Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mene ne asali da hikimar yi wa jarirai aski?
- Marubuci, Abdullahi Bello Diginza
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 6
Hausawa da wasu ƙabilun Najeriya kan aske jariransu (maza da mata) a kwanakin farko na haihuwarsu, kamar yadda ala'dunsu suka tanadar.
Yayin da a wasu ƙabilun kuwa ake ganin saɓanin hakan, inda suke barinsu gashinsu har girma idan mata ne, in kuwa maza ne sai bayan watanni, ko ma shekaru.
Mutane da ama sun jima suna mauhara kan wanne ya fi tsakanin yin askin da rashinsa ga jaririn.
Addini da al'ada da kuma likitanci na daga cikin hujjojin da muke ke gabatarwa.
Ko wanne ne ya fi amfani a mahangar addini da kiwon lafiya?
Za mu yi ƙoƙarin amsa wannan tambaya da ma sauran tambayoyin da suka jiɓanci wannan a mahangar al'adu da addini da kuma kiwon lafiya.
Yaushe aka fara yi wa jarirai aski?
Sheikh Halliru Maraya Malamin Addinin Musulunci kuma mamba a kwamitin aikin Hajji na jihar Kaduna da ke Najeriya ya ce askin jarira ya samo asali ne daga addinin Musulunci.
''Sunna ce da Manzon Allah (S.A.W) ya assasa fa ɗasarsa cikin hadisin Samra ibn Jundub - wanda ibn Dawud da ibn Majah da Tirmizi suka ruwaito - Manzon Allah ya ce idan abin haihuwarku (Jariri) ya kai kwana bakwai to ku yi masa aski''.
''To wannan shi ne asalin yi wa jariri aski a musulunce'', in ji malamin addinin.
Amma a al'adance yana da matuƙar wahala a iya fayyace lokacin da Bahaushe ya fara yi wa jaririnsa aski, kamar yadda masana al'ada suka bayyana.
Farfesa Aliyu Muhammad Dan Bunza ƙwararren masanin al'ada kuma malami a Jami'ar Usmanu Danfodio da ke Sokoto, ya ce babu haƙiƙanin lokaci ko ranar da Bahaushe ya fara yi wa jaririnsa aski.
''Sanin ranar da aka fara yi wa Bahaushe aski na da wuya, saboda kusan duka ƙabilun baƙaken fata suna yi wa jariransu aski'', in ji shi.
Haka Farfesa Maryam Mansur Yola, ƙwararriya a fannin aladun Hausawa, kuma malama a Jami'ar Bayero da ke Kano, ta ce duk da cewa ba a san haƙiƙanin lokacin da Bahaushe ya fara yi wa jariransu aski, ana kyautata zaton cewa an fara ne tun zamanin addinin gargajiya.
''Tun kafin zuwan addinin musulunci, lokacin da Bahaushe ke bautar iskokai'', in ji malamar jami'ar.
Farfesa Bunza ya ce abin da ya sa a ba za a iya tantance lokacin da Bahaushe ya fara yi wa jariransa aski ba shi ne rashin rubutaccen bayanin tarihi game da hakan.
''Duk rubutun da ake da shi kan tarihin aski bai wuce shekara 200'', a cewar malamin Jami'ar.
Amma a mahangar Addinin Musulunci da galibin Hausawa ke bi ....
Me ya sa ake yi wa jarirai aski?
Farfesa Maryam Mansur Yola ta ce abin da ya sa Hausawa ke yi wa jariransu aski bai rasa nasaba da nemar masa kariya da waraka daga cutukan jarirai.
''Ana yi wa jarirai aski ne saboda magani, daga cututtukan da suke damun jarirai kamar ciwon kai da makamantansu'', in ji ta.
Shi ma Farfesa Bunza ya jaddada wannan zance yana mai cewa Bahause ya yi imanin cewa gashin da jariri ya zo duniya da shi, ya tsira ne a mahaifa, don haka yana iya tahowa da wata cuta da za ta yi wa yaro tasiri a duniya.
''A ganin Bahaushe wancan gashin cikin mahaira ya tsira don haka dole a aske shi na duniya kuma ya tsira, don wancan na iya tahowa da wata cuta da ba a san makarinta ba, ko iskokai ko wata cuta'', in ji ƙwararren masanin al'adun Hausawan.
Amma a fuskar addini, Sheikh Maraya ya ce akwai binciken addini da ya tabbatar da cewa askin na ƙara wa fatar kan jariri ƙarfi da raba kan jariri da wasu ƙwayoyin cutukan da za su iya cutar da jariri.
''Wannan dalili ne ya a wasu malamai suka ce abin da ya sa Annabi ya yi umarnin aske masa gashin a kwana bakwai'', in ji malamin addinin.
Yaushe ya kamata a aske jariri?
Sheikh Halliru Maraya ya ce a ƙa'idar musulunci, Manzon Allah, (S.A.W) ya ce idan jaririnku ya kai kwana bakwai ku yi masa aski.
''Wannan ya nuna kenan a musulunci ana yi wa jariri aski bayan ya cika kwana bakwai a duniya'', in ji shi.
Haka ma ta fuskar al'ada akan yi wa jariri aski ne a ranar kwana bakwai, wato ranar suna, kamar yadda Farfesa Bunza ya bayyana.
''Akan yi wa jariri aski ranar bakai, idan wani dalili ya hana, akan bari sai mako ya zagayo, kenan mako biyu'', in ji shi.
Ya ake da sumar jariri bayan askin?
Sheikh Maraya ya ce a addinance idan an yi wa jariri aski akan auna gashinsa sai a bayar da sadakar kuɗin da suke daidai da nauyin gashin.
''Idan aka aske jariri za a auna gashinsa a sikile, sai a bayar da sadakar daidai da nauyin dinare na wannan sikeli, amma kuma fa wannan mustahabbi ne ba wajibi ba'', in ji shi.
Amma a mahangar al'ada akan ƙulle gashin jaririn a bai wa mahaifiyarsa ta ajiye masa har sai ya girma, ko kuma a ƙona shi domin yi masa maganin wata lalura.
Farfesa Maryam Mansur Yola ta ce akan mulmule sumar a ajiyeta har zuwa wani lokaci domin yi wa yaron maganin wasu lalurori da za su taso masa.
''Idan an yi askin ba zubar da sumar za a yi ba, cureta za a yi a ajiyeta, ko a ƙonata a ajiye tokar sai ya kai shekara bakwai idan za a yi masa kaciya a ɗauko domin yi masa magani'', in ji malamar jami'ar.
Shi kuwa Farfesa Bunza cewa ya yi wasu kan ajiye sumar har yaron ya girma a ba shi ita domin ya ajiye da kansa.
''Wani har ya tsufa yana ajiye da sumar, wani ma raba wa ƴaƴansa da jikokinsa ita zai yi ya faɗa musu sunan wanzamin da ya yi masa askin da garin da aka haife shi, domin su ajiye a matsayin tarihi'', in ji masanin al'adun Hausawan.
Amfanin aske jarirai
Dokta Lawal Musa Tahir, likitan yara a wani asibitin Abuja da ke Najeriya ya ce a likitance babu wata hujja da ta tabbatar da amfanin askin da ake yi wa jarirai.
''Sai dai wasu mutane kan ce in an aske kan yaron wani gashin mai kyau zai fito, wasu kuma kan ce saboda jaririn ya samu iska sosai, amma a likitance babu wata takamammiyar hujjar likitanci'', in ji shi.
Farfesa Bunza ya ce wani dalilin da ya sa Bahausehe ke yi wa jariri aski shi ne kare shi daga sanyi.
''Galibi idan za a yi wa jariri aski, akan yi masa ne da ruwan ɗumi, kuma wannan ruwan ɗumin ba ya jimawa zai koma mai sanyi, to idan ba a yi masa aski ba, ruwan zai riƙa tsayawa a gashinsa, daga baya ya riƙa zubo masa a jikinsa ko shiga fatarsa, kuma hakan zai iya kwawo masa mura'', in ji shi.
Wani dalilin da ya sa Bahaushe ke yi wa jaririnsa aski shi ne lura da maɗigarsa.
''Ta dalilin askin ne za a iya lura da maɗigar domin sanin irin maganin da za a yi mata'', in ji shi.
Ita ma Farfesa Maryam Yola ta ce ta hanyar asikin ne ake gane idan jariri yana da matsalar maɗiga.
Hama ƙwararriyar a fannin al'adun Hausawa ta ce aske gashin jariri kan taimaka masa wajen kare shi daga rama.
''Bahaushe ya yi imanin cewa gashi kan sa mutum rama idan ya yi yawa, don haka ne ake yi wa jariri aski ba a barinsa da suma, saboda hana shi ƙiba, tare da sanya shi ramewa'', in ji ta.
Da me ya kamata a yi askin?
Dokta Lawal Musa Tahir ya ce idan har za a yi wa jariri aski yana da kyau a yi masa da kayan aiki mai tsafta, wana ba zai cutar da jaririn ba.
''Idan za a yi a nemi kayan aiki mai tsafta da inganci wajen yi wa jariri aski don kare shi aga kamuwa da cutan da ake ɗauka ta hanyar aski'', in likitan.