APC ta yi tattakin nuna goyon baya ga hukumar zaɓe a Abuja

...

Magoya bayan jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya sun gudanar da wani tattaki a birnin Abuja, wanda suka ce sun yi ne domin nuna goyon baya ga demokuradiyya.

Hakan na zuwa ne kwana guda bayan da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, mai hamayya, Atiku Abubakar ya jagoranci zanga-zangar rashin yarda da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Tattakin, wanda magoya bayan jam’iyyar APC ɗin suka shirya, sun ce sun yi ne domin nuna amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar wanda aka gudanar a watan Fabarairu.

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC, ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, inda zai gaji shugaba mai ci, Muhammadu Buhari, wanda ke kammala wa’adin shugabancinsa na biyu na shekara huɗu-huɗu.

Sai dai manyan jam’iyyun adawa, irin su PDP da LP sun nuna rashin amincewa da sakamakon, inda dukkaninsu suka sha alwashin ƙalubalantar sakamakon a kotu.

..
...

Ƙorafi kan ingancin zaɓe

Abin da ake ta rikici a kansa shi ne na'urar da aka gabatar domin karɓar sakamakon zaɓen wadda ake kira BVAS, wadda aka yi tsammanin za ta sauƙaka maguɗin zaɓen da ake yi a zaɓen Najeriya, ya kuma sanya zaɓen ya zama mai sahihanci.

Ƙorafe-ƙorafen da ake yi na cewa ma'aikatan hukumar sun gaza tura sakamakon zaɓen daga rumfunan zaɓensu zuwa rumbun tattara zaɓe na INEC, wanda hakan ya janyo ƙorafin cewa kamar da haɗin bakin hukumar domin a yi maguɗi.

Hukumar INEC ce suka fito da dokar cewa za su riƙa ɗaukar hoton sakamakon su aike da shi daga rumfunan zaɓe sama da 175,000 da ke faɗin ƙasar, bayan duka jam'iyyun sun sanya hannu kan amincewa da hakan.

Lokacin da suke ƙorafi a wani taron manema labarai na haɗin gwiwa tsakanin mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP da na LP sun yi zargin cewa ko dai an haɗa baki da INEC ta taimaka wa jam'iyya mai mulki ko kuma intanet ɗinsu ta katse.

...