Hajji 2020: Babu aikin ibada ga Musulmi kusan miliyan uku a bana

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya ta ce za a yi aikin Hajji a bana - amma mutane kalilan ne za su sami damar halartar wannan ibda mai matukar muhimmanci.
Kasar ta yanke wannan shawarar ce saboda yadda annobar Covid-19 ke kara yaduwa a ciki da wajen kasar, kuma tana ganin matakin zai taimaka wajen dakile bazuwar cutar.
Miliyoyin mutane na ziyartar biranen Makkah da Madina yayin aikin Hajjin.
A lokutan da duniya ke cikin kwanciyar hankali, aikin Hajji na cikin mafi muhimman ayyukan addini ga Musulmin duniya a kowace shekara.

Asalin hoton, MASJID AL NABAWI
Kimanin maniyyata miliyan biyu da rabi daga kasashe 168 na duniya kan kwarara zuwa birane masu tsarki na Makkah da Madina domin sauke farali.
Sai dai a bana babu maniyyata daga kasashen waje da za su sami damar zuwa Saudiyya saboda fargabar da ake da ita na kara yada annobar korona yayin aikin Hajjin.
A bana, 'yan Saudiyya da kuma 'yan kasashen waje mazauna Saudiyya ne kawai za su sauke farali - sai dai mahukuntan kasar ba su bayyana yawan maniyyatan da za a bari su yi aikin Hajjin na bana ba.
A bara 'yan Saudiyya fiye da dubu 630 ne suka gudanar da aikin Hajji.

Asalin hoton, Getty Images
Saudiyya na da masu dauke da kwayar cutar korona fiye da 160,000, wanda cikinsu fiye da mutun 1,300 sun riga mu gidan gaskiya.
Ma'aikatar aikin Hajjin ta Saudiyya ta sanar da cewa an dauki wannan matakin ne a matsayin kiyaye maniyyata kamuwa da cutar ta korona.
A Gabas ta Tsakiya, Iran da Turkiyya ne kawai suka fi Saudiyya yawan masu fama da cutar korona.










