Waiwaye: Kashe sojojin Najeriya da naɗin sabon kocin Super Eagles
Wannan maƙala ce da ke kawo muku muhimman batutuwan da suka faru a Najeriya cikin makon da muke bankwana da shi

Asalin hoton, Nigerian Police
A ranar Litinin ɗin mako ne rundunar ƴansandan Najeriya ta ce wani abin fashewa ya kashe mutum biyu a wata makarantar Islamiyya da ke Abuja babban birnin ƙasar.
Wata sanarwa da rundundar ta wallafa ta ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safiyar Litinin a ƙauyen Kuchibuyi da ke ƙaramar hukumar Bwari.
"Bayanan farko-farko sun nuna wasu mutum uku ne suka kai wa shugaban makarantar Tsangayar Sani Uthman Islamiyya Mallam Adamu Ashimu ziyara, kuma su ake zargi da kai bam ɗin," in ji sanarwar.
"Biyu daga cikin mutanen sun mutu a fashewar a farfajiyar makarantar, yayin da na ukun da kuma wata mata mai sayar da kayayyaki suka ji munanan raunika kuma suke samun kulawa a asibiti."
Sanarwar ta ƙara da cewa 'yansanda na tsare da Mallam Adamu, sannan kuma za ta bayyana abin da bincikenta ya gano.
Dakarun Najeriya sun kashe ƙasurgumin ɗanbindiga, Sani Rusu a Zamfara

Asalin hoton, Defence Headquarters Nigeria
A ranar Litinin ɗin ne kuma dakarun haɗin gwiwa na Operation Fansar Yamma da ke yaƙi da ƴan fashin daji a yankin arewa maso yammacin Najeriya suka sanar da tabbacin cewa sun hallaka wani ƙasurgumin ɗan fashin daji mai suna Sani Rusu.
Jami'in hulɗa da jama'a na dakarun, Laftana Kanal Abubakar Abdullahi ne ya tabbatar da lamarin.
Ya ce rundunar ta ce ta samu nasarar murƙushe shi ne yayin wani samame da suka kai ta ƙasa da sama zuwa matattarar ƴan bindiga da ke ƙauyen Bamamu a ƙaramar hukumar Tsafe cikin jihar Zamfara, inda suka kashe ƙarin wasu mutanen da kuma ƙwato tarin makamai.
EFCC ta kori ma'aikatanta 27 saboda 'zambatar' mutane

Asalin hoton, EFCC
A cikin makon ne kuma hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta ce ta kori ma'aikatanta 27 a shekarar 2024 saboda zargin aikata zamba da sauran laifuka.
Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa shugaban hukumar Ola Olukoyede ne ya amince da matakin.
"Duk wani zargi da aka yi wa wani ma'aikacin hukumar, sai an bincika shi, ciki har da na dala 400,000 da ake yi wa wani ma'aikaci da ba a gano shi ba zuwa yanzu," a cewar sanarwar.
Ya ƙara da cewa EFCC "na sane da ayyukan sojan gona da ɓata sunan da wasu ke yi da ta hanyar amfani da sunan shugaba [Olukoyede] domin zambatar manyan mutanen da ake zargi", wanda shi ma ake kan bincikawa.
'Iswap ta kashe sojojin Najeriya shida a jihar Borno'

Asalin hoton, AFP
A cikin makon dai an samu rahoton cewa mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Islamic State (IS) sun kashe sojojin Najeriya shida yayin wani hari da suka kai kan sansaninsu da ke jihar Borno a arewacin Najeriya, a cewar rahoton kamfanin labarai na AFP.
AFP ya ambato jami'an sojin Najeriya biyu na cewa maharan na ƙungiyar Islamic State West Africa Province (Iswap) sun far wa sansanin da ke Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa ranar Lahadi da tsakar dare.
Rahotonni sun ce sun cinna wa sansanin wuta tare da ababen hawan da ke cikinsa.
"An kashe mana sojoji shida a harin na Iswap da suka kai sansanin bayan zazzafar musayar wuta," kamar yadda ɗaya daga cikin jami'an ya faɗa wa AFP.
Ɗaya jami'in ya ce jirgin sojin sama da aka aika daga binrin Maiduguri, mai nisan kilomita 100, shi ne ya kori maharan.
Najeriya ta naɗa Éric Chelle kocin Super Eagles

Asalin hoton, Getty Images
A ranar Talata hukumar ƙwallon ƙafa ta Najeriya NFF ta naɗa tsohon kocin tawagar Mali, Éric Sékou Chelle, a matsayin kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Super Eagles.
Chelle mai shekara 47 ya jagoranci Mali har zuwa zagayen kwata fayinal a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 a Ivory Coast, kafin mai masaukin baƙi ta doke su.
NFF ta ce ta amince da naɗin nasa ne bayan kwamatinta na musamman ya bayar da shawarar yin hakan a ranar Talata.
"Kocin zai fara aiki nan take, kuma zai mayar da hankali wajen sama wa Najeriya nasara a wasannin neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026," in ji NFF cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Talata da dare.
Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi na Kano zuwa Kaduna

Asalin hoton, Nigeria Railway Corporation
A cikin makon dai bankin raya ƙasa na China ya bai wa Najeriya rancen dala miliyan 254.76 domin gina titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna.
Sanarwar da bankin ya fitar ta zo ne gabanin ziyarar ministan harkokin wajen China a Najeriya.
Minista Wang Yi ya kai ziyara Najeriya domin ganawa da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, da sauran manyan jami'an gwamnatin tarayya.
Aikin layin dogon mai tsawon kilomita 203, ana sa ran zai laƙume dala miliyan 973 amma ya dakata saboda ƙarancin kuɗi.
Hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yi kan rikicin masarautar Kano

Asalin hoton, Mai Katanga/Facebook
A ranar Juma'a kotun ɗaukaka ƙara da ke zama a Abuja, babban birnin Najeriya ta yanke hukunci kan ƙararrakin da aka ɗaukaka game da rikicin masarautar Kano a gabanta.
Rikicin ya shafi nadin Muhammadu Sanusi II a matsayin sarkin Kano na 16 da kuma soke masarautun Kano biyar da dokar masarautun Kano ta 2019 ta naɗa.
Hukuncin nata ya shafi hukunce-hukunce biyu ne da aka yanke a kotuna biyu da ke birnin Kano, wato Babbar kotun tarayya da ke Kano da kuma Babbar kotun jihar ta Kano.











