Yadda rarrabuwar kan ƴan hamayya ta sa Tinubu nasara

.

Asalin hoton, AFP

Sabon zaɓaɓɓen Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ba lalle ya yi nasara a zaɓen da aka gudanar ba da a ce an yi shi ne a shekarar da ta gabata kafin rarrabuwar kai ta janyo samun ɓangarori uku a babbar jam'iyyar hamayya ta PDP.

Da jumullar ƙuri'un abokanan karawarsa - ɗaya ɗan Jam'iyyar PDP da wasu biyu tsofaffin ƴan jam'iyyar - suka samu ya wadatar jam'iyyar ta sake komawa kan mulki, saboda gaba ɗaya ƴan takarar sun samu kashi 60 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa.

Ɗan takarar PDP, Atiku Abubakar ya samu kashi 29 cikin 100 na ƙuri'un, Jam'iyyar Labour ta Peter Obi ta samu kashi 25 cikin 100 sannan Rabiu Musa Kwankwaso na NNPP ya samu kashi 6 cikin 100 yayin da sabon zaɓaɓɓen shugaban Najeriyar ya tashi da kashi 37 cikin 100.

Da zai fi yi wa dunƙulalliyar PDP sauƙi ta yi amfani da ƙorafe-ƙorafen masu zaɓe kan matsin tattalin arziki da rashin tsaro da kuma hauhawar farashin kaya da suka fuskanta a mulkin Shugaba Muhammadu Buhari mai barin-gado da kuma Jam'iyyar APC wajen samun nasara.

Tinubu ya taka rawa wajen gina APC kuma ana kallonsa a matsayin "ubangidan ƴan siyasa" - ya taimaka wajen ɗora Muhammadu Buhari a kan mulki tsawon shekara takwas.

Amma shekara guda lokaci ne mai tsawo a siyasa - kuma tsohon gwamnan Legas mai shekara 70, bisa taimakon jam'iyyarsa, ya samu sauƙin samun nasara.

...
...

Kwalliya ba ta biya kuɗin sabulu ba

An ayyana zaɓen shugaban ƙasar a matsayin mafi zafi a Najeriya tun zamanin mulkin sojoji a 1999.

Hakan ya faru ne saboda ɗan takara na uku ya kasance yana gogayya da manyan jam'iyyu. Tsawon shekara 20 da ta gabata, Najeriya ta kasance tana tafiya ne kan tsarin manyan jam'iyyu biyu a mataki na ƙasa.

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, PDP da Atiku Abubakar sun yi nasara a wasu jihohin Arewa amma sun sha kaye a hannun Peter Obi a Kudu
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Duk da cewa akwai wasu ƴan takara daga wasu jam'iyyun da ke neman shugabancin Najeriya a wannan lokaci, babu wanda ya ja hankali fiye da Peter Obi wanda matasa ke matuƙar marawa baya.

Shi ne wanda ya mara wa ɗan takarar shugaban ƙasa na PDP a 2019 baya - kuma tsohuwar jam'iyyarsa ta mulki Najeriya tsawon shekara 16 bayan mayar da ƙasar kan tafarkin dumukuraɗiyya.

A lokacin, jam'iyya ce da ta haɗa kan miliyoyin mutane a faɗin ƙasar duk da cewa ta fi ƙarfi a Kudanci, inda aka ba ta tabbacin ƙuri'u a kowane zaɓe.

Bayan da PDP ta sha kaye karo na biyu a babban zaɓen ƙasa a 2019 ƙarƙashin Atiku, ta bayyana ƙarara cewa tana buƙatar sake farfaɗo da kanta domin janyo hankalin miliyoyin matasa da suke jin an mayar da su saniyar-ware a siyasa.

Kuma suka fusata da ƴan siyasa da suke ganin su ke da hannu a rashin ci-gaban Najeriya.

Addini da ƙabilanci sun taka rawa wajen rarrabuwar kai a ƙasar tsakanin Musulmai da suka fi yawa a Arewa da Kiristoci a Kudu inda ake da ɗaruruwan ƙabilu.

Ƴan kudu da dama suna ganin kamar PDP ba ta mutunta biyayyar da suka yi mata ba bayan da ta buɗe ƙofar bayar da tikitin takarar shugabancin ƙasar ga ƴan takara daga ko ina a Najeriya.

Maimakon taƙaita damar ga ƴan takara daga kudu maso gabashi - yankin Najeriya da zuwa yanzu bai samar da shugaban ƙasa ba a wannan zamani.

Hakan ya bai wa Atiku, babban mai tallafa wa jam'iyyar da kuɗi kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Musulmi daga Arewa maso gabas, damar sake tsayawa takara.

Mista Obi, Kirista da ya fito daga kudu maso gabas wanda kuma ya taba zama gwamnan Anambra sau biyu, ya fice daga PDP ƴan kwanaki kafin zaɓen fitar-da-gwani.

Wasu gwamnonin Kudanci masu ƙarfin faɗa-a-ji sun ƙi goyon bayan Atiku a zaɓen - ana tunanin wasu a cikinsu suna tare da abokan hamayyarsa.

Rabiu Musa Kwankwaso, fitaccen ɗan siyasar Arewa a Kano, birni na biyu mafi girma a Najeriya ya fito ƙarƙashin NNPP domin gwada sa'arsa a neman shugabancin.

Kwankwaso wanda ya yi gwamnan Kano har sau biyu shi ma ya fice ne daga PDP gabanin zaɓen ya tafi jam'iyyar NNPP, kuma ya tsaya mata takarar.

Duk da cewa PDP a yanzu ta sake cin zaɓe a wasu jihohin Arewa da APC ta ci a 2019, ta tafka gagarumar rashin nasara a jihohin Kudanci da ta fi ƙarfi inda Mista Obi ya yi bajintar samun ruwan ƙuri'u.

Me ya sa aka samu rashin fitowar masu zaɓe?

Wannan ya yi wa APC daɗi wadda ta yi riƙo ga dabarar da ta yi mata aiki a baya - inda ta samu ƙuri'u a jihohinta da ke Arewa da jihohin kudu maso yamma.

Ta kuma samu taimakon matsalolin da aka samu a ranar zaɓe inda ma'aikatan zaɓe suka isa rumfunan kaɗa ƙuri'a a makare - a wasu wuraren sa'a uku da rabi ana shirye-shiryen rufe rumfunan zaɓe.

Wannan ya sa mutane da dama ba su iya jefa ƙuri'a ba.

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Peter Obi ya nemi ƙuri'un masu zaɓe da al'ummar kirista

Galibin masu yin zaɓe a karon farko da suka isa rumfunan zaɓe kafin wayewar gari ba su samu damar yin zaɓe ba saboda rashin isar kayan aiki da wuri.

"Na isa rumfar zaɓena da ƙarfe 8:00na safe amma har zuwa 11:00, ban ga kowa ba," kamar yadda wani da a karon farko yake yin zaɓe a wata rumfa da ke Airport Road a Abuja, babban birnin ƙasar, ya faɗa wa BBC bayan da ya samu ya jefa ƙuri'a.

A birnin Legas da ke Kudu maso yamma, inda galibin matasa masu ilimi ke goyon bayan Mista Obi, wakilan BBC sun gana da mutane da dama da suka isa wurin zaɓe da wuri.

Amma suka bar wajen bayan shafe sa'o'i suna jiran jami'an zaɓen da ba su bayyana ba.

A wasu rumfunan zaɓe inda ake da dubban masu zaɓe da suka yi rajista, ba a soma zaɓe ba har sai ƙarfe 1:00 na rana - sa'a ɗaya da rabi kafin rufe lokacin zaɓe.

Kuma duk da tsawaita lokacin zaɓen a wuraren, mutane da dama ba su samu damar jefa ƙuri'a ba saboda dare ya yi kuma jami'an tsaro sun bar wuraren.

A wasu cibiyoyin zaɓen a wuraren da ƴan hamayya suka fi ƙarfi, ba a ma yi zaɓe ba kwata-kwata.

Kuma an samu wuraren da aka yi satar akwatin zaɓe da tashin hankali da yi wa masu zaɓe barazana a jihohin ƴan hamayya da ke Kudu kamar Rivers da Legas da Delta.

Ƙungiyar da ta sa ido a zaɓen kamar Yiaga, ta ce kashi 10 kaɗai cikin 100 na rumfunan zaɓe a kudu maso gabas da kashi 29 cikin 100 a Kudu ne aka fara tantance masu zaɓe da jefa ƙuri'a da ƙarfe 9:30 na safe a ranar Asabar - sa'a guda bayan da aka buɗe rumfunan zaɓen.

Wasu rumfunan zaɓe kashi 63 cikin 100 a kudu maso yamma da kashi 42 cikin 100 na rumfunan zaɓe a arewa maso yamma, inda APC ta fi ƙarfi, sun soma zaɓe a lokacin.

Masu sa-ido a zaɓen daga NDI-IRI da Turai sun ce zaɓen bai zama sahihi ba.

A ƙarshe, yawan masu kaɗa ƙuri'a kashi 27 cikin 100 ne kawai Tinubu ya samu ƙuri'a miliyan 8.8 - ƙasa da kashi 10 na masu zaɓe miliyan 93 da aka yi wa rajista.

Rashin fitar mutane su kaɗa ƙuri'a bai zama wata matsala ba kamar matsalolin da aka fuskanta a ranar zaɓe.

Tana iya kasancewa yawan mutanen da ke da rajistar zaɓe ya yi yawa sosai - saboda ba a ɗora bayanan mutanen da suka mutu da waɗanda suka fice daga ƙasar ba.

An kuma bijiro da na'urar Bvas ne domin hana mutane yin zaɓe fiye da sau ɗaya.

Idan hakan ya yi aiki kuma aka samu wasu da sunayensu ya bayyana fiye da sau ɗaya a rajistar masu zaɓe, hakan na iya janyo raguwar mutane.

Wata matsalar kuma na iya zama ƙarancin takardun kuɗi da man fetur a wasu yankunan ƙasar da ya sa mutane da dama suka fuskanci matsalar yin bulaguro domin jefa ƙuri'a.

A jawabin da ya yi, Tinubu ya ce akwai kura-kurai a zaɓen amma ya ce "ba su taka kara sun karya ba kuma ba su kai yawan da za su shafi sakamakon zaɓen nan ba."

Hukumar zaɓe ta INEC ma ta bayyana irin wannan ra'ayin.

Kasada ta biya

Mutane da dama suna kallon Bola Tinubu a matsayin ƙwararre a fagen siyasa kuma kasancewar ya yi yaƙin neman shugabanci ƙarƙashin taken: "Emi lo kan", wato "lokacina ne" a harshen Yarabanci, ta yiwu ya daɗe yana shirya wa wannan lokaci.

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Magoya bayan Bola Tinubu sun fi yawa a Kudu maso Yamma da Arewa

An ƙirƙiri jam'iyyarsa ta APC daga Alliance for Democracy (AD), wadda ta kusan narkewa shekara ashirin da ta gabata a zamanin da Olusegun Obasanjo, yake shugabanci yake kuma jagorantar PDP.

Duk da haka Tinubu yaƙi shiga PDP kamar yadda sauran jihohi da gwamnoni suka yi a lokacin.

A maimakon haka, ya yi amfani da albarkatun jihar - cibiyar kasuwancin ƙasar inda ya zama gwamna daga 1999 zuwa 2007 domin gina magoya bayansa a kudu maso yamma.

Ya dage wajen farfaɗo da ƙaramar jam'iyyarsa har zuwa 2013 lokacin da ta haɗe da wasu jam'iyyu a Arewa aka samar da APC kuma nasarar da ta samu a yaƙin neman zaɓen 2015 ta sa Buhari ya hau kan mulki.

Karon farko ke nan da jam'iyyar hamayya ta doke shugaba mai-ci wanda hakan ya nuna wa Tinubu hanyar haure duk wani ƙalubalen zuwa ga kujerar shugabanci.

Duk da haka, Tinubu, Musulmi ɗan Kudu ya yi kasada a ƙudirinsa.

A maimakon ya zaɓi mai mara masa baya daga Kiristocin da ke Arewa , sai ya zaɓi Musulmi ɗan arewa.

Ba ya so ya raba kan galibin Musulmin arewa - duk da cewa ya fusata Kiristoci da ya tsayar da Musulmi a matsayin mataimakinsa.

Manyan abokan takarar Tinubu sun yi alƙawarin ƙalubalantar nasararsa, inda suka yi zargin jami'an INEC sun gaza ɗora sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe daga kwanfuta.

A yanzu PDP da Labour suna ɓangaren ƙin yarda da zaɓen inda tun da farko wakilansu suka fice daga zauren tattara sakamakon zaɓen.

Daga bisani kuma suka gudanar da taron manema labarai tare.

Wataƙila magoya bayansu na fatan da jam'iyyun sun ɗauki wannan matakin kafin zaɓen wato na zama karkashin inuwa ɗaya.