Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya rasu

A Nigerian governor

Asalin hoton, Rotimi Akeredolu/Facebook

Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo da ke kudancin Najeriya, ya rasu.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ce gwamnan ya rasu ne a ƙasar Jamus.

Ya rasu yana da shekara 67, bayan ya shafe lokaci yana fama da cutar kansar jini da ta mafitsara.

Rasuwar tasa na zuwa ne kimanin mako biyu, bayan ya rubuta wasikar tafiya jinya, inda ya miƙa ragamar mulkin jihar ga mataimakinsa, Lucky Aiyedatiwa.

Kafin sannan, an yi ta dambarwar siyasa a jihar Ondo, a kan yunƙurin tsige mataimakin gwamnan daga kujerarsa, amma daga bisani Shugaba Bola Tinubu ya shiga tsakani.

Gwamnan dai ya shafe kusan wata uku a ƙasar Jamus yana jinya, daga bisani ya koma Najeriya a watan Satumba.

Sama da wata biyu bayan komawar Rotimi Akeredolu daga tafiyar jinyarsa ta farko, ba a iya ganinsa a bainar jama'a ba.

Da ya koma ɗin kuma, ya aika wa majalisar dokokin jihar wasiƙa, inda ya sake neman ƙarin hutun jinya a ranar 15 ga watan Yuli.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yayin da rashin lafiyarsa ya tsananta, Gwamna Akeredolu ya fuskanci matsin lambar neman ya yi murabus ko ya miƙa harkokin mulki ga mataimakinsa, daga jam'iyyun adawa da 'yan fafutuka, kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada.

A watan Oktoba, majalisar dokokin jihar ta rubuta wa alƙalin alƙalan Ondo wasiƙa, inda ta sake neman ya kafa kwamitin da zai binciki Lucky Aiyedatiwa a kan zarge-zargen aikata ba daidai ba. Mataimakin gwamnan ya garzaya kotu inda ya fara ƙalubalantar ƙoƙarin raba shi da muƙaminsa.

Daga bisani dai, gwamnatin jihar Ondo ta fitar da sanarwa a kan rasuwar Rotimi Akeredolu, wanda ta ce ya tafi ya bar wagegen giɓi a zukatan al'umma.

Sanarwar wadda kwamishiniyar labaran jihar, Bamidele Ademola-Olateju ta fitar, ta tabbatar da cewa Aredolu ya mutu ne lokacin da yake jinya a ƙasar Jamus sanadin cutar kansar mafitsara da ya yi fama da ita tsawon lokaci.

“An aika wasiƙa ga Shugaba Bola Tinubu don sanar da shi a hukumance game da labari mai ɗaga hankali. Iyali da Gwamnatin Jihar Ondo na jinjinawa goyon bayansa ga Gwamna Akeredolu a lokacin rashin lafiyarsa.”

Sanarwar ta ce za a fitar da sanarwa nan gaba don jin ƙarin bayani game da shirye-shiryen yi masa jana'iza.

A Nigerian governor

Asalin hoton, Rotimi Akeredolu/Facebook

An zaɓi Akeredolu a matsayin gwamnan jihar Ondo a wa'adi na biyu a shekara ta 2020.

Ɗan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ya fara cin zaɓen gwamna a watan Nuwamban 2016.

An haifi Arakunrin Rotimi Odunayo Akeredolu ranar 21 ga watan Yulin 1956, kuma ya halarci makarantar Aquinas College Akure kafin ya tafi Jami'ar Obafemi Awolowo University da ke Ile Ife.

Ya riƙe muƙamin kwamishinan shari'a na jihar daga 1997 zuwa 1999.

A 1998 ya zama babban lauya mai lambar SAN a Najeriya, sanan ya riƙe shugabancin ƙungiyar lauyoyi ta ƙasar tsawon shekara biyu daga 2008.

Kafin mutuwarsa, ya kasance shugaban ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya, wadda ta ƙunshi gwamnoni daga jiha 17. Ya kuma jagoranci sauran takwarorinsa biyar a matsayin shugaban jihohin Kudu maso Yamma, inda suka yi ta fafutukar kawo sauye-sauye da dama, musamman a ɓangaren tsaro, daga ciki har da yunƙurin kafa rundunar tsaro na Amotekun.