Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda cutar murar jarirai ta 'Jaundice' ke illata rayuwa har mutuwa
- Marubuci, Nkechi Ogbonna
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Lagos
- Lokacin karatu: Minti 3
Duk da cewa Babatunde Fashola, wanda aka fi sani da Baba, ya kai shekara 22 har yanzu tsayinsa bai kai sentimita 70 ba, wato ƙata biyu da inchi 4.
Yana fama da cutar murar jarirai ne, wadda ta sa yake buƙatar kula ta musamman. Ba ya iya tafiya ko magana, kuma da bututu yake cin abinci.
Tun yana jariri iyayensa suka yi watsi da shi, amma shekara 10 da suka gabata, sai ya tsinci kansa a gidan lura da masu cutar murar jarirai da ke jihar Legas.
"Baba na da nauyin kilogiram 12, kuma yana cikin ƙoshin lafiya," in ji mai gidan, Nonye Nweke a zantawarta da BBC.
Ms Nweke da ma'aikanta suna aiki ne ba dare ba rana domin kula da masu fama da wannan lalura, wadda ta taɓa ƙwaƙwalwa.
Duk da cewa babu wata ƙididdiga a hukumance, cutar murar jarirai na cikin cututtukan ƙwaƙwalwa da suka fi illa a Najeriya. A shekarar 2017, wani farfesa a tsangayar kiwon lafiya ta jami'ar Legas ya ce mutum 700,000 suna fama da lalurar.
Farfesa Chinyere Ezeaka, wanda likitan yara ne a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Legas ya shaida wa BBC cewa sama da kashi na jarirai suna fuskantar shawarar jarirai.
Jarirai da dama suna warkewa cikin ƴan kwanaki, amma wasu lalurar suna ƙamari duk da cewa ana iya warkewa.
Sai dai a Najeriya, ba a cika samun sauƙi cikin sauƙi ba, wanda hakan ya sa ƙasar ke cikin ƙasashe biyar da suke fama da matsalolin ƙwaƙwalwa da rashin samun waraka daga shawarar jarirai, kamar yadda alƙaluma daga Hukumar Lafiya ta Duniya WHO suka nuna.
A ƙa'ida dole ne a yi maganin shawarar jariran a cikin kwana 10, "idan ba haka ba kuma ya jawo matsalar ƙwaƙwalwa ta dindindin har ya kai ga cutar murar jarirai," in ji Farfesa Ezeaka.
Ms Nweke - wadda ke da ƴa mai lalurar- ce ta assasa gidauniyar kula da masu cutar bayan fama da sha wajen jinyar ƴarta mai suna Zimuzo.
"Lokacin da na kai ta cibiyar kula da yara, sai suka ce in mayar da ita gida saboda iyayen sauran yaran za su iya cire ƴaƴansu."
Yanzu Zimuzo ta kai shekara 17, sannan gidauniyar Ms Nweke na kula da masu lalurar.
Ranar da BBC ta ziyarci gidan, ta ga yadda aka baza kayayyakin wasa da aka jera a ƙasa domin masu lalurar su yi wasa da nishaɗi.
Idan lokacin cin abincin rana yi, sai masu kula da yaran wajen cin abinci. Wasu suna amfani da bututu ne wajen cin abinci, wanda ake yi duk bayan awa biyu a gidan, sannan akwai mutane da sama da 100 da suke jira a karɓi yaransu masu lalurar.
Sai dai ta ce karɓar ƙarin yara zai yi wahala saboda za ta buƙaci ƙarin kuɗaɗen kula da su. Kula da kowane mai lalurar a cibiyar na buƙatar aƙalla $1,000 (£790) duk wata - wanda ba ƙaramin kuɗi a ƙasar da mafi ƙarancin albashinta kusan $540 a a shekara.
Ms Nweke ta ce ta ce ta ɗauko Zimuzo ne daga wani gidan marayu.
Sai dai bayan wasu watanni da ɗaukarta, sai ta lura ba ta ƙara girma kamar sauran yara. Da aka kai ta asibiti ne aka gano tana da lalurar.
Sai aka ce ta mayar da Zimuzo gidan marayun da ta ɗauko ta, ta ɗauko wata, amma ta ƙi.
"Wani likita ya faɗa min cewa ba za ta wuce shekara biyu a raye ba, amma ga shi har ta kai shekara 17."
Ta ce rashin wayar da kai da rashin kayan aiki na kawo tsaiko wajen ganowa da jinyar cutar.
Ba Ms Nweke kaɗai take irin wannan aikin na kula da yaran.
Gidauniyar The Oscar Project ta fara aiki a Legas a kwanakin baya.
"Muna taimakon asibitoci a matakan farko da manyan asibitoci da kayan aiki domin magance cutar shawarar jarirai," in ji Toyin Saraki.
Project Oscar da gudunmuwar gidauniyar Reckitt, na horar da ma'aikatan jinya 300 a Legas, inda suke sa ran za su horar da iyaye 10,000 a shekarar farko hanyoyin ganewa da kiyaye kamuwa da murar jarirai.
Gidauniyar Project Oscar, wadda aka assasa a Vietnam a shekarar 2019, ta taimaki aƙalla ƙananan yara 150,000 a ƙasar ta yankn Asia.
Mr Anderson mai shekara 22, ya ce burinsa hana yaransa faɗawa wannan lalurar.
Yana aiki tare da wasu domin gwada jariran da aka haifa domin gano ko suna ɗauke da shawarar jarirai, domin a yi magani cikin sauri.