An yanke wa fasto hukuncin ɗaurin rai-da rai saboda ɓatan yaro a cocinsa a Ondo

Asalin hoton, Getty Images
Wata babbar kotu dake a Akure, babban birnin jihar Ondo a kudancin Najeriya, ta yanke wa wani fasto Babatunde Alfa, da ake kira fasto Sotitoberi hukuncin daurin rai da rai domin zama a gidan kaso. bayan samunsu da laifin sacewa tare da garkuwa da wani yaro dan shekara daya .
Kazalika bayan shi akwai karin mukarrabansa biyar da suma aka yanke musu hukuncin saboda hada baki da su da ya yi, wajen yin garkuwa, sa kuma sace yaron a yayin da yaje ibada tare da iyayensa .
An dai samu faston da mukarraban nasa ne da laifi kan tuhume-tuhume guda biyu wadanda suka hada da satar mutum da taimakawa wajen garkuwa da bil'adama .
Wadanda aka yanke wa hukuncin, sun hada da Omodara Olayinka da Margaret Oyebola da Grace Ogunjobi da Egunjobi Motunrayo da kuma Esther Kayode.

Asalin hoton, Getty Images
Mai shari'a Olusegun Odusola, ya ce mai gabatar da kara ya tabbatar da kwararan hujjoji a kan wadanda ake zargin.
Iyayen yaron dai sun neme shi bayan sun halarci zaman bauta a majami'ar Sotitobire amma sai labarin batansa kawai ake fada a cikin cocin.
A watan Nuwamba na shekarar 2019, wasu suka sace yaron a cikin cocin da kuma ba a san inda yaron yake ba.
Abin da ba a sa ni ba shi ne, ko fasto Babatunde Alfa, wato Sotito-bire, zai daukaka kara ko kuma zai rungumi kaddarar da ta hau kansa tare da mukarrabansa shi ne ake jira a nan gaba don jin matsayarsa.











