Ƙungiyar agaji ta katse aiki bayan kashe ma'aikatanta a Gaza

Bayanan bidiyo, Gaza: Bidiyon da ke nuna yadda hari ta sama ya lalata motocin ƙungiyar ba da agaji ta WCK

Ƙungiyar ba da agajin abinci mai suna World Central Kitchen (WCK) ta dakatar da aikace-aikacenta a Gaza bayan mutuwar ma'aikatanta a wani hari da Isra'ila ta kai ta sama.

Ƙungiyar ta ce waɗanda aka kashe wani ɓangare ne na kwambar ma'aikatan agaji da ke barin wani gidan ajiyar kaya a tsakiyar Gaza.

Rundunar Tsaron Sojin Isra'ila ta ce tana gudanar da "cikakken nazari" a kan wannan al'amari.

Ofishin harkokin yaɗa labaran Hamas na Gaza shi ma ya ɗora alhakin abin da ya faru a kan Isra'ila.

WCK na ɗaya daga cikin manyan masu samar da abinci da ake tsananin buƙata a Gaza.

A cewar ƙungiyar ba da agaji, an kai wa kwambar ma'aikatan agaji hari ne lokacin da suke barin gidan ajiyar kaya na Deir al-Balah, "inda ayarin ya sauke abincin agaji fiye da tan 100 da aka kai Gaza ta hanyar sufurin teku."

Ƙungiyar ta ce an kai harin ne duk da yake ta shirya da rundunar sojojin Isra'ila game da tafiyar kwambar ma'aikatan.

Wata majiya daga cibiyar lafiya ta Falasɗinu ta faɗa wa BBC cewa ma'aikatan na sanye da falmaran gagara-harsashi wadda aka buga tambarin (WCK) sunan ƙungiyar a taƙaice.

Rundunar sojin Isra'ila a ranar Talata ta ce tana gudanar da cikakken nazari a matakin manyan jami'ai don fahimtar yanayin yadda wannan "mummunan lamari" ya faru.

"Rundunar IDF na ƙoƙari sosai don ganin an kai kayayyakin jin ƙai cikin aminci kuma tana aiki ƙut-da-ƙut da ƙungiyar WCK a muhimmin tsayin dakansu na samar da abinci da tallafin jin ƙai ga al'ummar Gaza," ta ƙara da cewa.

A cewar WCK, ma'aikatan da suka mutu sun haɗar da wata 'yar Ostireliya da Poland da na Birtaniya da Bafalasɗine da kuma mutumin Kanada amma asalinsa daga Amurka.

"Ina cike da takaici da damuwa - ƙungiyar World Central Kitchen da al'ummar duniya - sun yi rashin mutane nagari a yau saboda harin da rundunar tsaron sojojin Isra'ila ta kai," shugabar ƙungiyar Erin Gore ta bayyana a cikin wata sanarwa.

"Soyayyar da suke da ita wajen ciyar da al'umma da himmar da suke da ita na nuna cewa jin ƙan ɗan'adam shi ne gaba da komai, sannan kuma gudunmawar da suka bayar wajen ceton rayuka babu adadi, za a ci gaba da tunawa da martaba hakan har abada".

WFK

Asalin hoton, World Food Kitchen

Bayanan hoto, Lalzawmi "Zomi" Frankcom ta bayyana a wani bidiyo na ƙungiyar ba da agaji ta WCK a makon jiya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar Cogat, cibiyar ma'aikatar tsaron Isra'ila da ke kula da ayyukan kai kayan agaji zuwa Gaza, ƙungiyar WCK ce ke da alhakin kai kashi 60 na kayan agajin da ƙungiyoyi ke shigar Gaza.

WCK ta faɗa a cikin wata sanarwa da ta fitar a baya-bayan nan cewa ta ba da abinci fiye da sau miliyan 42 ga mutane a Gaza tun cikin watan Oktoba kuma ta shirya samar da ƙari ga wasu mutane kimanin miliyan ɗaya.

Ƙungiyar a baya-bayan nan ta shiga kanun labarai bayan ta samar da ɗaruruwan tan na abinci ga al'ummar Gaza, wanda aka ɗauko a cikin jirgin ruwan kai agaji na farko a watan Maris.

Hukumomin ba da agaji sun shiga kai kayan agaji ta ruwa ruwa don ƙara yawan abincin da sauran kayan buƙatun rayuwa da suke shigarwa cikin yankin, wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yana gab da aukawa cikin bala'in yunwa.

Mista Andres da matarsa Patricia ne suka kafa ƙungiyar ba da agaji ta World Central Kitchen a 2010, da farko don samar da abinci ga mutanen da suka kuɓuta daga wata babbar girgizar ƙasa a Haiti.

A wani saƙo da ya wallafa a shafin sada zumunta game da mutuwar ma'aikatan nasa, Mista Andres ya yi kira ga gwamnatin Isra'ila "ta dakatar da waɗannan kashe-kashe ba-ji-ba-gani".

Firaministan Ostireliya Anthony Albanese ya tabbatar cewa ma'aikaciyar agaji Lalzawmi "Zomi" Frankcom na cikin waɗanda aka kashe kuma ya aika saƙon ta'aziyyarsa ga dangi da makusantanta.

A cikin wata sanarwa, ya ce: "Wannan mutum ce da ke aikin sa-kai a ƙasashen waje don samar da tallafi ta hanyar wannan ƙungiyar agaji ga mutanen da ke fama cikin matsananciyar takura a Gaza. Don haka, wannan kwata-kwata ba za a lamunta ba.

Ya ce Ostireliya na sa ran za a gabatar da "cikakken bahasi", ya kuma ce wannan wani "mummunan lamari ne da kwata-kwata bai kamata a ce ya faru ba".