Hagia Sophia: UNESCO ta nuna rashin jin daɗi kan mayar da ginin tarihi masallaci

A woman wrapped in a Turkish national flag gestures outside the Hagia Sophia museum on July 10, 2020 in Istanbul as people gather to celebrate after a top Turkish court revoked the sixth-century Hagia Sophia"s status as a museum, clearing the way for it to be turned back into a mosque

Asalin hoton, Getty Images

Ana samun gagarumin martani a ciki da wajen Turkiyya kan shawarar Shugaba Erdogan na mayar da ɗaya daga cikin gine-gine mafi shahara a duniya - Hagia Sophia - da ke birnin Santambul masallaci.

Matakin ya zo ne bayan wani hukuncin kotu da ke mara baya ga mabiya addinin Musulunci kuma magoya bayan Shugaba Erdogan masu ra'ayin 'yan mazan jiya kan mayar da tsohon cocin zuwa masallaci..

Sai dai 'yan adawan ƙasar sun yi watsi da hukuncin da ya ba da damar mayar da ƙasaitaccen ginin zuwa masallaci.

A wani jawabi kan batun, shugaba Recceb Tayyip Erdogan ya ce sauya mashahurin ginin zuwa masallaci, abu ne da ya shafi 'yancin cin gashin kan Turkiyya.

"Mu tabbas muna maraba da dukkan aƙidoji a tsakanin al'ummar duniya game da wannan batu.

Sai dai batun yanke shawarar amfanin ginin Hagia Sophia ya shafi 'yancin cin gashin kan Turkiyya ne," in ji shugaban.

Ya kuma ce buɗe Hagia Sophia ga masallata da wata sabuwar ƙa'ida, abu ne kawai da ya shafi Turkiyya a ƙoƙarinta na tabbatar da 'yancin cin gashin kai da take da shi.

Duk da haka ya kuma ba da tabbacin cewa za ma a buɗe ginin ga kowa da kowa nan gaba

Hagia Sophia, 28 Jun 20

Asalin hoton, Reuters

"Kamar dukkan sauran masallatanmu, ƙofofin Hagia Sophia ma za a buɗe su ga duk 'yan ƙasa da mutanen waje da musulmai da ma waɗanda ba musulmai ba".

Sai dai fitaccen marubucin Turkiyya, Orhan Pamuk ya ce lamarin ya ƙwace alfaharin da miliyoyin Turkawa ke da shi na kasancewar ƙasar ta Musulmai wadda ba ruwanta da addini.

Shi ma wani magana da yawun hukumar kula da al'adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO, Matthieu Guevel ya bayyana martaninsa ga hukuncin.

Ya ce hukumar UNESCO na matuƙar nadamar wannan shawara ta hukumomin Turkiyya wadda aka yanke ba tare da gudanar da tattaunawa ba.

Ba kuma tare da an yi tuntuɓa ba kafin nan, don haka ya ce suna kira da a kare darajar da kowa yake bai wa ƙasaitaccen ginin tarihin na duniya.