FIFA za ta binciki Rubiales kan sumbatar 'yar wasa

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta fara bincike kan shugaban hukumar kwallon kafar Sifaniya, Luis Rubiales, saboda halayya da ya nuna a wasan ƙarshe na cin Kofin Duniya ta Mata da aka yi ranar Lahadi.
Rubiales ya sumbaci 'yar wasan gaba Jenni Hermoso a lebe bayan Sifaniya ta doke Ingila a wasan ƙarshen gasar.
Tun da farko ya riƙe gabansa a lokacin da yake murnar kammala wasan.
Fifa za ta duba ko wadannan halayen sun keta doka ta 13 a cikin ka'idojin ladabtarwarta, game da ɗabi'a abar kyama.
A cewar kundin, jami'ai na daga cikin waɗanda dole ne su "bi ƙa'idojin wasa na gaskiya, aminci da mutunci".
Ta ce za a iya ɗaukar matakan ladabtarwa a kan duk wanda ya “take ƙa’idojin halayya masu kyau”, “cin mutuncin dan Adam ko na shari’a ta kowace hanya, musamman ta hanyar amfani da kalamai da halaye ko harshe” ko kuma “halayyar da za ta sanya wasan kwallon kafa ko kuma hukamar FIFA cikin kunya."







