Ko an maye gurbin Ibro a Kannywood shekara 10 da rasuwarsa?
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 5
Duk da ya bar duniya shekara 10 da suka wuce, har yanzu Rabilu Musa Ibro na cikin taurarin fim da ke da farin jini ga masu neman nishaɗi da kuma son kashe kwarkwatar idanunsu.
Har yanzu ƙananan bidiyon finafinansa na karakaina sosai a shafukan sada zumunta kamar Facebook da Tiktok.
Ya dai zama wani Mahadi mai dogon zamani - aƙalla a duniyar Kannywood.
Gwaninta da hazaƙa da kuma ƙwarewar zaƙaƙurin ɗan wasan finafinan barkwancin wajen iya sarrafa harshe, da nuna gargajiyar Bahaushe, da amfani da salo mai sauƙi don aika saƙo sun riƙa sa ƙarin ɗanɗano da armashi a finafinansa da ake shirya su da kuɗi ƙalilan.
Ya kai ƙololuwar ganiyarsa musamman a wajen masu ganin baiken finafinan da ke nuna "rayuwar ƙarya ta ƴan birni" da "raye-rayen ƴan mata masu ɗamammun tufafi" a kan titi.
Saurin yi da fitar da finafinansa masu zubi na daban, inda mafi yawa ke ɗauke da tambarin sunansa - kamar Ibro Angon Hajiya, Andamali, Na-Mamajo da Ibro Ɗan Almajiri, Ibro Ya Auri Baturiya, Ibro Ɗan Fulani, Ibro Ɗan Zaki, Ibro Ɗan Siyasa, Ibro Police - cikin sauƙi suka riƙa mamaye kasuwa.
Da wuya a iya cewa tabbas ga yawan finafinan Ɗan Ibro.
Yana kan sharafinsa lokacin da mutuwa ta riske shi a ranar Laraba 10 ga watan Disamban 2014.
Ɗan Ibro ya yi matuƙar fice a finafinan Kannywood da aka fi sani da Camama, ko da yake ya yi finafinai a ɓangaren Santimental daga bisani.
Sai dai kamar yadda Hausawa ke cewa, "Ba rabo da gwani ba, mai da kamar sa".
Tun bayan rasuwarsa, aka fara tunanin jarumin da zai iya maye babban gurbi da yake takawa wajen nishaɗantarwa da ƙoƙarin fito da tsagwaron gargajiyar Bahaushe da raya ta da isar da saƙo cikin salo mai sauƙi da kuma iya yanko magana irin na Ɗan Ibro.
"Kullum ji nake kamar yau Ibro ya rasu," in ji Daushe a lokacin da yake bayyana irin alaƙar da ke tsakaninsa da Marigayi Alhaji Rabilu Musa Ibro.
Alhaji Rabiu Ibrahim Daushe na cikin fitattun masu finafinan barkwanci da suka daɗe tare da Ibro, kuma ya bayyana wa BBC cewa a ganinsa, babu wanda zai maye gurbin da Ibro ya bari a Kannywood.

Asalin hoton, Daushe

Asalin hoton, Daushe
Wane irin giɓi ya bari?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi ma Sulaiman Bosho ya ce da su abokan marigayin, da ma masana'antar baki ɗaya har yanzu suna kewar fikirar da Allah ya yi wa Ibro.
"Ibro ne kaɗai yake iya abubuwan da yake yi," in ji Daushe a lokacin da yake amsa tambayar ko za a iya maye gurbin marigayin, inda ya ƙara da cewa da wuya a sake samun kamar marigayin.
"Saboda na san ba za a maye gurbinsa ba, shi ya sa na mayar da hankalina kan abu biyu. Na farko jiɓintar lamarin iyalansa saboda soyayya da zumuncin da ke tsakaninmu. Kuma har yanzu ƴaƴansa "Baba" suke kira na."
Daushe ya ƙara da cewa: "Kamar dai ni yanzu, misali akwai abubuwan da ni kaɗai na iya, haka idan ka ɗauko Bosho, akwai abubuwan da shi kaɗai ne zai yi maka su. Wasan kwaikwayo, baiwa ce da Allah ke bai wa mutum.
"Ibro ne zai maka ihu, ya yi kururuwa ka ji kamar da gaske. Haka yake kuka kamar da gaske - kai ka ce mutuwa aka yi masa. Ba ya wasa a fim, har duka da gaske yake yi, Yakan ce; shi ba wasa yake yi ba. Gaskiya ba za a maye gurbinsa ba."
Shi ma Sulaiman Bosho ya amince da irin bayanin Daushe, inda ya ce "idan ina wasa, mutane da dama suna kallo na, sai su tuna da shi, har su yi masa addu'a."
Rabi'u Daushe ya ce ko rikice-rikicen da suke ta ƙaruwa a Kannywood ma suna da alaƙa da rashin Ibro.
A cewarsa, "Tun da Ibro ya rasu, ban san wani shahararre ko mai riƙe da wani muƙami a wannan masana’antar da ke ware lokaci, yana sanyawa a yi wa Kannywood addu’a domin ganin ci gabanta ba."

Asalin hoton, Hannafi Ibro
'Kama da wane, ba ta wane'

Asalin hoton, Muhsin Ibrahim/Facebook
BBC ta tuntuɓi masana harkokin Kannywood domin jin ko akwai giɓin da marigayin ya bari, da kuma ko an yi nasarar mayewa, inda suka bayyana cewa kama da wane, ba ta wane.
Malam Ibrahim Sheme ya ce: "zan iya cewa ba a samu makwafinsa cif-da-cif ba. Da ma ka san Hausawa na cewa ba a maimaita gwani.
"Ko lokacin da yake wasa, akwai wasu da suke bakin ƙoƙarinsu, amma in dai a wannan fagen ne, babu kamarsa. To kuma da Allah ya masa rasuwa, akwai waɗanda suka ci gaba. Akwai ɗansa ma da ya gaje shi yana wasan barkwanci, amma Ibro daban ne."
Sheme ya ƙara da cewa babu yadda za a samu wani ɗan wasan Hausa da ke yin daidai da Ɗan Ibro.
A nasa bayanin, Dokta Muhsin Ibrahim, malami a Jami'ar Cologne da ke Jamus, ya ce ai shi Ibro daban ne.
"Idan aka ce ba za a samu irinsa ba, ba ana nufin ba za a samu wanda zai riƙa yin wasan barkwanci yana ba da dariya ba, a'a, ana nufin ba za a samu wanda zai riƙa yin irin abin da yake yi, kuma yake ba da dariya kamar Ibro ba.
"Kusan za a iya cewa baiwa ce domin bincike ya nuna cewa ba za ka ce ga wani mutum da Ibro ya taso yana kwaikwaya ba."
"Ya taso ne kawai yana yin wasanninsa, wasu suka zo suna kwaikwayonsa. Kuma ko an kwaikwaye shi, ai kama da wane ba ta wane," in ji shi.
Muhsin ya ƙara da cewa shi Ibro ko kallonsa kawai ka yi, "ko bai ce komai ba, zai ba ka dariya."
Halin da muke ciki bayan shekara 10 - Iyalan Ibro

Asalin hoton, Hannafi Ibro
BBC ta tuntuɓi Hannafi Rabilu Musa Ibro, wanda ɗa ne ga marigayin, kuma jarumin barkwanci a masana'antar Kannywood game da yadda rayuwa ta kasance musu, shekara goma bayan rasuwar mahaifinsu.
"Ai kowa ya rasa mahaifi, dole zai shiga yanayi maras daɗi saboda mun rasa bango babba. Kuma tun bayan rasuwarsa, gaskiya rayuwa ba daɗi, sai dai mu ce Alhamdulillah kawai."
"Sannan akwai abubuwan da yake yawan yi mana a gida a matsayinmu na ƴaƴansa, da mun tuna, ko mun ga irin wuraren da yake zama ko yin wasu harkoki, dole mu tuna da shi."
A game da alaƙar iyalan marigayin da Kannywood, Hannafi Ibro ya ce wasu sun manta da su baki ɗaya.
"Alaƙar mahaifinmu da Kannywood da jarumanta mai kyau ce lokacin da yake raye, amma wasu sun watsar da ita, wasu kuma suna nan muna ci gaba da zumunci sosai.
Ya ce ya shiga fim ne saboda shi ɗan gado ne, "kuma saboda yadda na ga har yanzu idan aka ga mahaifinmu, ana yi masa addu'a. Wannan ya nuna cewa abin kirki ya yi."

Asalin hoton, Hannafi Ibro












