Watakila Hamas ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a Gaza

Gaza

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Gaza

Masu shiga tsakani na kasar Masar sun shaidawa wata jaridar Amurka cewa Isra'ila ta bai wa kungiyar Hamas wa'adin mako guda da ta amince da shawarar da aka gabatar mata na tsagaita bude wuta tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza, ko kuma za ta kai farmakin da ta dade tana barazanar yi a Rafah.

Kungiyar Hamas ta tabbatar da cewa tawagarta za ta je birnin Alkahira domin tattaunawa da masu shiga tsakani a yau Asabar.

Kawo yanzu Hamas na nazari akan martani da za ta mayar ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da aka yi wa kwaskwarima.

Israilar ta yi wa Hamas tayin dakatar da bude wuta na tsawon kwanaki 40 tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su.

Hossam Badran wanda babban jami'i ne a Hamas ya ce kungiyar na nazari kan abubuwan da yarjejeniyar ta kunsa da kyakkyawar manufa.

Sai dai kuma ya zargi firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da kokarin ganin cewa yarjejeniyar ta gaza ta hanyar dagewa akai-akai a kan cewa sai Israila ta kai wa mayakan Hamas da ke Rafah hari ko ta yaya.

Hukumar lafiya ta duniya ta sake yin wani gagarumin gargadi cewa idan har wannan farmaki ya gudana toh ba zai haifar da komai ba illa zubar da jinin miliyoyin falasdinawa da suka rasa matsugunansu da ke samun mafaka a can.

Tun da farko wani jami'in W-H-O ya ce hukumar na da wani shiri na kai dauki idan Israila ta kai hari a Rafah.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Rik Peeperkorn wanda shi ne wakilin Hukumar lafiya ta duniya a Gaza da Yammacin Kogin Jordan ya ce farmakin da sojojin Israila za su kai zai haifar da mumunan sakamako:

" Farmakin sojojin Israila zai sa a sake samun mutanen da su saka rasa matsuguninsu, da karin cunkuson jama'a da rashin abinci da ruwan sha da rashin tsaftar muhali da kuma karin bullar cututtuka da sauransu. Yanayin tsaro kuma zai kara tababbarewa'' in ji shi.

Ita ma Amurka ta ce za ta ci gaba da nuna damuwarta a tattaunawar da ta ke yi da Israila kamar yadda kakakin fadar White House Karine Jean Pierre ta fadawa yan jarida:

" Mun fito fili game da matsayarmu. Za mu c i gaba da bayyana matsayinmu a gaban bainar jama'a. Mun nuna damuwarmu a kan wani gagarumin farmaki da Israila ke son ta kai ta kasa a Rafah, mun fito fili karara mun ce wannan nada matukar hadari ga farar hula. Mun kuma ba su shawara a kan wata hanya daban da Israila za ta iya amfani da ita wajan wargaza Hamas"

"Kun dai san ana ta kwan-gaba -kwan- baya kan alamarin . Mun yi ammanar cewa Israila za ta duba damuwar da mu ka nuna yayin da ta ke shirin daukar matakin soji na gaba"

Fadar White house ta yi ammanar cewa bangarorin biyu za su cimma matsaya kan yarjejeniyar tsagaita bude wuta tare da sakin mutanen da aka yi garkuwa da su koda yake ta yi la'akari da cewa abin da ya rage a yanzu shi ne Hamas ta dauki mataki na gaba.