Akeredelu, Jegede da Ajayi za su fafata a zaɓen gwamnan Jihar Ondo

Asalin hoton, FACEBOOK
Cikin kwana kwana uku masu zuwa, masu katin kaɗa ƙuri'a za su tafi rumfunan zaɓe a Jihar Ondo da ke Kudu Maso Yammacin Najeriya domin zaɓar gwamnan jiharsu.
Al'ummar Ondo ba su yi zaɓen gwamna ba lokacin da sauran jihohi suka kaɗa ƙuri'u a 2019 sakamakon wani hukuncin kotu a 2017.
A cewar hukumar zaɓe ta INEC, mutum 1,822,346 ne suka yi rijistar kaɗa ƙuri'a a zaɓen na ranar 10 ga watan Oktoba.
Jam'iyyu 17 ne za su fafata ciki har da APC da PDP, jam'iyyu mafi girma a Najeriya.
Sai dai babu mace ko ɗaya a cikin 'yan takarar.
Manyan 'yan takara
Duk da cewa 'yan takara 17 ne INEC ta tantance domin shiga zaɓen, uku daga cikinsu ne kawai suka fi shahara sosai.
Gwamna mai-ci Arakurin Oluwarotimi Akeredolu wanda na jam'iyyar APC mai mulki, da Eyitayo Jegede na jam'iyyar PDP, da kuma Agboola Ajayi na jam'iyyar ZLP wanda tsohon kwamishinan shari'a ne, su ne suka fi shahara.

Asalin hoton, FACEBOOK
Waɗannan 'yan takarar uku ne mafiya shahara ganin yadda jam'iyyunsu ke da ƙarfi a ƙananan hukumomi 18 na jihar.
Jegede na ZLP na yin takarar ne a karo na biyu bayan ya nema a 2016.
Dukkanin 'yan takarar uku lauyoyi ne kuma sun fito daga mazaɓun sanata uku daban-daban - Akeredolu daga Ondo ta Arewa; Jegede daga Ondo ta Tsakiya da kuma Ajayi daga Ondo ta Kudu.
Taƙaddamar da ta mamaye zaɓen

Asalin hoton, FACEBOOK
Mutane da dama na ganin cewa takarar za ta yi zafi sosai ganin cewa kowanne ɗan takara na da sashen da ya fi ƙarfi.
Kazalika, fafatawar ba za ta zo da sauƙi ba sakamakon irin hatsaniyar da ta faru tsakanin magoya bayan 'yan takarar.
Lamarin ya fara ƙamari ne lokacin da mataimakin gwamna ya fice daga APC zuwa ZLP, wadda ke da goyon bayan tsohon gwamna Olusegun Mimiko.
An samu arangama tsakanin magoya bayan APC da PDP, abin da ya jawo raunata magoya bayan ɓangarorin biyu da dukiyoyinsu.
A ranar 10 ga watan Satumba, gobara ta tashi a ofishin hukumar INEC da ke Akure, babban birnin jihar.
Gobarar ta ƙone wata kwantena da ke ɗauke da na'urar tantance masu kaɗa ƙuri'a ta Card Reader.
Shirin da INEC ta yi wa zaɓen

Asalin hoton, TWITTER/INEC
Tuni INEC ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen na 10 ga Oktoba cikin adalci da lumana.
Shugaban hukumar Farfesa Mahmud Yakubu tare da wasu jami'an hukumar sun zagaya ƙananan hukumomin jihar, inda suka horar da ma'aikatan INEC da jami'an tsaro da 'yan jarida kan yadda za a gudanar da zaɓen.
Hukumar ta shawarci mazauna jihar da su guji aikata duk wani abu na tashin hankali da ka iya kawo cikas ga kaɗa ƙuri'a.
Shirin da 'yan sanda suka yi wa zaɓen

Asalin hoton, NIGERIA POLICE FORCE
Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya tura tawagar manyan jami'ai 13 na 'yan sanda don tabbatar da tsaro a Ondo yayin kaɗa ƙuri'a.
Mohammed Adamu ya ce ya tura DIG ɗaya da AIG ɗaya da kuma CP 11 domin jagorantar harkokin tsaro tare da haramta wa 'yan sanda bai wa 'yan siyasa tsaro na musamman a ranar zaɓe.











