Hotuna: Coci-coci da aka mayar Masallatai da Masallatan da suka koma Coci-coci

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da zazzafar muhawara dangane da sauya Aya-Sufiya zuwa masallaci bayan shekaru kusan 90 da aka mayar da ginin wajen yawon bude ido.
Shugabannin siyasa da na addinai sun bayyana ra'ayoyinsu, sai dai shugaba Erdogan na Turkiyya ya kare matsayar kotu na yanke wannan hukunci.
Mun yi nazari kan wasu gine-gine biyar na Coci-coci da aka mayar Masallatai da Masallatan da suka koma Coci-coci.
1- Hagia Sophia - Turkiyya
Fitaccen ginin tarihin da ke Istanbul - an mayar da shi masallaci. Ginin mabiya darikar Orthodox.
Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya sanar da matakin bayan kotu ta yanke hukuncin cewa ginin na tarihi ya koma masallaci.

Asalin hoton, Getty Images
An gina Hagia Sophia shekaru kusan 1,500 da suka gabata a matsayin wurin bautar addinin Kirista, sai dai bayan shekaru a 1453 lokacin mulkin daular Ottoman aka sauya ginin zuwa masallaci.
Wurin bautar, da ya samu amincewar hukumar raya al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya, a 1934 aka mayar da shi wurin zuwa yawon bude ido lokacin mulkin Ataturk na Turkiyya.
Sai dai a farkon wannan watan kotun Turkiyya ta umarci a sake bude ginin a matsayin masallaci, kuma amfani da shi a matsayin wani abu sama da masallaci ya ''saba doka''.
Fafaroma Francis ya yi wasu kalamai a kan hukuncin: ''Ina tare da al'ummar Istanbul. Tunanin hukunci da aka yanke kan Santa Sophia abin bakin ciki ne.''
Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce a ranar 24 ga watan Yuli za a dawo da sallah a karon farko a Hagia Sophia.

Asalin hoton, Getty Images
Tarihin ginin tarihin a duniya
- Tarihin Hagia Sophia ya samo asali ne tun a shekara ta 537 zamanin iyalan Justinian dynasty da suka mulki a matsayin coci mafi girma.
- Girman hasumiyar ginin, yasa ake bayyana shi a matsayin coci da kuma gini mafi girma a duniya.
- Ya kasance a hannun mulkin masarautar Byzanite kafin shekara ta 1204 da aka ci birni a yaki.
- A 1453, daular Ottoman Sulta Mehmed II ta kwace birnin Istanbul (wanda aka baya ake kira Constantinople) kuma ta yi nasara jagorantar sallar juma'a ta farko a wurin bautar wato Hagie Sophia.
- Masarautar Ottoman ta mayar da ginin baki daya masallaci, sannan ta sauya abin da aka lulube gini da kuma sauya rubutun da ke jikinsa zuwa na Arabiya.
- Bayan kwashe shekaru mai tarin yawa a karkashin daular Ottoman, a 1934 aka mayar da ginin wurin zuwa yawon bude ido a wani kokari na mayar da Turkiyya kasa mai zaman kanta da soke bangaranci.
- A yau Hagia Sophia ya kasance fitaccen wuri a Turkiyya da duk wanda ya je kasar ke burin ziyarta, akalla mutum miliyan 3.7 ke ziyarta ginin a kowacce shekara.
2- Masallacin Babri, Ayodhya - India
A 2019, ginin masallacin Babri da ake rigima a kai a yankin Ayodhya na arewacin India, kotu ta mayar da shi wajen bautar Hindu.
A cewarsu ginin a baya wajen bautar mabiya addinin Hindu ne kafin Musulmi su kwace shi a 1592, suka kuma mayar da shi masallaci.

Asalin hoton, Getty Images
An dau tsawon lokaci ana ce-ce-ku-ce a kan wannan batu. Rigimar da ake, ita ce ainihin ginin mallakin waye tsakanin Musulmi da Hindu.
Kotun ta yanke hukuncin cewa za a bai wa Musulmi wani filin su gina masallaci.
'Yan kabilar Hindu da dama na da yarda cewa anan aka haifi abin bautarsu wato 'God Ram'. Musulmi kuma sun ce sun jima suna ibada a ginin tun kaka da kakanni.
A 1992, 'yan Hindu da suka fusata sun afka wa masallacin tare da lalata shi. Rikicin ya yi sanadi mutuwar mutum dubu biyu.

Kotu ta ce shaidun da aka gabatar mata sun tabbatar da cewa ba Musulmi ne suka yi ginin ba.
An yi bincike akan sauran baraguzan masallacin da aka lalata.
Kotun ta yanke hukuncin cewa Dhimsaha zai koma wajen bautar 'God Ram na Hindu', sannan su Musulmi za a basu inda za su yi ginin nasu masallacin.
Sai dai, Kotun ta ce rusa Masallacin Babri da aka yi ya saba doka.
Majalisar Musulmi da suka nuna rashin gamsuwa da hukuncin kotun sun ce ba za su daukaka kara ba.
3- Masallacin Cordoba
A 2014, dubban mutane sun shigar da kara na neman sauya masallacin zuwa cocin Katolika.

Da farko dai ana amfani da gini ne a matsayin masallaci da jamhuriyar Musulunci ta Andolisiya ta gina kafin ya koma coci a karni na 15.
Ginin da Musulmi suka soma gina shi, su koma kiristoci suka sake yi wa fasali, na dauke da tambarin addinan duka biyu.
Daga cikin masu korafi a kotu na cewa an yi kokarin cire alamar masallaci da coci daga jikin ginin.
Sai dai 'yan darikar katolika sun musanta hakan, sannan sun yarda da cewa a baya ginin masallaci ne.
''Abu mai sauki ne a cire tarihin Musulunci a jikin ginin,'' wani shugaban Katholika ya shaida wa BBC hakan a 2014.
A kalla mutum miliyan 1.3 ke ziyarta ginin a kowacce shekara daga sassa daban-daban na duniya.
4-Ingila- An mayar da tsohon Coci zuwa Masallaci
A 2017, majalisar gudanarwa ta Burtaniya ta jefa kuri'ar amincewa a sauya wani tsohon cocin kasar zuwa masallaci. Wannan mataki na majalisa ya kunno rikici da sabanin ra'ayi, wannan dai ya bai wa Musulmi damar samun wurin bauta.
5- Masallacin Granada
A 2003, Musulmi a Spaniya suka samu damar iko da Masallacin Granada, wanda aka kwace ikonsa daga hannun su shekaru kusan 500 da suka gabata.
Birnin da aka gina wannan masallaci shi ne cibiyar Musulmi Turawa.
A lokacin bikin bude masallacin, musulmi da dama da jami'an gwamnatin Spaniya sun halarci taron da aka gudanar.

A cewar Musulmi, dawo musu da masallacin ya sake zaburar da martabarsu da ta addini.
Sai dai akwai dimbin Spaniyawa da basu ji dadin hakan ba. Kowa na fargabar tanka batun.
Kusan shekaru 500 da suka gabata, Spaniyawa kiristoci sun mamaye kudancin kasar, da kawo karshen shekaru 800 na mulkin Musulmi daga yamma.
Masallacin dai ya kasance wurin bauta ga Musulmin Spaniya sama da dubu daya a yankin kamar yadda wani shugaban addinin Musulmi yankin Granada ya shaida.











