Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasar da mata suka fi mutuwa lokacin haihuwa a duniya
- Marubuci, Makuochi Okafor
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa health correspondent, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 7
A matsayinta ta ƴar shekara 24, Nafisa Salahu ta shiga cikin matsanancin hali inda ta zama ɗaya daga cikin alƙalumman da ake lissafawa, a ƙasar da mace ke mutuwa a duk minti bakwai a yayin haihuwa.
Idan naƙuda ta kama mai haihuwa lokacin da ake tsaka da yajin aikin likitoci, duk da kasancewar ki a asibiti, babu wani ƙwararre da zai taimaka idan kika shiga hali mai tsanani.
Kan jinjirinta ya maƙale a lokaci haihuwa. Abin da kawai aka gaya mata shi ne ta kwanta ta jira, haka ta yi har tsawon kwana uku.
Daga ƙarshe aka ce dole sai an yi mata aiki an cire jinjijrin, aka tsara likitan da zai yi aikin.
"Na gode ma Allah saboda na kusa rasa raina. Ban da wani sauran kuzari, kuma ba ni da komai da ya rage min," kamar yadda Salahu ta shaida wa BBC daga jihar Kano da ke arewacin ƙasar.
Ta rayu amma dai ta rasa jinjirinta.
Bayan shekara 11 ta sha komawa asibitin domin haihuwa, abin da ta ce ya zama sabo. "Na riga na san na shiga halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai , amma ba zan sake jin wata fargaba ba kuma," in ji ta.
Najeriya ce ƙasar da ta fi kowace haɗari a duniya ga mata masu haihuwa.
A cewar sabbin alƙaluman Majalisar Ɗinkin Duniya sun yi ƙiyasin cewa ita ce ƙasa mafi haɗari, da aka fitar daga 2023, ɗaya a cikin mace 100 na mutuwa a lokacin naƙuda a waɗannan ranaku.
A shekarar 2023 Najeriya ce ke da kashi 29 cikin ɗari na adadin mata masu mutuwa a lokacin naƙuda a faɗin duniya.
Wannan adadin ya kai mata 75,000 da ke mutuwa a shekara, wanda ke gwada cewa a duk minti bakwai mace ɗaya na mutuwa.
Gargaɗi: Wannan labari na ƙunshe da hoto mai nuna yadda ake haihuwar jinjiri.
Abin da ke damun wasu da dama shi ne yawan mutuwar da ake samu - sanadiyyar abubuwa irin zubar jini bayan haihuwa - ba a iya hana afkuwar su.
Chinenye Nweze mai shekara 36 ta zubar da jini sosai da ya yi sanadiyyar rasa ranta a wata asibiti da ke garin Onitsa a kudu maso gabashin Najeriya, kimanin shekaru biyar da suka gabata.
"Likitoci na buƙatar jini," kamar yadda ɗan'uwanta Henry Edeh ya tuna. "Jinin da ake da shi a lokacin bai wadatar ba, suna ta kai komo. Rashin 'yar'uwata - zafin da na ji ko maƙiyina ban yi wa fatan jin sa."
Wasu daga cikin abubuwan da suka fi haddasa mutuwar mata a wurin haihuwa sun haɗa da ɗaukar tsawon lokaci ana naƙuda da hawan jini da zubar da ciki ba kan ƙa'ida ba.
Yawan mutuwar mata a yayin haihuwa da ya yi "tsanani" a Najeriya na da nasaba da abubuwa da dama a cewar Martin Dohlsten, jami'in Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya wato Unicef.
Daga cikin su a cewar sa akwai rashin tsarin kiyon lafiya mai ingancin, da ƙarancin magunguna, da tsadar aikin wanda ba kowa ne ke da ƙarfin biya ba, da yadda wasu ke saka al'adu da kuma rashin tsaro.
"Babu daɗi mace ta mutu a lokacin naƙuda" in ji Mabel Onwuemena, jami'ar gudanarwa na wata gidauniya mai bayyana ci gaban mata.
Ta bayyana cewa wasu mata musamman a yankunan karkara, sun yi imanin "cewa zuwa asibiti ɓata lokaci ne" sai suka zaɓi "yin amfani da hanyoyi magungunan gargajiya a maimaikon neman taimakon likita, wanda ɗaukar wannan mataki da suke yi na haifar da cikas.
Ga wasu, zuwa asibiti ma wani abu ne da ba zai yuwuwa - saboda babu hanyoyin sufuri, amma Onwuemena ta yi amanna cewa ko da mace ta gwada tafiya a haka, matsalolinsu ba za su ƙare ba.
"Galibin asibitoci ba su da wadatattun kayan da ƙwararrun likitoci da ma'aikata, hakan ya sa abu ne mawuyaci maras lafiya ya samu kulawar da ta dace."
Gwamnatin Najeriya a yanzu na ware kashi 5 cikin ɗari na kasafin kuɗinta a fannin lafiya - abin da bai kai kashi 15 cikin ɗari ba da aka aka nemi ƙasar ta ware a lokacin yarjejeniyar Ƙungiyar Ƙasashen Afirka ta shekarar 2001.
A shekarar 2001 akwai ungozoma 121,000 ga yawan jama'a miliyan 218 kuma ƙasa da rabin dukan haihuwar da ake yi ƙwararren jami'an kiyon lafiya ne ke kula da su.
An yi ƙiyasin cewa ƙasar na buƙatar ƙarin malaman jinya da ungozoma 700,000 domin cimma adadin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta buƙata.
Haka kuma akwai matuƙar ƙarancin likitoci.
Ƙarancin ma'aikata da kayan aiki ya sa ana tsananin buƙatar taimakon ƙwararru.
"A gaskiya ban cika yarda da asibiti ba, akwai labarai da dama da ke nuna irin sakacin da ake samu musamma a asibitocin gwamnati," in ji Jamila Ishaq.
"Misali, lokacin da zan yi haihuwa ta huɗu na gamu da matsala a yayin naƙuda. Ungozoma da ke gida ta ba mu shawarar mu je asibiti, amma da muka je babu wani jami'in kiyon lafiya da muka tarar da zai iya ba ni kulawa. A kan tilas muka koma gida inda a can na haihu," a cewar ta.
Jamila 'yar shekara 26 da ta fito daga jihar Kano na sa ran haihuwa karo na biyar.
Ta ƙara da cewa ta gwammace zuwa asibiti mai zaman kanta amma kuma tsadar ta yi yawa.
Ita kuma Chinwendu Obiejesi, tana sa ran haihuwa karo na uku, tana da ƙarfin zuwa asibiti mai zaman kanta, "ai ba ni da buƙatar zuwa in haihu a wata asibiti daban".
Ta ce a yanzu an samu raguwar mace-macen mata tsakanin ƙawayenta da iyalai, inda sai wanda ba a rasa.
Tana zaune ne birnin Abuja, inda ake samun asibitoci a sauƙaƙe, inda ake da hanyoyin mota masu kyau, kuma hanyoyin agajin gaggawa na aiki. Kuma mafi yawan mata da ke zaune a birane na da ilmi sun kuma san muhimancin zuwa asibiti.
"Nakan je awon ciki akai-akai...nakan samu damar tattaunawa da likitoci yadda ya kamata, tare da yin gwaje-gwaje da suka kamata domin tabbatar da lafiyata da ta jinjirina," kamar yadda Misis Obiejesi ta shaida wa BBC.
"Alal misali lokacin da na samu cikin yarona na biyu, sun yi tsammanin zan zubar da jini da yawa, kan haka suka yi tanadin isasshen jini ko da za a buƙaci yi min ƙarin jini. Na gode Allah ban buƙaci haka ba, komai ya tafi yadda ya kamata."
Har ila yau, wata ƙawarta ba ta yi nasara ba.
A lokacin haihuwar ɗanta na biyu, "mai karɓar haihuwa ta kasa taimakawa a haifi jinjirin, sai ma ta nemi in yunƙura da ƙarfi, abin da ya sa jinjirin ya mutu." Daga lokacin da aka garzaya da ita asibiti an riga an makara. Dole aka yi mata aiki domin a cire gawar jaririn. Labarin ba shi da daɗin ji.
Dakta Nana Sandah-Abubakar, ita ce daraktar a Hukumar Kula da Lafiya a Matakin Farko ta Najeriya (NPHCDA), ta amince cewa yanayin na da muni amma ta ce akwai sabbin tsare-tsaren da aka soma amfani da su domin maganace wasu matsalolin.
A watan Nuwaman da ya gabata gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da wani sabon shiri a matakin farko da ya shafi Rage Mutuwar Mata a wurin haihuwa. Shirin zai karaɗe jihohi 33 na faɗin ƙasar, wanda zai magance mutuwar fiye da rabin mace-macen na mata a Najeriya.
"Mukan tantance duk mace mai juna biyu mu gano inda ta ke zama, mu taimaka mata daga farkon cikin har zuwa haife shi" in ji Dakta Sandah-Abubakar."
Tuni dai aka gano mata masu juna biyu 400,000 a jihohi shida a wani binciken gida-gida da muka gudanar, "tare da cikakkun bayanansu idan suna zuwa awo da ma waɗanda ba su zuwa."
"Manufar shirin dai ita ce wayar da kansu da haɗa su da cibiyoyin kiyon lafiyar, kuma sukan haihu lafiya."
Shirin na da manufar yin aiki da ƙungiyoyin sufuri domin su yi aiki tare wajen jigilar matan zuwa asibitoci da kuma ƙarfafa gwiwar mutane domin su yi rajista ƙarƙashin inshorar lafiya mai sauƙin kuɗi.
A yanzu dai ya yi wuri a ce wannan tsarin zai yi wani tasiri, amma dai hukumomi na fatan ƙasar za ta bi turbar da sauran ƙasashen duniya ke kai.
Tun daga shekarar 2000 an samu raguwar mace-macen mata da kashi 40 cikin ɗari a ƙasashen duniya da dama, wannan abin a yaba ne da ci gaban da aka samu a ɓangaren kiwon lafiya. A Najeriya ma an ɗan samu ingantuwar haka a daidai wannan lokaci - amma da kashi 13 cikin ɗari kawai.
Baya ga wannan shirin da aka yi wa take da Mamii, an fara gwada wasu shirye-shirye, wasu ƙwararru sun yi imanin cewa dole a yi wani tartibin abu - ciki har da saka jari a ɓangaren.
"Nasarar hakan ta danganta da samar da tallafin kuɗi mai ɗorewa, da aiwatar da shirin yadda ya dace tare da ci gaba da sanya ido domin tabbatar da an samu sakamakon da ya dace," in Mista Dohlsten na asusun Unicef.
Haka kuma, rasa kowace uwa a Najeriya - 200 a kowace rana - zai ci gaba da zama abin baƙin ciki ga duk iyalai da hakan ta shafa.
Amma ga Mista Edeh, har yanzu tana jin baƙin cikin rasa 'yar'uwarta.
"Muna kallon ta matsayin abar koyi kuma ƙashin bayan ci gabanmu saboda iyayenmu sun rasu lokacin da muke tasowa," in ji shi.
"Idan ina ni kaɗai da na tuna da ita nakan yi kuka har in gaji."