Me ya sa ake haihuwar jarirai da tawaya?

    • Marubuci, Aisha Babangida
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa, Abuja

"Da yake an haife shi da tawaya ne, har yanzu maganarsa ba ta fita, idan ba shi da lafiya ko baya jin daɗi, zai yi ta kuka ba tsayawa, idan zai yi fitsari ko kashi, sai dai yayi a jiki, kullum sai na yi aikin kashinsa, sauran yara na gudunsa da ƙyamarsa saboda yawun da ke fita daga bakinsa."

Waɗannan kalaman wata mata ce da ke renon yaron da aka haifa da tawaya.

Hukumar lafiya ta duniya ta ce kimanin jarirai 240,000 ne ke mutuwa a duniya a cikin kwanaki 28 da haihuwa a kowace shekara saboda an haifo su da tawaya ko nakasa.

Hukumar ta ce tawaya na haifar da ƙarin mutuwar yara 170 000 tsakanin watanni 1 zuwa shekaru 5 kuma tara daga cikin yara goma da aka haifa tare da tawaya suna cikin ƙasashe masu matsakaicin ƙarfi..

Dakta Lawal Musa Tahir, likitan yara ne a asibitin Nizamiye de ke Abuja, kuma ya ce tawaya tana nufin a haifi jariri ba tare da ya samu cikkakiyar halitta ba, ya zama wani gaɓar jikin sa bai sami cikakkiyar halitta ba wanda kuma zai iya shafan harda ƙwaƙwalwa da hankali har ma da tunani.

Likitan ya ƙara da cewa tawaya ko nakasa na iya kasancewa na dogon lokaci, wanda ke yin tasiri sosai ga ɗaiɗaikun mutane da kuma iyalai kamar yadda Asabe waziri ta shaida wa BBC irin ƙalubalen da take fuskanta wajen renon yaron da ke da tawaya ko nakasa.

Ta ce ba ita ta haifi yaron ba, inda ta ce uwar da ta haifi yaron ƴar wata makwaciyarta ce kuma ta so zubar da cikin lokacin da ta gano tana da juna biyu.

Asabe ta ce uwar ta ɗauki cikin ne ba ta da aure, tsoron iyayenta da gudun maganganun mutane ne ya saka ta nemi hanyar da za ta zubar da cikin inda ta sami wata ƙawarta da ta ba ta shawarar siyan wasu magungunar zubar da cikin.

"Uwar da kanta take faɗa min cewa ita da wata ƙawarta suka je suka siya magungunan zubar da cikin, wanda ta ɗauki kwana uku tana sha, amma cikin ya ƙi zubewa."

"Uwar ta ce da ta ga cikin ya ƙi zubewa kuma kafin iyayenta su gano ta, sai ta sake komawa ta nemi wani maganin mai ƙarfi, amma duk da hakan, cikin bai zube ba, daga baya dai iyayenta suka gano, a lokacin kuma cikin ya riga ya yi wata 6."

"Ganin hakan ne, iyayen suka ce toh ta san yadda za ta yi da cikin, karda ta sake ta kawo musu wani ɗa, saboda su ma wahala suke sha, ba kuɗi, cin abinci wahala, a yadda take ba ni labarin."

"Toh ni kuma, ina ganin haka kuma ni ba yara ne da ni ba kuma miji na ya rasu, shine kawai na ce idan ta haihu, zan karɓi jaririn na rene shi."

Asabe ta ce ko da uwar ta haifo yaron, gaba ɗaya sai a hankali, hannunsa a lanƙwashe, ƙafafunsa a lanƙwashe, bakinsa a karkace, a haka ta ce ta ansa jaririn.

"Uwar na haifar yaron suka bar garin, suka koma garinsu da ke Kaduna, yau shekara 5 kenan, ni ke renon yaron."

"Na canza masa makaranta sau huɗu kenan, duk makarantar da na saka shi, ba ya daɗewa, ko dai masu lura da shi su ce ya cika kashi da fitsari a jiki, kuma yana ɓata jikin sauran yaran, sai masu cewa kukansa yana hana sauran yaran karatu." in ji ta.

"Abinci wata sa'in sai dai na ɗura masa, bai da wani aboki saboda yara suna ƙyamarsa da zolayarsa."

"Idan ya fara kukan nan nasa, ba na iya rarrashinsa sai dai idan ya gaji ya bari, da dare idan ya so, ya ƙi kwanciya, har ma makwabta na cewa yana da na ɓoye ne," Asabe ta ƙara da cewa.

Asabe ta ce a lokacin da aka haifi yaron, ta kai shi asibiti domin ta gano ko za a iya masa magani, amma ta ce a nan ne likitan ya tambayeta ko ita ta haifi yaron, sai ta ba shi labarin yadda abun ya faru, shine likitan ya ce mata yaron ya fito a haka ne ta sanadiyyar magungunan da mahaifiyar shi ta sha domin zubar da cikin.

Waɗanne abubuwa ke haddasa tawaya a jarirai

Dakta Lawal ya ce abubuwan da ke kawo tawaya a jarirai sun kasu kashi-kashi.

Likitan ya ce akwai abun da ya shafi ƙwayoyin halitta wanda ake gado da su wato gene kenan da chromosomes waɗanda ke iya sa cututtuka daban-daban da ake haihuwar jarirai da su kamar irin su 'down syndrome'.

"Ana kuma iya samun tawaya saboda muhalli kamar irin wuaren da ke da sinadarai masu gurɓata muhalli kuma mace mai juna biyu tana zama a irin wurin nan."

"Sai kuma idan ya kasance mahaifiya tana da matsalar rashin sinadarai masu inganci na abinci kafin ta sami juna biyu ko kuma farkon juna biyunta har zuwa kusan mako takwas, wannan yana iya haddasa haihuwar jariri da tawaya.

"Idan kuma mahaifiya ta kasance tana amfani da magunguna masu ƙarfi na sha ko na shafawa, na asibiti ko na gargajiya, waɗannan suna iya zama sun shafi jariri."

Waɗanne ire-iren tawaya ake da su?

Dakta Lawal ya shaida wa BBC cewa tawaya na iya shafear kusan kowanne ɓangare na jikin jariri.

Likitan ya ce ana iya haifar jariri da ƙaton kai ko da ɗan ƙaramin kai ko kuma a haife shi da matsala a idanunsa ko a sami matsala da ta shafi hanci ko kuma ya zama dasashinsa ya ɓarke.

"Wannan tawayar na iya shafar laɓɓa ma, ana iya samun su zama sun ɓarke, ana kuma iya samun ɗan gajeran wuya ko mai faɗi."

"Ana kuma iya samun tawaya ta shafi zuciya, kuma tawaya na iya sa a haifi yaro da hanji a waje ko kuma a samu matsalar da ta shafi laka wato abin da ake kira da 'spina bifida'.

Likitan ya kuma ce ana iya haifar jariri da matsala a hannu ko ƙafa su zamo 'yan gajeru ko kuma a lanƙwashe.

Ya ƙara da cewa ana iya samun a gaban jaririn a samu matsala ko kuma matsala ta wajen dubara wanda zai iya shafar hankalin mutum da yanayin yadda yake abubuwa idan yana girma.

Dakta lawal ya ƙara da cewa magungunan zubar da ciki na yin tasiri wajen haifar jariri da tawaya ko naƙasa.

Ana iya gane jariri na ɗauke da tawaya tun a ciki?

Likitan ya ce idan aka je awo, ana iya gane cewar jaririn da ake ɗauke da shi yana da naƙasa, wanda ya ce shi ya sa musamman ake yin wani hoto na jariri domin a gane ko shin jaririn lafiyayye ne ko yana da wata matsala kafin a haife shi.

"Ga wadanda ba sa zuwa asibiti awo, gaskiya zai yi wahala a gane cewar jaririn na da nakasa saboda dai ba hoto aka yi ba ballantana a ga jaririn kuma a gane cewa yana da tawaya."

"Sannan idan ya kasance mahaifiya tana shan sigari ko giya ko kuma ƙwayoyi da suke sa maye, duka suna iya sa a haifi jariri da tawaya ko nakasa."

Dakta Lawal ya ƙara da cewa idan ya kasance mahaifiyar ta tsufa kuma ta sami juna biyu, shi ma yana ɗaya daga cikin abubuwan da ke kawo hatsarin haifar jariri da tawaya, amma kuma wannan ba ya faruwa sosai."

Za a iya kaucewa haihuwar jariri da tawaya?

Dakta Lawal ya ce akwai wasu abubuwa da idan aka guje musu, za a samu saukin hatsarin haihuwar yaro mai tawaya. Abubuwan kuwa su ne kamar haka:

  • Mace mai juna biyu ta guji shan taba da giya da kuma ƙwayoyin da ke sa maye.
  • Mace ta kasance kafin lokacin da za ta sami juna biyu, tana cin abinci mai sinadarai na gina jiki musamman sinadarin folic acid
  • Idan mace na da ciwon suga, ya kasance an ɗauki mataki yadda za a ce an shawo kan cutar kafin ta samu juna biyu.
  • Idan mace na da juna biyu, a duba sauran cutuka kamar su 'rubella' da kuma matakin da ya kamata a bi wajen magance su.
  • Mace ta guji shan magunguna barkatai musamman idan mace na da juna biyu ko ana tunanin za ta sami juna biyu da kuma guje wa magungunan zubar da ciki.
  • Mace ta gujewa shan ruwan da ba shi da inganci.
  • A dage da zuwa asibiti da wuri saboda a yi bincike a gane cewar jaririn da aka ɗauka na cikin ƙoshin lafiya.