Isra’ila za ta shigar da kayan agaji Gaza

....

Asalin hoton, EPA

Rundunar sojin Isra’ila ta ce za ta ƙara yawan kayan agajin da take kai wa Gaza a ƴan kwanaki masu zuwa.

Wannan na zuwa ne bayan shugaban Amurka, Joe Biden ya jaddada buƙatar shigar da kayan agajin Gaza, da kuma lalubo hanyar tsagaita wuta.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa Falasɗinawa a yankin, su na fuskantar matsananciyar yunwa, lamarin da ya sa ƙasashen duniya da dama ke kiran a ƙara shigar da kayan agaji ga mabuƙata.

Kakakin rundunar tsaron Isra’ila, Daniel Hagari, ya ce za a shigar da kayan agajin zuwa Gaza ne ta sabbin hanyoyin kan iyaka, kuma aikin zai gudana a cikin wannan makon.

Ya ce: "Shigar da kayan agaji Gaza na daga cikin muhimman tsare-tsaren mu, saboda muna yaƙi ne da Hamas ba wai da jama’ar Gaza ba. Za mu taimaka wajen sauƙaƙe wahalar da fararen hula ke sha a Gaza. Halin da ake ciki yanzu, sakamako ne na yaƙin da Hamas ta ƙaddamar a ranar bakwai ga watan Oktoba, lokacin da ta kashe mutane ta kuma yi garkuwa da wasu."

Fadar White House ta ce shugaba Biden ya sake jaddada buƙatar kai agaji Gazan, a wata tattaunawa ta waya da ya yi da Firaiminista Benjamin Netanyahu.

Tun da farko dai, ƙungiyar bayar da tallafin abinci ta duniya ta ce, a yau Litinin za ta sake ƙaddamar da shirin ta, na kai tallafin abinci Gaza, wata guda bayan wani harin Isra’ila ya kashe mata ma’aikata bakwai.

Ta ce akwai kayan abinci aƙalla tirela 300 da ake shirin shiga da su Gaza, ta mashigar Rafah.