamas nawa aka kashe?

Kafin harin na ranar 7 ga watan Oktoba, ana hasashen Hamas na da mayaka kusan 30,000 a Gaza, kamar yadda rahotannin kwamandojin Dakar un Isra'ila suka bayyana.

A wata sabuwar sanarwa, dakarun Isra'ila sun ce sun yi nasarar kashe kusan mayakan Hamas 13,000 tun daga lokacin da aka fara yakin, duk da cewar ba su bayyana yadda suka samu wannan adadi ba.

Isra'ila ta kuma wallafa sunayen shugabannin Hamas da ta ce ta kashe.

Kimanin mutane 113 ne aka bayyana sunayensu tun daga watan Oktoba, akasarin wadanda aka ce an kashe a watanni uku na farkon yakin. Sojojin na Isra'ila ba su bayar da rahoton wani babban jami'in Hamas da aka kashe a Gaza ba a cikin wannan shekara har zuwa Maris.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A ranar 26 ga Maris dakarun Isra'ila sun sanar da kashe Marwan Issa, mataimakin kwamandan reshen soja na Hamas. Kasancewar daya daga cikin mutanen da Isra'ila ke nema ruwa a jallo, ya kuma zamo babban shugaban kungiyar da aka kashe tun lokacin da aka fara yakin. Amurka ta ce ta yi imanin cewa an kashe shi duk da cewar Hamas ba ta tabbatar da hakan ba.

Rundunar sojin Isra'ila IDF ta wallafa sunayen wasu mutanen da ta ce manyan shugabannin Hamas ne da aka kashe, amma babu tabbas ko 'yan kungiyar ne. Daya daga cikin wadanda aka ambata a cikin wannan rukunin shi ne Mustafa Thuraya, wanda ke aiki a matsayin dan jarida mai zaman kansa a kudancin Gaza lokacin da aka afka wa motarsa ​​a watan Janairu.

Mun samu wasu sunaye da aka maimaita cikin jadawalin, tuni muka janye su daga cikin adadin.

Jagoran siyasar Hamas Saleh al-Arouri ya mutu sakamakon fashewar wani abu a yankin kudancin birnin Beirut na Dahiyeh a watan Janairu. An dora alhakin kisan kan Isra'ila .

Sai dai 'kwararru da muka ji ta bakinsu sun ce fitattun shugabannin Hamas a Gaza da suka hada Yahya Sinwar na nan da ransu.

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Da dama daga cikin shugabannin 'kungiyar da suka hada da Yahya Sinwar na nan a raye.

"Rundunar IDF ba ta iya kaiwa ga manyan shugabannin Hamas ba," in ji Mairav ​​Zonszein, wani babban manazarci kan al'amuran Isra'ila da yankin Falasdinawa.

Mutanen da aka yi garkuwa da su nawa ne suka rage a Gaza

Alkaluman hukuma a Isra'ila sun ce an yi garkuwa da mutane 253 a ranar 7 ga Oktoba:

An sako wasu a wani bangare na musayar fursunoni a lokuta daban-daban.

Sojojin Isra'ila sun kubutar da wasu mutum uku lokacin wani samame da suka kai.

An gano gawarwaki 12 na mutanen da aka yi garkuwa da su da suka kunshi mutane uku da dakarun IDF suka kashe a wani lokaci da suka kai farmaki.

Mafi karancin shekaru cikin wadanda suke tsaren shi ne matashi mai shekaru 18 wanda ya fi kowa shekaru kuma wani tsoho ne mai shekaru 85.

Isra'ila ta bayyana cewar daga cikin mutane 129 da suka rage 34 sun mutu

Hamas ta kara da cewar adadin wadanda suka mutu ya fi haka sakamakon hare-haren dakarun IDF, To sai dai tabbatar da wannan batu ya yi wahala.

Matasa biyu masu ƙarancin shekaru da aka yi garkuwa da su a hare-haren Hamas su ne Ariel da Kfir, masu shekaru 4 da watanni 9 a lokacin da aka yi garkuwa da su. An ba da rahoton mutuwarsu, amma ba a tabbatar da hakan ba.

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, A watan Fabrairu aka sako Fernando Simon Marman tare da Louis Hare

Hanyoyin Hamas na karkashin kasa guda nawa aka lalata?

A wani bangare na alwashin da ta sha na kawar da Hamas, Isra’ila ta yi alkawarin lalata hanyoyin karkashin kasa na Hamas da ke a fadin Gaza, wadanda take amfani da su wajen safarar abubuwan bukata da kuma al’umma.

A watan Oktoba, mai magana da yawun dakarun Isra’ila, Jonathan Conricus, ya ce: “Abin da ke faruwa shi ne a Gaza akwai hawa biyu, akwai hawan da na fararen hula ne yayin da kasa kuma na Hamas ne. Muna so ne mu bankado wurin da Hamas ta gina”.

A baya Hamas ta bayyana cewa hanyoyinta na karkashin kasa sun kai tsawon kilomita 500, wato mil 311, duk da dai babu wata hanya ta tantance gaskiyar hakan.

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Hamas ta ce hanyoyinta na karkashin kasa sun kai tsawon kilomita 500

Mun tambayi dakarun Isra’ila game da yawan hanyoyin karkashin kasa na Hamas da suka lalata, a martanin da suka bayar, IDF ta ce dakarunta “sun lalata da dama daga cikin wuraren da ‘yan ta’adda suka gina a Gaza”.

A lokuta da dama rundunar sojin Isra’ila ta sha nuna wasu hanyoyin karkashin kasa na Hamas da suka gano.

Misali, a watan Nuwamba IDF ta fitar da bidiyon wata hanyar karkashin kasa da ke a karkashin asibitin al-Shifa a Gaza, wadda Isra’ila ta yi ikirarin cewa ana amfani da ita a matsayin wata cibiyar ayyukan Hamas.

A kokarin gani yawan hanyoyin karkashin kasa da sojojin Isra’ila suka gano a Gaza, sashin fayyace gaskiya na BBC Verify ya duba sakonnin da IDF ta wallafa shafinta na sada zumunta da ke nuna hanyoyin karlashin kasa a Gaza tsakanin 7 ga watan Oktoban 2023 zuwa 26 ga watan Maris 2024.

Daga cikin abubuwan da aka wallafa, sau 198 aka ambato cewa an gano hanyoyin karkashin kasa. Sannan wasu sakonnin 141 da aka wallafa sun bayyana cewa an lalata ko tarwatsa hanyar karkashin kasa.

Akasarin sakwannin da aka wallafa ba su bayar da cikakken bayani ko wurin da abin ya faru ba, saboda haka ba zai yiwu a iya tantance yawan hanyoyin karkashin kasa da sojojin Isra’ila suka gano ko suka lalata ba.

Hanyoyin karkaahin kasa da ke Gaza sun kunshi abubuwa da dama, kamar hanyoyin da ake bi da dakuna masu girma daban-daban da kuma hanyoyin da suka hawo zuwa doron kasa.

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, An lalata akasarin yankin Gaza tun bayan barkewar yaki watanni shida da suka gabata

A cikin sakonnin da aka wallafa wadanda muka yi nazari a kansu, 36 daga cikin sun bayyana cewa an lalata sama da hanyoyi karkashi kasa sama da 400.

Sai dai kuskure ne a tabbatar da cewa lalata hanya daya ta shiga karkashin kasa na nufin an lalata dukkanin hanyoyin da sula hada da ita, in ji Dr Daphné Richemond Barak, wadda ke da ilimi kan yakin karkashin kasa a jami’ar Reichman University da ke Isra’ila.

Lalata hanyar shiga hanyoyin karkashin kasa kawai ba zai yi illa ga sauran hanyoyin da ke can karkashin kasa ba, kamar yadda ta bayyana. “Idan aka yi la’akari da zurfin ramukan karkashin kasa na Hamas, ba abu ne mai yiwuwa a ce an lalata dukkanin hanyoyinsu na karkashin kasa ba,” in ji ta.

Wasu mutanen da dama an tarwatsa su tare da barin babu muhalli a lokacin da dakarun Isra’ila ke kokarin lalata ci iyoyin Hamas.

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa sama da mutum miliyan 1.7 aka mayar da su ‘yan gudun hijira a yankin.

An shafe unguwanni da wuraren zaman al’umma, an lalata hanyoyi, an tarwatsa jami’o’i sannan an lalata gonaki.

An rushe ko kuma lalata sama da kashi 56 cikin dari na gine-ginen da ke a Gaza tun daga 7 ga watan Oktoba, kamar yadda hotunan tauraron dan’adam ya nuna.

Wata shidda bayan kaddamar da wannan yaki har yanzu babu tabbas ko Isra’ila ta cimma manufarta game da yakin.