Hagia Sophia: An yi sallar Juma'a a mashahurin ginin tarihin karon farko cikin shekara 85

Worshippers laid out prayer mats outside the Hagia Sophia, waiting for the opening ceremony

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Masu ibada sun shimfida tabarmunsu a wajen ginin Hagia Sophia, suna jira a tayar da Sallah

Ɗumbin Musulmi ne suka gudanar da Sallar Juma'a karon farko a mashahurin ginin tarihin duniya na Hagia Sophia da ke birnin Santambul.

"Musulmi sun cika da ɗoki, kowa yana son zuwa wurin bude masallacin," in ji Gwamnan Santambul Ali Yerlikaya.

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jagoranci manyan ministoci wajen yin Sallah a masallacin

Matakin na zuwa ne bayan sanarwar da gwamnatin Shugaba Erdogan ta bayar don mayar da ginin zuwa masallaci a watan jiya.

Tun ainihi dai an gina Hagia Sophia a matsayin cocin daular gabashin Roma ko kuma Byzantine, amma sai aka mayar da shi zuwa masallaci bayan cin birnin Santambul da daular Ottoman ta yi a 1453.

A 1935 ne kuma, mutumin da ya assasa Turkiyyar zamani wadda ba ruwanta da addini, Kemal Ataturk, ya mayar da Hagia Sophia zuwa ginin adana kayan tarihi.

Shugaban Turkiyya ya jagoranci manyan ministoci wajen yin Sallah a masallacin

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaban Turkiyya ya jagoranci manyan ministoci wajen yin Sallah a masallacin
line

A wajen Hagia Sophia

Daga Neyran Elden, BBC Turkish

Dubun dubatar maza da mata ne suka jira kiran Sallah; mutane da dama sun baro wasu jihohi da ke fadin kasar inda suka tafi Santambul domin yin Sallah.

Masallata sun shimfida tabarmi a wajen masallacin. Wasu kuma sun samu wuri a karkashin bishiyoyi.

An tsaurara tsaro a harabar ginin mai dimbin tarihi; a wani gefen, masallata da dama ne suka karya shingen da 'yan sanda suka girke. Wani rukunin jama'a sun rika daga tutar kasar Turkiyya a ginin na Hagia Sophia suna cewa "Allahu Akbar".

Mutum 1,000 ne za su rika shiga ginin na Hagia Sophia a lokaci guda

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Mutum 1,000 ne za su rika shiga ginin na Hagia Sophia a lokaci guda

Ko da yake wasu 'yan kasar ta Turkiyya sun soki mayar da ginin tarihin masallaci, amma akasarin 'yan kasar sun yi matukar murna da yin hakan.

Wata mata mai shekara 45 ta ce tana son Hagia Sophia a matsayin ginin tarihi, kuma "ko da yaushe ina kallonsa a matsayin ginin mai kyawu."

line

A farkon wannan wata, Fafaroma Francis ya ce bai ji daɗin shawarar Turkiyya ba, ta sake mayar da ginin zuwa masallaci.

Wakilin BBC kan harkokin diflomasiyya ya ce: "Juma'a 24 ga watan Yuli, rana ce da ta buɗe wani sabon babi cikin ɗumbin tarihin Hagia Sophia mai dogon zamani."

Gini, wanda ya shafe tsawon shekara 900 a matsayin coci, ya koma masallaci tsawon shekara 500, kafin ya yi shekara tamanin a matsayin ginin adana kayan tarihi.

Kuma a Juma'ar nan ce, albarkacin gwagwarmayar da ƙungiyoyin Turkawa masu kishin addinin Musulunci suka shafe tsawon shekaru gommai suna yi da kuma burin Shugaba Erdogan, Hagia Sofia ta sake zama masallaci.

A woman wrapped in a Turkish national flag gestures outside the Hagia Sophia museum on July 10, 2020 in Istanbul as people gather to celebrate after a top Turkish court revoked the sixth-century Hagia Sophia"s status as a museum, clearing the way for it to be turned back into a mosque

Asalin hoton, Getty Images

Ga magoya bayan shugaban ƙasar masu ra'ayin 'yan mazan jiya, wannan lokaci ne mai cike da ɗumbin alfahari da ƙasarsu Turkiyya.

Ga Turkawa masu ra'ayin ƙasar da ba ruwanta da addini, zargin cewa Mista Erdogan yana sake tunkuɗa Turkiyya don komawa tsarin mulkin Musulunci, abin fargaba ne da ban takaici.

Shi dai Erdogan ya ce masu irin wannan tunani da ma Kiristoci, babu wani abu da zai razana su.

Za a ci gaba da buɗe ginin Hagia Sophia ga kowa kuma ba za a taɓa mashahurin zayyanar adon bangwayenta na zamanin Byzantine ba, ko da yake, za a dusashe su a lokutan salloli cewar shugaban.

Hagia Sophia, 28 Jun 20

Asalin hoton, Reuters

Sai dai daɗin bakin shugaban da karkata hankalinsa ga tarihin daular Ottoman na Turkiyya na nuni da wani faffaɗan burin siyasa, wanda zai sa a riƙa kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin Musulmin duniya da ya suka gaban kowa.