Ba za a buɗe Masallacin Harami Ranar Arafa da Ranar Sallah ba

Wannan shafi na kawo muku bayanai kai tsaye dangane da irin wainar da ake toyawa a fadin duniya musamman batutuwan da suka shafi Najeriya da Nijar da makwabtansu.

Rahoto kai-tsaye

Nasidi Adamu Yahaya and Umar Mikail

  1. Rufewa,

    Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka kawo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Alhamis idan Allah ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.

    • Ga wasu daga cikin labaran da muka wallafa a wannan shafin a yau:
    • Nadin Fani Kayode a masarautar Shinkafi na janyo cacar baki
    • An sace samfur na gwajin cutar korona a Afirka ta Kudu
    • Annobar korona ta jefa matalautan ƙasashe cikin wani hali
    • Ranar Juma'a ta sama za a yi Babbar Sallah a Najeriya - Sarkin Musulmi
    • Najeriya za ta fara sayen man fetur daga Nijar
    • An saki wakilin gidan talbijin na Iran da aka kama a Abuja
    • An zargi ɗan sandan DSS da marin ma'aikacin filin jirgi a Abuja
    • Ba za a buɗe Masallacin Harami Ranar Arafa da Ranar Sallah ba
    • Shugaba Buhari zai tafi ƙasar Mali
    • 'Yan bindiga sun sace 'yan China huɗu a Calabar da ke kudancin Najeriya

    Za ku iya duba ƙasa domin karanta waɗannan labaran da ma wasu muhimmai.

  2. Gobarar tankar mai ta kashe mutane 20 a Delta

    Gobara

    Mutane akalla 20 ne suka mutu sakamakon kama wuta da wata tankar mai tayi a yankin Niger Delta a Najeriya.

    Lamarin ya faru a ranar Laraba a kan babbar hanyar da ke haɗa jihar Edo da kuma jihar Delta.

    Wasu daga cikin mutanen sun ƙone ƙurmus yadda ba za a iya gane su ba.

    Ganau sun bayyana cewa galibin waɗanda suka mutu sun gamu da ajalinsu ne a lokacin da suke ƙokarin ɗiban mai daga tirelar wacce ta faɗi.

    Take wuta ta tashi kuma ta fantsama a kan hanyar ta kuma kama wasu daga cikin motocin da ke wucewa a kan hanyar.

    Wani jami’in gwamnatin jihar Delta ya shaida wa BBC cewa tirelar ta kife ne a lokacin da take kokarin shan wata kwana sannan daga bisani ta kama da wuta.

  3. Asibitoci a Madagascar sun shiga wani hali

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Asibitoci a Madagascar sun shiga wani hali bayan ƙara yaɗuwar cutar korona a ƙasar.

    A baya dai shugaban ƙasar ya ta tallata wani jiƙo na tazargade a matsayin maganin na korona.

    An sake samun mutum 614 da suka kamu da cutar ta korona a ƙasar wanda a halin yanzu adadin waɗanda suka kamu da cutar ya kai 8,162 sai kuma mutum 69 da aka tabbatar da sun mutu.

    Tuni ƙasashen Afrika bakwai suka bayar oda domin kawo musu tazargaden na Madagascar.

    Sai dai Hukumatr Lafiya Ta Duniya ta bayyana cewa babu wani tabbaci da ke nuna cewa tazargaden na Madagascar na magance cutar ta korona.

  4. Sojojin Amurka sun kashe mayakan IS bakwai a Somalia

    Sojojin Amurka sun bayyana cewa sun kashe masu mayaƙan ƙungiyar IS bakwai a arewa maso gabashin Somalia.

    Rundunar sojojin Amurka da ke aiki a Afrika ta bayyana cewa sojojin Amurka tare da hadin gwiwar na Somalia sun kai harin ta sama ga 'yan ƙungiyar ISIS-Somalia bayan wani hari da suka kai ga sojojin kusa da ƙauyen Timirshe.

    Sojojin Amurkan sun bayyana cewa ba a raunata wani farar hula ba ko kuma kisa yayin harin.

    Wani gidan Rediyo a Somalia ya ruwaito cewa sojojin sa kai na yankin sun kashe mayaƙan IS 20.

    Ƙungiyar ta IS na ci gaba da kai hare-hare a ƙasar kusan shekaru biyar, sai dai ƙungiyar al-Shabab na neman shafe ƙungiyar ta IS.

  5. 'Yan bindiga sun sace 'yan China huɗu a Calabar da ke kudancin Najeriya

    'Yan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan bindiga sun sace wasu 'yan China hudu masu aikin gine-gine a jihar Cross River da ke kudancin Najeriya.

    Kwamishinar 'yan sanda ta jihar, Irene Ugboh Itohan ya tabbatar wa BBC faruwar lamarin.

    Ta ce an kashe wani dan sanda da ke aiki da 'yan Chinan a lokacin sace su ɗin a yankin Akampka a ranar Talata da daddare.

    An tura jami'an tsaro wajen don neman 'yan Chinan.

    Har yanzu ba a san dalilin sace su din ba, amma satar mutane don karɓar kudin fansa abu ne da ya zama ruwan dare a fadin Najeriya, sannan abin bai bar kan kowa ba baƙi da 'yan kasa.

    A wasu lokutan masu satar mutanen kan kashe waɗanda suka sace idan har ba a biya kuɗin fansa ba.

  6. Labarai da dumi-dumi, Shugaba Buhari zai tafi ƙasar Mali

    .

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Shugaban Najeriya Miuhammadu Buhari zai tafi Bamako babban birnin ƙasar Mali a ranar Alhamis.

    Tafiyar ta shugaban ƙasar ta biyo bayan tattaunawarsa da Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, wanda yana daga cikin masu shiga tsakani daga ƙunigyar ECOWAS da suka je Mali domin kawo sasanci.

    Wasu daga cikin shugabannin ƙasashen Yammacin Afrika irin su Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou sun amince su hadu a Mali domin tattaunawa domin kawo sasanci tsakanin Shugaban Mali Boubacar Keita da kuma 'yan adawa a ƙasar.

    Ana sa ran Shugaban Ghana Nana Akufo Addo da kuma na Cote d'Ivoire Alassane Ouattara za su halarci tattaunawar.

  7. Kim Kardashian ta amsa matsalar ƙwaƙwalwa da mijinta Kanye ke fama da ita

    Kim Kardashian da Kanye West

    Asalin hoton, Reuters

    Tauraruwa mai sayar da kayan kwalliya 'yar Amurika, Kim Kardashian West ta yi magana kan matsalar ƙwaƙwalwar da mijinta Kanye West ke fama da ita bayan ce-ce-ku-cen da aka riƙa yi a kwana nan.

    Ta rubuta a shafinta na Instagram: "Kamar yadda kuka sani, Kanye yana da matsalar ƙwaƙwalwa.

    "Duk wanda yake da wannan matsala ko kuma yake da ɗan uwa da yake da ita ya san irin wahalar da hakan ke da ita ga mutane su fahimta."

    Mutum ne "mai hazaƙa amma rikitacce" wanda "kalamansa ke cin karo da niyyarsa," in ji ta.

    Kim Kardashian da Kanye West sun yi aure a shekarar 2014.

    Kanye West na ɗaya daga cikin mawaƙan rap shahararru kuma masu arziki a Amurika kuma yanzu yana ƙoƙarin tsayawa takarar shugaban ƙasa.

  8. Ba za a buɗe Masallacin Harami Ranar Arafa da Ranar Sallah ba

    ka'aba

    Asalin hoton, Getty Images

    Manjo Janar Mohammed Bin Wasl Al-Ahmadi, mataimakin shugaban jami'an tsaro na Masallacin Harami yayin aikin Hajji, ya faɗa ranar Talata cewa masallacin zai ci gaba da kasancewa a rufe a ranakun Arafa da Idin Babbar Sallah saboda hana bazuwar cutar korona.

    Kafar yada labarai ta intanet ta Saudi Gazette ta ruewaito shi yana cewa: Dakatar da sallah a cikin masallacin da harabarsa zai ci gaba da aiki. Mun shawarci mutanen garin Makkah da su karya azuminsu na Ranar Arfa a gaidajensu,'' in ji shi.Manjo Janar Al-Ahmadi ya yi wadannan jawabai ne a yayin wani taron manema labarai inda ya sanar da kammala matakin farko na tsara Aikin Hajjin bana.

    Ya ce tsarin tsaro na hajjin bana zai mayar da hankali ne kan tsaro da jin kai da batun lafiya.Mun mayar da hankali ne bana kan batun lafiya saboda yanayin da aka samu kai a ciki. Sauran matakan za a kammala su a kwanaki masu zuwa,'' in ji Manji Janar Al-Ahmadi.Ya ce an sanya sabon tsari don lura da shiga da fitar mahajjata cikin Masallacin Haramin don tabbatar da cewa an bi dokar yin nesa-nesa da juna.Daga cikin matakan kariyar da aka dauka, an kebe hanyar zuwa wajen dawafi da na Safa da Marwa, sannan za a bar masu izini a hukumance su shiga harabar masallain in ji Manjo Janar Al-Ahmadi.

  9. Majalisa ta shawarci Buhari ya gabatar mata da kasafin kuɗin 2021 a watan Satumba

    Buhari da shugabannin Majalisar Ƙasa

    Asalin hoton, Nigeria Presidency

    Majalisar Dattawan Najeriya ta shawarci Shugaba Muhammadu Buhari da ya miƙa mata kasafin kuɗin shekarar 2021 nan da watan Satumba domin samun damar aiwatar da shi a kan lokaci.

    Kafafen yaɗa labarai a Najeriya sun ruwaito Ahmad Lawan shugaban majalisar yana bayyana hakan a yau Laraba yayin da ya karɓi buƙatar da Shugaba Buhari ya aika na daftarin hasashen abin da za a kashe a kasafin kuɗi daga 2021 zuwa 2023.

    Bayan karanta wasiƙar da Buhari ya aike musu wadda ke ƙunshe da daftarin na 2021-2023 Medium Term Expenditure Framework and Fiscal Strategy Paper, Ahmad Lawan ya umarci kwamitocin majalisar kan harkokin kuɗi da su fara aiki a kanta.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito Ahmad lawan yana cewa: "Ya kamata ɓngaren zartarwa ya fara aiki a kan kasafin kuɗin 2021, ina nufin muna so mu tabbatar cewa mun karɓi bayanan kasafin a ƙarshen watan Satumba don mu duba mu amince da shi kafin Disamba."

    An umarci kwamitocin da su gabatar da rahotonsu cikin mako huɗu.

  10. An zargi ɗan sandan DSS da marin ma'aikacin filin jirgi a Abuja

    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama a Najeriya ta zargi shugaban 'yan sandan DSS da cin zarafin wani ma'aikacin hukumar a filin jirgin sama na Abuja.

    Federal Airports Authority of Nigeria (FAAN) Safiyanu Abba, shugaban DSS na filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe, ya mari wani ma'aikacin hukumar saboda ya ankarar da shi bayan ya karya dokar hukumar.

    Lamarin ya faru ne ranar Juma'a 17 ga watan Yuli, in ji hukumar, sannan Safiyanu ya sake karya dokar tsaro ta filin jirgin saboda ya bayar da umarnin a lalube wani matafiyi.

    BBC ba ta ji ta bakin Safiyanu Abba ba game da lamarin amma hukumar ta ce ta kai ƙararsa, duk da cewa ba ta bayyana inda ta kai ƙarar ba.

    "Hukumar FAAN ta yi Allah-wadai da wannan ɗabi'a ta karya doka da kawo cikas ga tsarin tsaro a filin jirgin," in ji hukumar a wani saƙon Twitter da ta wallafa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  11. An saki wakilin gidan talbijin na Iran da aka kama a Abuja

    Danjuma

    Asalin hoton, PressTV

    Bayanan hoto, 'Yan sandan ba su tuhumi Danjuma Abdullahi da wani laifi ba

    BBC ta samu labarin cewa 'yan sandan birnin Tarayyar Najeriya, Abuja sun saki Danjuma Abdullahi, wakilin gidan talbijin na PressTV, mallakin ƙasar Iran.

    Rahotanni sun ce an kama Danjuma Abdullahi ne lokacin da yake daukar labarai kan zanga-zangar da mabiya Shi'a bangaren Sheikh Ibrahim El-Zakzaky suke yi a Sakatariyar Gwamnatin Najeriya da ke Abuja ranar Laraba.

    Rundunar ba ta tuhumi Danjuma da kowane laifi ba. An kama dan jaridar ne tare da mai rike masa na'urar daukar hoto.

    Da farko 'yan sandan sun ajiye Mr Danjuma Abdullahi a ofishinsu da ke sakatariyar ta gwamnatin tarayya ko da yake daga bisani sun tafi da su ofishin CID.

    Wannan ba shi ne karon farko da 'yan sanda ke yi wa 'yan jairda dirar-mikiya ba.

  12. 'Yan sandan Australia sun umarci wata mace ta cire ƙunzugunta yayin wani bincike

    'Yan sandan Australia

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda a birnin Sydney na Australia sun tilasta wa wata mace da ta cire ƙunzugunta - audugar mata - yayin wani binciken ƙwaƙwaf da suka yi wa wasu mata tsirara, a cewar wani rahoton jami'an tsaro.

    Wannan yana ɗaya daga cikin ayyukan 'yan sanda na rashin kyautawa da aka bankaɗo a shekarar da ta gabata, inda aka binciki lokuta biyar da hakan ta faru.

    Akasarin binciken wanda ake sa mutane su yi tsirara, sun faru ne a wuraren biki, inda ake barinsu cikin kunya da yanayi na wulaƙanci, a cewar rahoton.

    Hukumar 'yan sandan New South Wales ta ce za ta duba abubuwan da rahoton ya ƙunsa.

    Rahoton ya umarci 'yan sanda da su nemi afuwar ɗaya daga cikin 'yan matan da abin ya faru da su sannan ya ce an dakatar da wani ɗan sanda a kan hakan.

  13. Najeriya za ta fara sayen man fetur daga Nijar

    Man fetur

    Asalin hoton, Getty Images

    An ƙulla yarjejeniyar kasuwanci tsakanin kamfanin man fetur na najeriya, NNPC, da kuma na Nijar, SONIDEP, game da sayar wa Najeriya tataccen mai da za ta riƙa amfani da shi a cikin gida.

    Ba wannan ce yarjejeniyar farko da kasashen biyu suka ƙulla ba kan wannan batu sai dai wannan ne karon farko da za su ɗauki ƙwararan matakai don ganin yarjejeniyar ta yi nasara.

    An dakatar da waccen yarjejeniya ne tun bayan da hukumomin Najeriya suka ɗauki matakin rufe iyakokin ƙasar, abin da ya jawo dakatar da shiga da man ƙasar.

    Ita ma annobar korona ta ƙara tillasata wa kasashen ɗaukar matakan ba-sani-ba-sabo.

    Nijeriya ta ce sayen man daga Nijar zai rage mata wasu wahalhalu da take fuskanta wajen sawo man da take amfani da shi cikin gida daga ƙasashen Turai.

    A watan Nuwamban 2011 ne Nijar ta shiga sahun ƙsaashen da ke haƙo man fetur.

    Kampanin NCCC na China ne gwamnatin ƙasar ta damka wa alhakin haƙo man daga Agadem na Jihar Diffa tare da tace shi a garin Ɗan Baki na Jihar Damagaram, yayin da kamfanin mai na ƙasar, SONIDEP, ke da alhakin kasuwancinsa.

    Kampanin da ke tace man futur a Nijar, SORAZ, na tace gangar mai 20,000 a kowace rana, wanda shi ne za a fara sayar wa Najeriya.

  14. Mutum na ƙarshe da aka yi wa shari'a tare da Nelson Mandela ya rasu

    Afirika ta Kudu

    Asalin hoton, Getty Images

    Andrew Mlangeni, mutum na ƙarshe da gwamnatin wariyar launin fata ta ɗaure tare da Nelson Mandela a gawurtacciyar shari'ar Rivonia Trial a Afirka ta Kudu, ya mutu yana da shekara 95.

    Ana ganin wannan ce shari'ar da ta sa Mandela ya shahara a duniya.

    Mista Mlangen ya rasu bayan an kai shi wani asibitin sojoji a Pretoria sakamakon raɗaɗi a mararsa.

    Mutuwarsa na nufin shuɗewar tarihi da wurare kusan baki ɗaya," a cewar Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa.

    A cewar littafin tarihin Mlangeni na 2017, The Backroom Boy, Mandela ya zaɓe shi ne domin ya yi aiki da mutum biyar na farko da ke yaƙi da gwamnatin wariyar, waɗanda za a tura China domin samun horo.

  15. Ranar Juma'a ta sama za a yi Babbar Sallah a Najeriya - Sarkin Musulmi

    Kwamitin ganin wata da ke karkashin shugabancin Sarkin Musulmi na Najeriya ya ce ranar Juma'a 31 ga watan Yuli za a gudanar da Idin Babbar Sallah.

    A sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, kamitin ya ce an ga sabon watan Dhul Hijjah a wurare da dama ma kasar ranar Talata, don haka yau Laraba ce daya daga watan Dhul Hijjah.

    A cewarsa, an ga sabon watan ne a Abuja da Jalingo da Ilorin da Lafiya da Minna da kuma Misau.

    Ya kara da cewa masarauta Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III za ta fitar da sanarwa a hukumance da za ta yi cikakken bayani kan tsarin Babbar Sallah.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  16. Bobi Wine ya kafa sabuwar jam'iyya a Uganda

    Bobi Wine

    Asalin hoton, AFP

    Dan majalisar dokoki na bangaren adawa a Uganda, Robert Kyangulanyi wanda aka fi sani a matsayin Bobi Wine ya kaddamar da wata sabuwar jam’iyyar siyasa a yayin da ake shirin gudanar da zabe a kasar a shekara mai zuwa.

    Bobi Wine ya ce jam’iyyarsa ta National Unity Platform Party za ta fafata a zaben shugaban kasa.

    A watan Junairun 2021 ne za a gudanar da zaben shugaban kasa a kasar Uganda a yayin da shugaba Yoweri Museveni zai nemi wa’adi na shida a mulki.

    A ranar Talata ne Mr Museveni ya karbi takardar neman takara a zaben shugaban kasa.

    Hukumar zaben kasar Uganda ta haramta gangamin yakin neman zabe a kasar saboda annobar korona.

  17. Gwamnan Jihar Ekiti ya kamu da cutar korona

    Kayode Fayemi

    Asalin hoton, @kfayemi

    Gwamnan Jihar Ekiti da ke kudancin Najeriya, Kayode Fayemi ya bayyana cewa ya kamu da cutar korona, wadda ake yi wa laƙabi da Covid-19.

    Gwamnan ya bayyana haka ne a wani saƙon Twitter da ya wallafa yau Laraba.

    "Na yi gwajin cutar korona jiya (Talata) kuma ina ɗauke da cutar," in ji Fayemi.

    "Ina cikin ƙoshin lafiya kuma tuni na killace kaina a gida ƙarƙashin kulawar tawagar likitocina."

    Gwamna Fayemi ya ƙara da cewa ya bar wa matamakinsa wasu ayyukan, yayin da shi kuma zai ci gaba da jan ragamar mulkin jihar daga gida.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  18. Annobar korona ta jefa matalautan ƙasashe cikin wani hali

    Korona

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata Ƙungiyar samar da ci gaba ta ce cutar korona ta haifar da ƙalubale ga ƙasashen da ke fama da talauci da rikici da kuma matsalolin muhalli.

    Ƙungiyar Development Initiatives ta ce buƙatar kai ɗauki ta fi na kowane lokaci, inda sama da mutane biliyan suke buƙatar tallafin a yanzu.

    Amma kuma ta yi gargaɗi cewa ana samun raguwar tallafi, inda ƙasashe masu arziki ke karkatar da dukiyoyinsu domin biyan buƙatun gida saboda annobar korona.

    A cewar ƙungiyar, lamarin zai jefa ɓangaren lafiya na ƙasashen da ke fama da talauci cikin mawuyacin hali.

    Alƙaluman da Jami'ar Johns Hopkins ke tattarawa na cutar sun nuna cewa mutum kusan miliyan 15 ne suka kamu da ita a duniya (14,968,982) sannan dubu 616,985 suka mutu da kuma miliyan 8,486,019 da suka warke.

  19. An sace samfur na gwajin cutar korona a Afirka ta Kudu

    Afirka ta kudu

    Asalin hoton, Anadolu Agency

    'Yan sanda a Afirka ta Kudu suna bincike kab sace wata babbar motar daukar kaya wacce ke dauke da samfur na gwajin cutar korona a birnin Port Elizabeth.

    An sace motar ce wacce aka ajiye a kofar asibiti ranar Litinin sannan aka yar da ita a wani wuri, a cewar kafar watsa labarai ta SABC.

    An ce an sace gwaje-gwajen na cutar korona wadanda aka adana a cikin kankara.

    Jami'an lafiya sun gargadi wadanda suka sace motar da kuma jama'a cewa kada su taba su saboda za su iya kamuwa da cutar korona,in ji rahotaon shafin intanet na news24 website.

    An yi wa mutum kimanin miliyan biyu da rabi gwajin cutar korona a kasar.

    Ita ce kasar da ta fi yawan mutanen da suka kamu da cutar a Afirka.

  20. Nadin Fani Kayode a masarautar Shinkafi na janyo cacar baki

    Kayode

    Asalin hoton, Zamfara Govt

    A Najeriya, wasu jama’ar arewacin kasar sun fara bayyana adawa da wani mukamin sauratar ‘‘Sadauki’’ da masarautar Shinkafi a jihar Zamfara ta ba wani dan asalin yankin kudu maso yammacin kasar na al’ummar Yarabawa, kuma tsohon ministan sufurin jiragen sama na Najeriyar, Cif Femi Fani Kayode.

    Masu adawa da wannan nadin sarautar, suna ganin mukamin gargajiyar bai dace ba, saboda zargin da suke yi masa cewa makiyin arewacin Najeriya da jama’ar yankin ne.

    Mr Fani Kayode jigo ne a jam'iyyar PDP mai adawa a kasar kuma ya kasance mutum me yawan jawo cece-kuce game da abubuwa da ke faruwa a cikin kasar musamman yawan dora alhakin matsalolin Najeriya kan shugabanni a arewacin kasar.

    Matakin bai wa Cif Kayode mukami ya sa wasu masu rike da mukamai a masarautar Shinkafi yin murabus.